01

2.1K 147 10
                                    

Yayin da iska hade da guguwa ke kadawa kadawa me karfi,  hadari ya lulube sarraryin samaniya luf,  cida da walqiya na bayyana wanda ze tabbatarwa da mutum ruwa na iya saukowa a kodayaushe.

Hakan be hana wata matashiya tafiya ba , cikin sauri sauri take tafiya kallo ďaya zaka mata ka tabbatar da cewa ba'a cikin hayyacinta take ba, domin hakan ya bayyana karara a fuskarta,  bata san yadda akai ba sai kawai tsintar kanta tai a faculty ...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Hakan be hana wata matashiya tafiya ba , cikin sauri sauri take tafiya kallo ďaya zaka mata ka tabbatar da cewa ba'a cikin hayyacinta take ba, domin hakan ya bayyana karara a fuskarta,  bata san yadda akai ba sai kawai tsintar kanta tai a faculty dinsu,  wanda a sama an rubuta da manyan baki *FACULTY OF MEDICINE*  cincirondan mutanen data hango tun daga nesa ne yasa ta qara tabbatar da cewa tabbas an kafe musu sakamakon jarrabarsu na shekara ta farko da ze tabbatar musu da makomarsu a makaranta,  duk da maza dasuka mamaye wajen hakan be hanata kutsawa ba cikin zafin nama dan ganin sakamakonta hannuta jiki da duk wasu gabanta na karkarwa tai qoqarin daidaita kanta amma ta kasa,  hadiye yawun bakinta tai ta fara duba sunnayen a hankali,  da takardar farko ta fara sam bata ga sunanta ba,  hankalinta ya sake tashi,  ďayar pepar ta sake dubawa shima ba sunanta, hannu ta na karkarwa hakama bakinta tana kokarin magana amma sam ta kasa
  "malama indai baki sunanki anan ba to ki duba wancan list din ba mamaki kina cikin a withdraw"
   Zaro ido tayi tana kalansa, tana maimaita kalmar 'withdraw a zuciyarta ta nemi sannin asalin kalmar amma ta rasa tabbas tasan kalmar amma ma'anarta sam ya gushe daga kwakwalwarta,  jiki a sabule ta nufi wajen dayan list din,  hannu na karkarwa ta shiga duba sunannaye,  idanuwanta ne suka hango mata sunanta dara dara
    *ZAHIRA ABDULRA'UF* a gaban sunan ansa _WITHDRAW_ iya kidimewa ta kidime bata tsaya duba sauran bayyanan ba ta bar wajen, kuka take nema ido rufe ko ta samu sassaucin radadin da zuciyarta ke mata, amma sam ta nema shi ta rasa! Nan da nan idanunta suka fara juyawa kafafunta na nema dena daukanta take ta nemi wata kujera ta zauna ta dafe kanta tana runtse ido ko kuka yazo amma sam yaki zuwa.
     
     Rufe maidaidaitan idanuwanta tai take hoton fuskar Ummu ta gani, Da wani idan zata kalli Ummu da tasha gaya mata cewa kullum takan roki tsahon rai a wajen Allah domin taga rannar da zata cimma nasararta a rayuwarta rannar da duk burinkanta zasu cika, da wani idan zata kalleta tace mata an kore batai nasara ba!, batai aune taji hawaye na riga rigar saukowa tuni ta fashe da kuka kuka me tsanani, takai akala mituna goma tana abu daya idanuwanta sunyi jawur duk sun koma ciki,  jakarta ta sakala jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga makarantar,
    "Zahirah am soo sorry naga sunanki cikin yan withdraw sorry ehen Allah sauya miki da mafi alheri"  muryar abokin karatunta Kabir ke fadan haka
   Jiki a sanyaye tayi kokarin kirkiro murmushi tace
   "nagode Kabir se anjima" bata jira amsarsa ba tayi saurin tai gaba abinta,  me adaidaita ta tsayar ta shige batare da ta fada masa inda zasu je ba
"hajiya ina zamuje ne? " muryar dan. Adaidaita kenan data katse mata tunaninta
  Cikiin sauri ta masa kwatacen gidansu,  minti sha biyar ne ya kaisu kofar gidansu a lokacin har hadari ya fara washewa, sai iska me sanyi dake kadawa a hankali,  ikon Allah kenan! ,  zaro dari biyu tayi ta mika masa ta juya ta shiga gidan.
    Ummu na ganin shigowarta ta washe baki sosaii take murmushi, kallo daya ta mata ta gane akwai abinda ke damunta dan idanuwanta sunyi ja jawur ga fuskarta ta kumbura, kan tayi magana Zahirah ta karaso da gudu ta rungumeta tana kuka, kuka sosaii wanda ya tada hankalin Ummu ba kadan ba,  cikin sauri ta dago kanta ta shiga share mata hawaye
"Zahirah kukan me kike haka?"
  Bakinta na rawa tace
  "ummu wai sai yaushe zan cimma nasara a rayuwata ne?  Sai yaushe zan shiga sahun yaya mata masu yanci! Meyasa banida sa'a a rayuwata? Ummu na sake faduwa jarrabawata Ummu sun koreni daga makaranta na shiga uku Ummu"
   Da sauri Ummu ta sa hannun ta rufe mata bakinta
  "karki sake fadan wannan maganar kinji?  Kowanne bawan da kikagani a duniyar nan Allah na jarrabatarshi kisani wannan itace jarrabawarki Zahirah,  kiyi kokarin cinye jarrabarwarki wajen Allah zaki sha mamaki nan gaba.  Allah yana sane da halin da kike ciki" ta fada tana share mata hawayenta da kyar ta lallasheta ta kaita madaidaicn dakinta sannan ta fito cike da tausauin Zahirah ta tuno irin wahalar data sha ta tuno irin gwagwarmaryar da suka sha kafin ta samu addmission har Allah cikin ikonsa yasa ta samu Medicine sai gashi ranna daya duk wahalarsu ta tashi a banza, 
  "Kaico! Hakika kina fuskantar jarabawowin masu wahala a rayuwarki Allah ya baki ikon cinyeta" ta fada tana share hawayenta.
   Tunda Zahira ta zauna kuka take, tunanin rayuwarta takeyi da babu wani abun birgewa a cikinta,  jin sallamar datai ne yasa ta zaro ido hade da dafe kanta
   "Ya Allah!  Da wani ido zan kalli YA Mubarak dayasha gwagwarmaya me tsanani wajen ganin na cimma burina da wani ido zan kalleshi nace masa na fadi jarrabawa ta!  Innalalahi waina illaihi rajun" ta sake fashewa da kuka me tsanani.

   Hello everyone🌚  ga yadda labarin Zahirah ya soma, me kuke ganin game da labarin nan?  Shin waccece Zahirah?  Wasu irin kalubale take fuskanta?  Shin kuna ganin zata cimma burinta a rayuwa?  ku biyoni dajin yadda labarin ze cigaba da tafiya

  Please dont forget to share vote and comment, i'ill be waiting to hear your thoughts and views😁
  Nagode🤝
#Love u all❤
#ZHR017
#Miss_Hafsah

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now