09

715 61 10
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
       
               _ZAHIRAH_
                      09
*Miss Hafcy*
         &
*Hauwa Damary*
      
         This page is yours *MEENAPARROT* we really appreciate your love for this book,Thank you.

    Wannan ai mr. Right din nane,!! ta fada cike da dunbin mamaki, mamaki take irin mamanki ba kadan ba ya akai komai yazo daya ya akai.. Kai tambayoyi dayawa ta dinga yima kanta wanda bata da answer dinsu ko daya,  abu ďaya ta sani wannan haďin Allah ne kuma shikadai ya barwa kansa dalilin yin haka.
    Wayarta ta shiga lalalubowa ta kira imra sedai ta nemi number ta rasa har a call log dinta abin mamaki,  Rukky ta kira ta bata labarin komai itama mamaki tayi ta kuma bata shawara ta dan dakata tukun kartai saurin fadawa Imra cewa ta amince dan ana san mace da jan aji,  Zahirah tajita ne  kawai amma bata tunanin zata iya amincewa da hakan. Shiru tai tana kallan hoton xuciyarta cike da farin ciki,  jin an tura kofar ne ya sata saurin maida hoton cikin envelope ta dauko wayarta kamar tana dannawa. 
    "Zahirah baki ji tun ďazu ina kiranki ba?  Hala baki san na dawo bama me kikeyi haka? " ummu ta fada tana yaye laluban ďakin

  "Lah ummu yi hakuri wallahi bansani ba, kinga na dawo kaina na ciwo shine na dan kwanta yanxu ma wayata na dauko ina shirin kiranki" Zahirah ta fada tana sosa keya
   Ummu ta karaso bakin gadon tayi murmushi
   "Mubarak dai ya sami aiki acan abuja ashe shiyasa daya gama bautar kasa be dawo kano gabadaya se dazu yamin waya yace inata kiranki be samu ba kin yada shi ba kadan ba"
   Washe baki " Lahhh Ya Mubarak dina Allah sarki wallahi inata missing dinshi,  Ummu ban numbersa na kirashi namai congrats kinsan tun dana canza layi muka dena waya dashi"
  "zan baki wayar na hannun Assad yanzu ai  a satin nan yace min zezo gidan nan ma"
   "toh shikenan Allah ya kawoshi lafiya.

           *************
    Su Zahirah sunyi hutu na 1week aka basu dan haka yasa ma bata zuwa school gashi abin mamaki ta nemi number Imra ta rasa,  tana ta so ta kira Ayaan amma bata san me zata ce masa ga number dai amma ba damar kira samun Imra shikadai ne mafita tama rasa ya zatayi
    _Salam Princess yau burinki ze cika na ganin masoyinki na hakika ki xamana cikin shiri yau zakiyi arba da masoyinki na gaskiya ki cigabada hakuri saura kiris_
               _Muhammad M_
    Shine sakon data ci karo dashi tana bude wayarta mamaki take takuma ji dadi da yau Allah yasa zataga wannan me damunta din wanda ko sau daya bata taba jin ya burgeta ba balle azo ga batun so.

    Suna zaune. A palour dukkansu hadda Asad suna dan hira jefi jefi., akai knocking kofa da sauri Zahirah ta tashi ta bude ganin Ya Mubark ya sata wangale baki cike da murna ta kira sunansa , ya amsa da naam kanwata sannan ya karaso ciki murna sosaii Zahirah tai na ganinsa dan a zahirin gaskiya tana balain sansa jinshi take tamkar yayanta uwa da daya uba daya dan ita har yanzu bata gama yadda dari bisa dari cewa ba danuwanta na jini bane,  tashi tai da sauri ta kawo masa ruqa da lemo da snacks nan suka gaisa da Ummu tareda hirar yaush rabo.
     Sun d'an jima suna hira inda mubaraq ya tak'ark'are basu labarin gurin aikinsa dake a garin Abuja da kuma irin nasarorin da ya samu,sun nuna farin cikinsu tare da yi masa fatan samun nasara a koda yaushe.
     Tara da y'an mintuna ya mik'e da niyyar tafiya tare da Alk'awarin dawowa kafin ya koma gurin aiki. Har gaban mota suka rakosa sannan suka koma inda suka bar Asaad yana danna waya nan suka sameshi.
    Wayar Zahirah ce tayi k'ara Alamar sak'o ya shigo.
          _slm princess,gani a k'ofar gidanmu_
                   _Muhammad M_
Gabanta ne taji ya d'an fad'i ta kalli inda umma take zaune tana kallo hankalinta kwance tace a sanyaye zata fita tayi bak'o. Umma tace tayi sauri taga dare yayi,"to" tace gami da mik'ewa domin d'akko hijabinta,Umma ta bita da kallo cike da so da kauna
     Tafiya take cike da zullumin ganin Muhammad M,wani 6angare na zuciyarta ke fad'a mata ko d'ai Mr Right d'inta ne,aiko da shine da tafi kowa farin ciki,
   Koda ta fita bata ga kowa ba Sai ya Mubaraq dake k'ok'arin fitowa daga cikin motarsa,Murmushi tayi"ya Mubaraq dama baka tafi ba,ko kayi mantuwa ne?"
  Wani malalacin murmushi ya sakar mata Wanda ya kashe mata jiki kafin yace"eh mantuwa nayi sis na manta Abu mai matuk'ar muhimmanci a rayuwata shiyasa na dawo ko ban d'auke shi a yanzu ba ina fatan in d'auke shi watarana" ya k'arashe maganan yana kallon cikin kwayar idonta.
    "Eyyah ya Mubaraq ai gara ka tafi dashi d'in yau" hannunta rik'e da waya tana k'ok'arin danna number Muhammad M a taro na farko domin ta sanar dashi gata a waje amma bata gansa ba,wayar ya Mubaraq ce dake gaban rigarsa ta d'auki ringing. Kallon mamaki take masa ta kasa gasgata Abunda ke faruwa yanzu fatanta Allah yasa ba abunda take tunani bane,gabanta ne taji yana fad'i cikin k'arfin hali tace"ya mubaraq,dama kai ne Muhammad M?"
   "Uhm" ya fad'a tare da kafeta da ido,gani yayi ta soma ja da baya sai kuma ta juya ta soma tafiya da Sauri har ta koma cikin gida ta barsa nan tsaya yana kallon hanyar da tabi,sai dai hakan bai dameshi ba dama yasan hakan ce zata faru. Yau jinsa yake kamar an sauke masa wani nauyi dake kansa ya amayar da abunda ke cikin ransa shekara da shekaru.
       Tana shiga d'aki ta rufo k'ofa zuciyarta na mata zafi,me yasa?why?meyasa ya Mubaraq zai mata haka a dai-dai lokacin da take ganin ta kusa samun farin cikin ranta,me yasa ya Mubaraq yazo mata a matsayin Saurayi ba yayanta mai k'aunarta ba?why? Batai Aune ba sai ji tayi wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata.
                          *********
       "Ya Imra pls call her wallahi duk na k'agu naji answer da zata bada" ya fad'a yana marairaicewa.
   Harararshi tayi cikin wasa"bro  anya are u in your right sense? Gaskia I doubt,kalli yanda duk ka susuce akan mace Allah gara kazo kayi wa kanka fad'a ,idan ta gane kana sonta sosai u will suffer"
   Sunkuyar da kansa yayi k'asa indai akan son Zahirah ne zai iya jure komai,sai dai wani 6angare na zuciyarsa na fargabar kar tak'i yin accepting d'insa.
      Cikin tunaninsa yaji ya Imra na fad'in"Hello Zahirah are you with me? Imra Tafeedah ke magana"
    Saurin d'agowa yayi yana mata nuni da ta sa handsfree yanda zai dinga ji,banza ta masa ta cigaba da maganarta.
   A sanyaye tace"Ina yini" a ranta kuma taji dad'in kirannan na ya Imra don ba k'aramin farin ciki tayi ba na kiran bazatannan Don ita har ta fara fidda rai,
   A yangance ya Imra ta amsata cigaba da fad'in"sorry kin jini shiru 2days na baki time ne kiyi tunani da kyau,pls I want you to be honest with me ki d'auke ni kamar sis d'inki,now tell me abunda ke cikin mind d'inki"
    Rufe ido tayi a zuciyarta tana jin wani irin sanyi,kunya ce ta lullu6eta bata iya furta tayi accepting.
  Jin tayi shiru yasa Ayaan zuba tagumi yana kallon ya Imraa wacce itama shiru tayi tana sauraren Abunda Zahirah zata fad'a,ji tayi alamar an kashe wayar cike da mamaki tabi wayar da kallo ta kasa d'agowa ta kalli Ayaan,dama Akwai macen da Ayaan d'in zai nuna yana so tak'i accepting a duniya,tana nan d'iyar Governor d'insu ke sintirin zuwa gidanta duk akan son Ayaan amma sai gashi Zahirah da take tunani ba komai ba ta nuna bata ra'ayi. A dai-dai lokacin text ya shigo a wayarta"  _ACCEPTED_" sai Emoji na rufe ido alamar kunya,bata San sanda murmushi ya kubce a pink lips d'inta ba,sai taji Zahirah ta k'ara shiga ranta dama anfi son mace mai Alkunya ba kamar wasu matan Zamaninnan ba da kamar Kira suke ace ana sonsu,wasu ma su da Kansu zasu fara suna son saurayi daganan kuma sai ya fara miki tunanin yar iska.
   Tsalle Ayaan yayi tare da bata side hug "thank you sister,I love you so much"
    Smiling tace"Oya tashi kaje yanzu ya rage naka"
  Da jin dad'i ya baro gidan ya Imra Don ya watsa ruwa ya tafi wajen Abun k'aunarsa.

                  *******
   Ta dad'e zaune tana zaman jiran Answer ko Kiran ya Imra amma shiru,gwuiwarta duk ta shacche,Umma ta lek'o ta kirata tazo ayi lunch tunda tak'i zuwa kitchen,cewa Umma tayi kanta ke ciwo kawai, Asaad suka fara iskewa saman table yana danna waya as usual ta6e baki tayi ta zauna ba tare da ta gaishe shi ba,ya d'ago idonsa tare da zabga mata harara,baka ko nuna ta damu dashi ba ta zuba ma su Umma Abinci da Abba ta zuba nata ta soma ci.
    Da yamma suna kitchen da Umma suna tuk'a tuwo,Umma ke sanar da ita d'azu Mubaraq ya kirata dam Zahirah taji gabanta ya fad'i,Umma ta cigaba da fad'in yace zai shigo sati mai zuwa,itadai Zahirah bata ce komai ba ta cigaba da kad'a miyar kuka wacce tasha kifi sai k'amshi take.
   Bayan sun gama ta nufi d'aki don yin wanka,wayarta ta diba taga anyi mata 2missed calls da wata number sai dai kaman an ta6a kiranta da number, kira tayi ringing biyu Aka d'auka cikin taushin Murya aka ce"Hello"
   Itama hello d'in tace
  Yace"nasan baki San mai magana ba,kina magana da Ayaan Tafeedah"
   Ras! Taji gabanta ya fad'i...........

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now