"What do you mean Azeema?" Ayrah ta fada cikin rashin fahimtar zancen Azeemar
Murmushi Azeema tayi
"Nifa ba tun yau na gano cewa kina son Ya Ayaan ba, am your best friend Ayrah be kamata kina boye min wannan ba, besides Ya Ayaan yaya ne, to me na boyewa?"
Tsaki Ayrah tayi ta fice daga dakin ba tare da ta waiwaiyi Azeema ba.Zahirah na gama breakfast ta shiga dakin Ummu dake tsaye tana jera turarurukan kan madubin ta, salamarta ya sata saurin juyowa, hade da aje wonder flower perfume dake hannunta
"Ummu sannu da aiki"
"Yauww Zahirah, kin gama kenan? Zauna bari nazo"
Tana zama wayarta ta hau ruri, se a lokacin ta tuna alkwarinta da Ayaan na zezo yau, runtse ido tayi tana tunanin mafita, cikin sakoni kadan ta maida wayar silent had'e da karawa a kunne
"Waalaikumus salam, dan Allah Madam kiyi hakuri, ina wani aiki ne but in na gama da wuri zanzo in sha Allah" ta kashe wayar ta aje.
Ummu dake kallo da saurarenta tun sanda ta fara wayar tace
"Ke dawa kike wayar Zahirah?"
"Nida Madame din Catering school dinmu ce ta kirani jiya wai zata wai taro akan abinci shine ta gayyaceni, na manta ba fada miki ba kuma yanzu zamuyi magana shiyasa nace mata"
Cike da nutsuwa Ummu tace
"Wannan ai ya kamata kije Zahirah, nasan akwai karuwa tunda ta har ta gayyaceki, tashi ki shirya kije in kin dawo mayi maganar".
Sai da ta nuna alamun bata san zuwa ,Ummu ta tsawatar mata, sannan ta tafi dama haka takeso
Tana shiga dakinta ta kirashi buga daya ya dauko.
"Roohi" ya fada cikin dadadar muryarsa
"Sorry dazu ina tare da Ummu shiyasa ban daga ba, ka taho?" Ta fada cikin k'asa k'asa da murya
"Eh nama kusa"
"Okay toh ka tsaya inda kake se kamin text na k'araso zan fada ma dalili"
"It's everything alright Roohi?"
"Karka damu bawani abu bane"
Katse wayar yayi had'e da faka motarsa gefen titi ya mata text ya zauna cikin motar yana jiranta.
Cikin sauri ta shirya
Salama tayi wa Ummu sannan ta fita, da taimakon text din daya turo mata ta isa wajensa, tun da hangota yake murmushi, fitowa yayi ya bude mata murfin motar sai daya tabbatar ta zauna, sannan ya koma barinsa ya zauna, daddarar kamshin da kuma sanyi Ac ya sata ajiyar zuciya
"I missed you Roohi"
Marairaice fuska tayi
"I missed you more"
Shafa sumar kansa yayi
"Amm meyasa kike ce mu hadu anan? Meya faru?" Ya jero mata tambabyoin
Duk abinda ya faru ta fayyace masa cike da haushi
"Babu me rabamu insha Allahu! Karki bari wannan ya dameki, kinji"
"Insha Allahu, amma inaga kawai ka turo, nasan koda Ummu zata goyi bayan Ya Mubarak, Abba baze bi ba ze so zabin rai na"
"Nayiwa Daddy magana insha Allahu soon komai zai daidaita"
Tana kokari magana wayarta tayi ruri, tana dubawa taga Ya Mubarak ne, tsantsar mamaki ya cikata, cikin nutsuwa ta daga wayar, a ranta tana sak'a irin rashin mutuncin da zata masa, tunda taga alama maganganun da tayi masa a baya basu ishe shi ba, sai dai ,yanayin muryarsa da yanayin yadda ya kira sunanta yasa jikinta yayi sanyi da duk rashin mutuncin data shirya yi masa,
"Idan kina gida ki sanar wa da Ummu cewa zanzo anjima, na kira wayarta a kashe, inda hali kena inasan magana dake"
"Bana gida, amma kaje tana gida ita ba inda zata fita, nikuma in na dawo da wuri to"
"Okay thank you princess" ya katse wayar
Ayaan daya kura mata ido tun sanda ta fara wayar yace
"Ke da wa?"
"Ya Mubarak ne"
Duba agogonsa yayi ,ya kalleta
"Inaga muje in aje ki a gida in wuce akwai abinda zanyi" ya fada yana duban agogonsa
Da mamaki ta kallesa domin ta fahimce cewa kishi yake
"Haushi kaji?"
"Taya bazanji haushi ba, Roohi?"
"Nifa takace nikadai na fada ma hakan tun tuni, ka dena damuwa pls"
"Okay kawai yace batare da ya kara cewa uffan ba
"To smile, in kayi dariya kafi kyau" ta fada tana dariya, dariya ce shima ta subce masa, cike da annusha da tsantsar soyayya ya aje ta a kofar gida ta shiga har saidata shiga sannan ya tada motarsa ya tafi cike da kewarta.Tana shiga falo taji an dokota ta baya cike da mamaki ta juyo taga waye haka? Ruky tagani wani irin juyi tayi ta rungumota
"Ruks! Kinyi suprising dina wallahi"
"Ai dama haka nace zanyi miki zuwan bazata, tunda ke bakya nema na, ni bari na nemeki, shikenan kuma daga zuwan mr right se a manta da besty?"
Janyo hannuwanta tayi " kemu shiga ciki sarkin mita"
A kan gado suka zauna, nan Zahirah ta fayyace mata duk abinda ke faruwa batareda ta boye mata komai ba, shiru Rukyy tayi tana tunanin abin, tabbas Zahirah be kamata tayiwa Ya Mubarak haka ba, ya zama dole ta fada mata gaskiya!
"Zahirah to be honest Ya Mubark be cancanci haka ba, besides Zahirah tunda har Ummu ta sa baki, inaga zefi kyau kibi zabinta ,ki kyale Ayaan ba mamaki K'addarace kawae tazo ta had'aku, bazaku kasance da juna ba"
Wani irin kallo ta aikawa Ruky
"Ruks bansan bak'in baki, nifa gaskiya bazan iya rabuwa da Ayaan ba, Ummu ma da kike k'okarin dole sena auri Ya Mubarak ta sani kokonta, sai naga anya tana so na? Saboda in tana sona ai dole taso abinda nakeso!
"Lallai Zahirah abin naki yafi karfin tunanina, Ummu kike kokonto kota na sanki? Kar so ya rufe maki ido Zahirah, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala baze hango ba, kibi zabin mahaifiyarki zakifi samun albarka"
"Ke Ruks wallahi dana san abinda zaki fada kenan da ban fada miki komai ba, ke da nake tunanin zakibi bayana, nagode zaki iya tafiya Ruks"
Dariya Ruky tayi
"Daga fadan gaskiya? Hada korata? to bari na tashi na tafi yarinya nasan dole kizo ki nemeni har inda nake" tana dariya ta dau jakarta ta fice,
Ummu dake kofa yana jinsu tun sanda tazo kiran Zahirah su gaisa da Mubark taji suna maganar ta tsaya tana saurare, jin alamun Ruks zata fito ya sata saurin dafa kanta wanda ke juya mata ta k'arasa dakinta, wani irin zugi kanta ke mata, dafe kanta tayi tana kiran duk adduoin da sukazo bakinta, da kyar take fidda numfashi, wayarta ta janyo ta kira Asaad dakyar, bugu daya ya dauka, sunanshi ta kira da kyar, kafin tayi wata maganar numfashinta ya s'arke.
Don't forget to vote and comment#NWA
#ZHR
#Hafss
#love you all❤️
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...