💥 *RUD'ANI...*🤦🏻♀️
*FREE BOOK*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*19*
Meeniosky da ta Gama fusata babu ko sallama tashiga dakin Fatima wadda take zaune sanye da hijab ta jingina da jikin gado tayi nisa cikin tunani taji alamar an shigo...Dan tsorata tayi zatai magana meeniosky ta tarbeta...."Fatima...INA fatan Baki mance da wanan muryar dakeyi Miki magana ba a halin yanzun,idan kin mance kuma in tuna Miki"....gaban Fatima ya yanke ya Fadi cikin sassarfa da furgici tace "inajin murya kamarta ameenah aminiyata kawata yar uwata kuma....Allah yasa ba gizo muryarki takeyimun ba"
"Ba gizo muryata keyi mikiba,nice dai meeniosky kawarki a da sanan point of correction Niba yar uwarki bace kawance mukayi a da kuma yanzun ya Zama tarihi gashi kin shigo gidan da nake mafarkin shigowa a matsayin sirika kinyimun Karan tsaye to ina Mai gargadinki ki fita a hanyar anuwar cikin awa ashirin da hudu ko kuma in tona Miki asiri Susan keba yar gudun hijira bace da uwarki da ubanki a garin Kaduna...koda yake bakin cikinki yayi sanadiyyar barin ubanki duniya in Baki saniba kisani ubanki ya kwanta dama kina yawon kwadayi wadda asara ta aura kawai wacce kwadayi yakaita GA auren aljani saboda tsananin son duniya"....waigawa meeniosky tayi Jin alamun takun takalmi yasa ta kalleta tayi tsaki ta fice,takun tafiyarta Fatima taji wacce ta sandare a zaune hawaye ke bulbula a idonta....wacce tuni zuciya tazo Mata kirji jikinta tsananin rawa yakeyi....babu Kalmar da ta doki kunnena kamar "ubanki ya mutu kina wajen yawon kwadayi bakin ciki yayi sanaddiyar mutuwar ubanki"
Kicibis meeniosky sukayi itada anuwar ya shigo sashen Fatima ta kalli hannunsa...plate ne dauke da abinci sai wani galon dauke da wani Abu kamar magani....wani kallo ya jefeta dashi yayi saurin ajiye galon din Zata wucesa ya dakatar da ita "ke....wani munafunci ya kawoki wanan sashen Mai kikazo yi"
Bakin ciki ne ya tokare Mata kirji cike da tsananin fushi ta dubesa,irin kallon da tayi masa yasashi tsananin mamaki sai kawai ta girgiza Kai cike da kishi tace "idan Ka Shiga Ka tambayeta abinda nazoyi tunda ita kakeso baniba tasan nidin ko wacece"idonta ya kawo ruwa ta cije Baki kamar Zata fashe da kuka tayi gaba....dage kafadarsa yayi ko a jikinsa ya nufi dakin Fatima.... meeniosky har takai kwanar fita sashen ta juyo cike da takaici tayi kwafa ta wuce tana share hawayen takaici....yau zuwanta ko kwana batayiba ta Fara fuskantar bakin ciki da kaskanci a sanadin Fatima kawarta?.....
Kamshin turarensa ne ya baibayeta samm Yadda ya tarar da Fatima ba karamin furgita anuwar yayi ba ya zaro wayarsa Yana kokarin Kiran afee kamar Yadda suka Saba ita ke magana da ita jikinsa ya kama rawa wayar ta subuce ta Fadi Akan tiles ji kake tassss....tabbas ta gane kamshin turaren nan da take yawanji a tare da ita...harshenta yayi Mata nauyi ya cika bakinta dakyar taja ajiyar zuciya ta sauke ta fashe da wani irin kuka Mai ban tausayi Wanda ya Kara furgitar da anuwar....
Cikin in ina ya soma magana cikin muryarsa Mai taushi "zahrah....kukan Mai kikeyi Mai akayi Miki?meke faruwa?ki fadamun menene"
Kuka kawai takeyi cikin tashin hankali kuka take Mai tsuma zuciya Wanda yasa jikin anuwar karayin sanyi ya narke da tsananin kaunarta da tausayinta...dubanta yakeyi cikin wani irin yanayi ji yakeyi tamkar ya rungumeta a kirjinsa ya hanata kukan da takeyi.....wani irin kuka takeyi maiban tausayi....
Afee ce ta shigo sashen tun daga bakin shigowa takejin kukan Fatima gabanta ya yanke ya Fadi tabbas taga shigowar anty meenah sashen nan ta window tanata tunanin Mai tazoyi
Shigowa tayi da sallamarta anuwar ya sauke ajiyar zuciya ganin afee yayi Mata Alama data tambayeta....cikin takaici afee tace"ya anuwar wallahi anty meenah ce Naga shigowarta cikin sashen nan ta window inaso inyi sallah yasa ban biyota ba"
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...