💥 *RUD'ANI....*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers*)*SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33*SADAUKARWA:* *FATY DANMALIKI*
*HAPPY BIRTHDAY to my lovely daughter BASHMAR Age with grace and mercy momy slimzy love you much*🎂💋
*27*
Ta cikin hasken farin wata anuwar ke kallon Fatima gaba Daya yanayinta ya bayyana masa tana cikin matsananciyar damuwa,tausayinta ne ya Kara kamashi haka ta karaso ya bude Mata kofar ta Shiga batare da ta rufe ba ta zauna....shiru batace masa komiba shima baice Mata ba sun dauki minti goma sha biyar a hakan,gajiya anuwar yayi ya sauke sarautarsa Dan ya fahimci Fatima haka take akwai Mulki murmushi yayi yace "ranki ya dade tunda Baki gaisheniba ni Bari in gaisheki"
Kunya ce ta lullubeta ta Kara sunkuyar da kanta Kasa tace "Ka tashi lafiya?"
"Ban tashi lafiya ba domin na kwana INA tunaninki na kwana da matsanancin ciwon Kai inata tunaninki Fatima"Kallonsa tayi a Karo na farko tausayinsa ya kamata anya Zata sanar masa da halin da Ake ciki kuwa?Sam bataso Dan mutane ya Shiga halaka ya kuma Kara zurfi cikin soyayyarta,
"Kinyi shiru ki fadamun abinda kike tunani domin kwayar idonki ta nunamin akwai damuwa sanan wani bangare na zuciyata dayake bugawa bugunsa ya Karu sakamakon inaji a jikina akwai wata matsala data taso ko take Shirin tasowa"
Mamakinsa ne ya kamata wani lokaci idan anuwar na fadin magana tamkar aljani haka yake ko kamar an sanar masa,murmushi ta kakalo "bakomi fa ba abinda yake faruwa Ka kwantar da hankalinka Ka koma gida Ka nemi magani Ka kwanta"
Tsareta yayi da Ido a Karo na farko Fatima ta Nuna damuwa Akansa Amma tabbas kwayar idonta na Nuna masa a zahirnn gaskiya karya tayi masa na ba abinda ke faruwa take wata hikima ta Fado masa "karya ba dabiarki bace kikan Fadi gaskiya ko zaa mutu ina mamakin Yadda kikace babukomi bayan na tabbatar akwai babbar matsala Dan Naga hakan a mafarkina na jiya Dan haka ki sanar Dani kawai"
Ajiyar zuciya ta sauke take taji jikinta yayi sanyi tabbas anuwar yayi nisa a soyayyarta tsananin tausayinsa yasa jikinta yayi sanyi hawaye masu dumi suka Shiga zubo Mata Shi kuwa kallonta yakeyi zuwa yanzun gari ya Fara wayewa sai charar zankara kakeji,
Nan ta kwashe Komi ta sanar masa na abinda yasameta tin daga faduwa har zuwa gidan Malam abbah....take hankalinsa ya tashi Yana Shirin magana ta dakatar dashi "Ka kwantar da hankalinka wanan Karon banida raayin zuwa neman wani magani domin inaji a jikina wani Abu zai iya samun mu"
"Babu abinda zai samemu Fatima Zahra sai ikon allah Dan haka banaso kiyimun musu Akan Komi"Yana Gama magana yasa hannu ya rufo murfin mota yasa lock yatada mota Bai Jira cewarta ba ya bar anguwar da ita,mamaki ne ya hanata magana ganin yadda ya yanke hukunci kawai tasan Inda ya nufa da ita kafesa tayi da Ido ya rame sosai yayi fari daka kallesa kasan akwai abinda ke damunsa dik yayi laushi anuwar Wanda ko murmushi bayayi saboda Jin Kai irin nasa.....
********
Faruk kuwa wanka yayi ya saka farar shadda da bakar hula dara ta matukar karbarsa Bai tsaya ko inaba sai sashin mahaifiyarsa,da tsananin damuwa da tunanin Yadda momy Zata karbi maganarsa da shawarar Daya yanke,Tana zaune gefenta wata hadimarta ce sanye da jajayen Kaya ya shigo cikin sauri ta kaskantar da Kai ta soma gaishesa a dakile ya amsa sanan yace "bamu waje"mikewa tayi ta fita saidai a bakin kofa ta tsaya jikinta na Bari tana waige waige Kada a kamata Dan tabbas aikin da mama Fulani tasata aikine Mai hatsarin gaske,
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...