25

436 32 13
                                    


Malam Hashimu dattijon mutum ne, wanda sana'arsa bata wuce faskare ba, dan asalin garin Danzabuwa ne, matarsa ta farko ta rasu wajen haihuwa da ita da abinda ke cikinta , ganin yana zaune shi kadai ba mata ne ya saka babban abokinsa Liman, shawarta masa auren A'ilo, wata fitatiyar yar bariki wadda talauci yayi sanadiyar fadawarta cikin wannan halin, yayi hakan ko  ze zamo silar shiryuwarta, sam Malam Hashimu beso ba, amma ganin hakan kamar jahadi ne, ya sashi amincewa, A'ilo kuwa dayake tana ganin mutuncin Liman batai musu ba ta amince duk da cewa ba sanshi take, a haka ta had'a kudadenta da amincewar sa ta samu yar rumfa a tasha take saida abinci, har Allah yasa ta samu ciki ta haifi santaleliyar yarta wadda taci sunan ZANIRA.

  Ba kamar A'ilo ba, Zanira ta taso yarinya me nutsuwa da tarbiya dan san karatun boko da islama, kowa na garin mamaki yake dan tunda aka haifeta babu wanda baya mata fargabar Allah yasa karta debo halin uwarta, cikin ikon Allah kuwa sai Allah ya temaka bata dauko komai ba, duk da cikin tasha suke wuni, mafi yawanci lokuta cikin yan bariki , amma hakan besa halinta ya canzu ba.

A haka ta k'arasa gidan, tana shiga kai tsaye wajen magajiya taje takai sakon, tana kokarin fita sukayi kicibis da wata budurwa wadda dagani shekaru kadan ta bata
"Yi hakuri bansan na bugeki ba"
Dafata ta tayi cike da murmushi
"Bakomai, Allah yasa dai kema ba nan gidan kike ba?"
"Ba nan nake ba Innata ce take aikoni,"
"Har na ji miki dadi yaruwa, kin burgeni ya sunanki?" Ta fad'a tana dafata
"Sunana Zanira"
"Masha Allah ni sunana Zainab, karki bari komai na nan ya baki shaawa nima kaddarace ta jefoni, sai anjima"
Da toh ta amsa sannan ta tafi

Tana tafe tana zancen zuci, juyowar da zatayi tayi kicibis da Abdulrauf , da mamaki tace
"Me kake anan?"

"Babu komai Zuneera, na fito zaga gari ne kefa?"

"Na farko dai ni ba sunana Zuneera ba, Zanira sunana, na biyu kuma aikena akayi" ta fada tana kare masa kallo

"Iyyee so kin iya magana har haka? to muje na rakaki gida"
Duk da bataso ba haka ta hakura har suka iso kofar gidan sukayi sallama ya wuce.

    Cikin wata daya suka saba sosai, har ya kai ga tana zuwa dakin dayake yana koya mata karatu, wani sain in beda aiki a tasha , wajen abinci yake yinin yanayi yana taya ta aiki , ko ajinki Inna dan ita wannan be shafeta ba, alala ala ma take taji yace yana san auren Zanira ya aureta ta huta.

Watarana bayan ya gama koya mata karatu ya juyo ya kalleta

"Wai Zuneera bakya jin wasu feelings akaina? Nifa wallahi sanki nake" ya fada yana kura mata ido sunkuyar da kanta tayi ta kasa magana se murmushi
"Hakan na nufin nima kina so na kenan? Gyada kai tayi ba tare da tayi magana ba

Ta dan jima kafin ta dago tana kallansa
"Amma kuma se nakega kamar baze yiwu ba idan ka tafi Gombe fa shikenan"

"Injiwa ya fada miki garin masoyi na nisa? Ya fada yana k'arasowa daf da ita
Da sauri ta dan ja da baya, ya kalleta yana murmushi
"Me na ja da baya kuma? Ba mun zama daya ba?"

"Uhm" kawai tace tana wasa da 'yan yatsunta

"Uhm? Akwai magana a bakinki" ya fada yana kura mata ido
"Babu, yamma nayi bari naje kar Baba ya nemeni"

"To shikenan... sai anjima my love, bari nazo na rakaki" kunya ma ya bata ta tashi da sauri ta rigashi fita

Haka dai suka cigaba da soyayya mai karfi har kawayenta suka gane, Baba daya fahimci yayi murna sosaii sai dai kuma gani yake kamar hakan baze yiwu ba dan haka ya kirata

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now