16

998 85 23
                                    

Cike da alamun tambaya take kallan kyakyawar jaririyar
" wannan dagani ana sane aka yada ita, in ba haka ba mene na saka sunanta?  kaico duniya ina zaki damu?"
rufe bakinta yayi daidai da kwankwasa kofar  Abban Asaad, da gudu Asaad yaje ya rungumoshi
"Abba oyoyo, Abba Ummu ta samo mana an baby me kyau"
Dariya Abban Asaad yayi
"Asaad naga sanda zaka dena shirme"
Ganin ta zaune rike da jaririya ya sashi firgita ainun
"Safiyya? Nidai nasan ban barki da ciki ba, watani uku da suka wuce da hannuwana na sa d'an da kika haifa a cikin kabarinsa bayan Allah ya karbi ransa, ina kika samo jaririya?"
Sai daya zauna sannan ta bashi labarin duk abinda ya auku, sosaii yake mamaki da tausayin jaririyar ,
"Wannan rashin adalcin har yayi yawa"
"Uhm Abban Asaad ai abin da matukar mamaki da kuma rashin imani, nidai a ganina in har mace zata iya daukan ciki batare da taji kunya ba to banga amfani jefar da abinda ta haifa ba, Allah ya kyauta"
Kwalin ya shiga zazzagawa take wata farar takada a nade ta fado da sauri ya dauka cikin nutsuwa ya fara karanta abinda ta kunsa,mamaki sosaii yayi, na yadda mata suka dauki cikin shege ba komai, abin haushi kuma su haifa su yar, basa ko tunanin irin halin da dan ze shiga a wannan duniya da bakowa ne nagari ba, mene ne ribarsu indan har sun yarda d'an  da suka haifa bayan sunsha wuyar nakudarsu? Me zasu cewa Ubangijinsu, da laifin zina zasuji? Ko kuma da laifin yardar da jariri Allah ta'ala wanda besan komai game da wannan duniyar ba, da wannan tunani gabadayansu suka kwanta, mussaman Safiyya datakeji zata iya komai domin ta raini yarinya ta kuma bata tarbiya ingantaciya domin kauce mata fadawa halin da mahaifiyarta ta shiga har ta sameta.

Tun safe da Safiyya ta tashi ta shiga store dinsu ta hado kayan wanka data siya na jaririn data haifa watani uku da suka wuce Allah ya karbi ransa, komai na jariri tana da shi dan haka ta dauko ta hada ruwan wanka tayiwa Babyn wanka, kayan data siya na babynta unisex ta saka mata, hade da rungume ta tana tunanin abinda zata sha ruwan maman ta ya fito ta fara shayar da ita, Abban Asaad ya fito cikin shirin sa na fita
"Ahh ya banga kin shirya ba?" Ya fada yana gyra kwalar rigarsa
"Zuwa ina Abban Asaad?"
"So nake muje Kano mukai babyn nan gidan marayu domin nan ya dace data zauna"
Zaro idanuwanta tayi cike da rashin fahimta tace
"Kana nufin wai bazamu  riketa ba?"
"Eh gidan marayu zamu kaita dan gaskiya ban iya rikon yar da bata halak ba, Kuma ma uwar data haifeta ca nake yarda ta tayi? Akan me zamu riketa?"
Rungume da babyn ta tashi idanuwanta na kansa
"Amma bakada imani Abban Assaad, wannan Allah kadai ne yasan me yake nufi daya sa har na tsinceta, nidai gaskiya bazan iya rabuwa da ita ba"
Sunfi minti talatin suna musu akan abu daya, Daya lura taki yarda yasashi kallanta a fusce
"To indai haka ne, sai dai ki zab'a koni ko ita"
Kuka ta saki ta kalli babyn da har yanzu ta rik'e hannunta gam, tana jin sonta a zuciyarta bazata iya rabuwa da ita ba a yadda take jinta, tasan cewa mijinta na santa bakuma ta tunanin ze iya rabuwa da ita, dan haka cike da kwarin gwiwa tace
"Gaskia bazan iya rabuwa da babyn nan ba"
"Au haka kikace?l
"Eh"
Cike da fusata ya kalleta
"To in haka ne ke da ita ku barmun gida na"
"Me kake nufi?"
"Ina nufin kije gida..... sai sanda na nemeki"
A razane ta kalleshi, ta fusata ainun, janyo hannun Asaad tayi wanda yake rike da na Abbansa gam
"Babu inda zakije dashi, tunda kin zabi wata can daban akan mahafinsa banga amfani kice zaki tafi dashi"
Batace komai ba illa  goye babyn da tayi ta shiga hada kayanta a dayar akwatin ta hade duk wasu kayan jarirai data siyawa late babynta, kudi ta dauko ta saka a handbag dinta sannan ta jayo akwatunan zuwa falo
"Kayi kuskure Abban Asaad, nasan ko ba dade ko bamijima dole zaka dawo ka nemeni"
Tana gama fada ta fice daga gidan Asaad nata kuka amma haka ta barshi. Kai tsaye motar kano ta hau daganan ta hau ta misau suka dauki hanya.

A gajiye ta tura kofar gidan nasu ta shiga, tun a zaure  ta jiyo muryar Kabir da Mama, dagani a tsakar gida suke zaune suna hira, salama tayi sannan ta shigo gidan, gabadaya sukai mutuwar tsaye ganinta, sun kasa gasgata cewa a zahiri ne, Kabiru ne yayi karfin hali karasowa wajenta ya dafa kafadararta, kuka ta fashe dashi hade da rungumeshi, Mama ta karaso da sauri idanunta cike da tambayoyi kala kala
"Safiyya Lafiya?"
Duk abinda ya faru ta kwashe ta fada mata, cike da fushi Mama ta falla mata mari
"Bansan baki da hankali ba sai yau Safiyya, zauna nan, in mahaifinki ya dawo kya fada masa"
"Mama ki tsaya ki saurareni..." kan ta karasa kuka ya cin mata
"Babu abinda zaki fada da har zan saurareki,zefi miki ki juye ki tafi gidan mijinki"
Rufe bakinta yayi daidai da shigowar Baba gidan yadda ya gansu cirko cirko, ya sashi tsaya neman baasi, bagan yaji komai ya jinjina kai yana kallan ta
"Safiyya ko kadan baki kyauta abinda kikai ba, duk irin daraja ta aure kika take ta akan yarinyar da kika tsinta lokaci daya wadda ko asalinta baki sani ba? amma na miki uzuri, ba mamaki hadda yarinta ma tana damunki, amma ki zaune gobe da sassafe zamu wuce kano, nida kaina zan maidaki gidanki base shi ya nemeki ba, kuma daga nan mu wuce mukai jaririyar gidan marayun kamar yadda yace, ba dole sena kina riketa ba in kinaso ma zaki iya daukan nauyinta nime baki gudunmawa ne, tunda har yace baze riqeta ba inaga bin umarninsa shi yafi, saboda darajar aure ta wuce duk tunaninki, tashi ki shiga ciki gobe ki zamana cikin shiri sa sassafe zamu wuce, Allahu ya maki albarka"
Tunda Baba ke magana take jin tamkar an datsa mata wani abu a zuciya, tabbas tana bin umarnin mahaifinta kuma ko sau daya bata taba saba umarnisa ba, koda kuwa umarnin bezo daidai da san ranta ba, amma a wannan ya zama dole itama ta tashi tayi magana, dan ba tun yau ba ta kuduri Niyyar zatai komai dangani ta zauna da jaririyar nan, cikin raunin murya ta katse shirun daya mamaye wajen tun bayan da Baba ya fara magana ta hanyar cewa
"Baba kamin afuwa dan Allah, ina bin dukkanin umarnin ka, inaso ka bani dama, Baba wallahi bazan iya rabuwa da wannan babyn ba, zan koma gidan Abban Asaad ne, duk sanda ya yanke shawarar in zauna in rainin wannan jaririyar!!"""

Naso yafi haka, amma abubuwa sunsha kaina, muje zuwa dai jama'ata yanzu aka fara💃🏻👻

Karku mata da danna tauraruwar nan da kuma fadan raayonyinki, i mean vote and comment please🙏🏻

In kun ci karo da typing error ignore please, ban tsaya nayi editing sosaii ba😫🙏🏻

#NWA
#ZHR
#Hafss
#love you all❤️

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now