Kamo hannuwanta yayi ya saka a cikin nasa, ya kalleta cikin ido yace
"Ki dena fadan haka Zahirah, in sha Allahu dani dake zamu reni babynmu ba abinda ze faru kinji?"
"A'ah akwai, nace maka mutuwa zanyi nidai ka yafemin"
Girgiza kai yayi yana hawaye
"Bazaki mutu ba in sha Allahu ki dena fadan haka"
Doc ta shigo za'a wuce da ita teater room, tana kuka yana kuka, haka aka shiga da ita, dawowa yayi wajensu Ummu wanda suma jikinsu yayi sanyi sai kai da kawowa sukeyi. Ya imra ta karaso wajen Ayaan ganin yadda idan sa yayi jawur, ta dafa shi
"Ayaan kayi hakuri muyita addua in sha Allah zaayi komai agama lafiya, bari naje na dauko Samha daga skul ,she will be fine in sha Allah karka damu"Jinjina kai kawai yayi ba tare da ce mata wani abu ba, ta tafi, suna zaune gabadayansu Ummu ,Ummi mummy da Inna ba wanda ke magana kowa yayi shiru yana addua a zuciyarsa
Bayan hours kadan , Dr ta fito dauke da murmushi a hannunta, baby ce a hannunta ta karaso wajensu, a zubure Ayaan ya tashi
"Ya jikin nata?"
Da murmushi tace
"Alhamdulilah shes fine ba wata matsala"
Nurses biyu suka karaso kowacce rike da baby a hannunta. Dr ta kalli Ayaan tana miqa masa Babyn hannunta
"Congratulations Ayaan Tafida, matarka ta haihu triplets namiji daya mata biyu" ta fada da murmushi a fuskartaTsayawa yayi cak, face su Mummy da suka tashi da sauri kowacce ta dauko babyn cike da murna, ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido sannan yakai dubansa gabas yayi sujadar godiya ga Allah ,sannan ya karaso wajen babies din yana kallansu idan ya kalli wannan, se ya dawo ya kalli wannan , yama rasa me zeyi ko me zece tsabar murna,
"Yanzu duk nawane? 'Yayanane wadannan koh?"
Inna da murmushi ta kalleshi
"Yayanka ne mana malakinka"
Daukansu ya dinga yi daya bayan daya yana rungumesu,tare da manna musu kiss kamar ya hadiyesu haka yakeji murna fal a cikinsa yama rasa me zeyi.Sanda aka fito da Zahirah ,Ayaan ne farkon shiga ya kallata
"Babe.. kinga abinda nake fada miki koh? Gashi nan yanzu komai ya wuce, amma babe dama kinsan yan uku zaki haifa baki fada min ba?"
"Ni kaina banda tabbaci, all i know its yaddda nakeji nasan ba da dayane a cikina ba, koda dr ta dage se anyi scanning da aka gani boye paper din nayi, dan banma yadda ba"
Hannuwanta tasa akan sumarsa ta danyi murmsuhi
"Love wallahi nazata mutuwa zanyi! Azaba amma Alhamdulilah"
"Ai ni kaina na tsorta anya kuwa zan kara barinki kisha wahalar nan?"
Kafin ta amsa su Inna suka shigo kowanne rike da Babyn suka miqowa Zahirah kallonsu ta tsaya yi kawai tana share hawayen fuskarta,
"Alhamdulilah Ummu kinga" ta fada cike da murmushin
Ummu ta dafa kafadarta
"Ribar hakuri kenan Zahirah, kinga da Allah ya tashi sai ya baki har guda uku fatanmu Allah ya rayasu ke kuma ya baki lafiya"
Ameen sukace gabadaya.Labarin haihuwar Zahirah ya dinga baza dangi a hankali, kowa cike yake da murna , tuni yan barka suka cika asibiti, Kwanata hudu aka salamosu. Mummy an rikice dan ita kayan barka daya ta dinga siya sai gashi har yan uku, nadama fal a cikinta , ita da ya imra suka shiga kasuwa hadda Daddy suka jibigo uban kaya.
Zahirah zaune tana ta kumbure kumbure Ganin yadda Babies din ,daddare sun hanata bacci ta samu ta dan kwanta sai kuka suke tsalawa , a lallai su yunwa sukaje ga Inna ta saya a gaba sai tashinta takeyi
"Dan Allah Inna ki barni nayi bacci kina ganin jiya hanamu bacci sukayi"
"To ya zakiyi? Renon kenan ai maza tashi ki basu kar ki shiga haqin yara"
Zumburo baki tayi ta dauki dayar macen wadda tafisu rigima duk cikinsu, Ayaan ya shigo dauke da ledoji a hannunsa da sauri ya aje ya karaso"Sannu Babe.. sun hanaki barci koh? Naga idanunki sunyi yayi ja"
"Wallahi love, kai dai bari sai Hamdala"
Murmushi sukayi suka shiga hirar shirye shiryenshi suna.Rannar suna anyi shagali , kamar ba gobe hall ya cika har ya batse yanuwa da abokan arziqi duk sunzo anyi taro lafiya an gama lafiya, Namijin yaci sunan Daddy Abdul ana ce masa Nabeel sai Yanmatan Daya Firdaus Imra da Zanira Amna.
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...