💥 *RUD'ANI..* .🤦🏻♀️
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)**SLIMZY*✍🏻
_wattpadd@slimzy33_*SADAUKARWA:FATY DANMALIKI*
*3*
Take ya rikidar Mata ya koma tsohon jiya jini nabin idonsa...zaro ido tayi Zata Kara kwalla Kara a Karo na biyu cikin kiftawar ido ya tallabota Yana kallonta cike da mamaki "menene yake faruwa matana menene?"...kallonsa takeyi cikin tashin hankali Amma ta Kasa magana sai kirjinta dake bugawa kmr ana buga Mata guduma,gumi ne ya karyo Mata ta sauke sassanyar ajiyar zuciya,ta Kasa kwace jikinta daga rukon da yayi Mata ta kwantar da kanta a kafadarsa kamshin turarensa ya daki hancin ta lunshe ido dakyar ta bude Baki cikin kasala da matsanancin ciwon Kai "sweetheart wani mafarki nayi Mai ban tsoro Amma bazan iya tuna mafarkin nawa ba"
Murmushin mugunta yayi "bazaki taba tuna mafarkin ki ba harabada.....sanan ba mafarki kikeyi ba ido biyu kike"...tayi saurin dago Kai "maganganunka suna kama da almara"
"Ba almara bace idan dai Saddam ne bakiga Komi ba"yace Yana dariya cikin sigar tsokana Yana kallonta cike da nishadi.....
Jimmm kadan tayi tana tunani ya katse Mata "nazo in tambayeki ne idan zaki aureni"...kwankwasa glass din motar akayi tayi saurin kallon agogo "lokacin lecture's yayi zamuyi magana kaji?"
Ruko hannunta yayi "Bana magana biyu ki amsamun bukatar aurena kafin ki fita..."
Wani dadi ne ya lullubeta me zaisa bazan amsa maka bukatar aure ba bayan daular da nake hangowa?"ta tambayi kanta cikin zuciyarta a zahiri kuwa tace "na amince ina sonka Zan aureka"tana fadin haka ta bude mota ta fice ta rufo...rikida yayi taki ya koma suffarsa ta tsoho da shigarsa...
"Keko soyayya tasa kin mance Damu muna jiranki ko gashi zakija mana lattin lectures kinsan jarabar mutumin nan idan kayi missing class dinsa sau uku bakada exams ko?"slimzy tayi tsaki tayi gaba,
Meeniosky tayi murmushi "Amina rigima Kenan ni wallahi bankai yarinyar nan rigima ba dikda sunan mu Daya,
Waigowa sukai a tare GA mamakinsu babu motar Saddam ta bace bat kuma babu shedar tayar mota na tafiya...kallon juna sukai "Kai gayen nan maye ne yaushe yaja mota Bamu saniba har ya fice a makarantar nan babu dalilinsa?"
Murmushi teemah tayi tayi yar Kara "soon to be Mrs Saddam... guess what?wai kinsan tambayata yakeyi Zan aureshi?yanaso ayi aurenmu nan kusa"
Meeniosky tayi tsalle "kice muyi Shirin biki Dan tabbas a wajen bikinki akwai manyan gayu inaga khamis hakuri zaiyi in caskale Dan ba karamin wanka zanyi ba"tace tana murmushi koda suka isa har an soma lectures slimzy ta Shiga abinta suna hangenta ta watsa musu harara....
*******
Bugun kofar duniya faruk yaki bude kofa ya kifa kansa jikin bango tunda yazo duniya baa taba wulakantasa haka ba soyayya taja mace tayi disgracing dinsa cikin bainar jamaa,babban tashin hankalinsa da guy din nan ke neman gane Shi Dan sarki ne....Jan numfashi yayi ya furzar da iska Mai zafi daga bakinsa,ya cire kayan jikinsa ya fad'a toilet ya sakarwa kansa ruwa.....Ya fito Yana tsane Kai da towel aka sake bugun kofar a Karo na biyu cike da takaici ya bude kofar...kyakkyawar budurwa ce tsaye ta turo Baki "haba ya faruk tun dazun nake bugun kofa Baka budemun ba"
"Am sorry...jeki ce driver ya shirya mota zamu fita shawagi cikin gari inaso mubi ta kofar babbar jamiar garin nan"...
"Momy ke magana dakai tace kazo gimbiya rumaisa tazo Ku gana"....takaici ne ya lullube faruk wai yaushe yarinyar nan zatabar bibiyarsa Shi bayasonta bayason auren zumunci su momy sunki ganewa...."jekice fitar gaggawa ta kamani"ta juya tana waigensa ya koma ciki ya Shiga shiryawa tsafffff
YOU ARE READING
RUD'ANI
Spiritualzazzafan labari Mai cike da darussa da nishadantarwa tabbas akwai rudarwa littafin RUD'ANI Ku biyoni Dan Jin labarin teemah dollar da saurayinta dattijon aljani....da faruk bawan Allah a gefe shin ya RUD'ANI zai kasance sai kun tsundumma Dan ganin t...