08

717 65 8
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
         
                 _ZAHIRAH_
                         08
*Miss Hafcy*
          &
*Hauwa Damary*

Cike da mamaki mummy ke kallon daddy wanda fuskarsa ke d'aure tamau ba alamar wasa cikin furucinsa. Juyowa tayi ba tare da tace ma kowa komai ba ta nemi waje ta zauna bisa dining table inda Azeema da Fahad ma suka rufa mata baya suna k'unk'unai cikin ransa.
  Abinci suke ci babu mai cewa komai kowa da abunda yake sak'awa cikin ransa inda daddy yaci Alwashi cikin ransa cewa zai gyara yanayin zamantakewar iyalansa, ya Imra ce farkon tashi sakamakon mijinta da yay mata waya shima Ayaan tashi yayi yayi masu sallama ya fita, tab'e baki mummy tayi  ta  cigaba da cin abincinta.
              ******
      _slm barka da warhaka sarauniyar farincikina,ina mai tabbatar miki da cewa gab nake da na bayyana kaina a gareki, nine naki mai kaunarki har kullum_
               _Muhammad M_
  Ajje wayar tayi a gefe bayan ta gama Karanta text d'in, sai dai wani 6angare na zuciyarta na mai k'osawa da son ganin M.M d'innan.
  Sai da ta gama shirinta tsaf sannan ta leqa d'akin umma domin ta sanar da ita zuwa gidansu Aminiyarta rukky sai dai tayi rashin Sa'a kwance ta isketa tana bacci kuma bata so a tasheta Idan tana bacci don haka sai ta yanke shawarar tafiya kawai da yake sunyi maganan d'azu dama wai ta tuna mata ne. Asadd ta gani zaune bisa motarsa hannunsa riqe da waya yana dannawa, ta gaishe shi don gudun tayi laifi amma bai d'ago ya kalleta ba balle tasa ran zai amsa, baki ta ta6e don ko a jikinta Idan ya amsa don kansa Idan bai amsa ba ma don kansa ita dai tayi nata.
   Inna ta iske zaune tana gyaran wake a tsakar gidan ta rusuna har k'asa ta gaisheta, dattijuwar wacce ta zata wuce shekara sittin a duniya ba ta d'ago ta amsa da fara'a tare da tambayanta Ummanta, tace tana lafiya tace a gaisheta, tace tana amsawa daganan ta shiga kiran Rukayya ta amsa daga k'uryar d'aki sai gata ta fito daga ita sai vest da dogon wando hannunta rik'e da mafechi sai faman fita takeyi
Tsalle Ruky tayi ta mak'aleta"oyoyo k'awata Yaushe rabon da in ganki an kusa sati rannan naje gida umma tace kina makrantar koyon girki nan na zauna muka sha Hira da ita"
   "Ta fad'a min wallahi kuma na kira wayanki sai ace min a kashe shiyasa nace dai bari nazo naga ko lafiya"
   Ruky taja hannunta"ke muje d'aki kiji, wallahi wayata saceta akayi rannan naje rijiyar zaki amso ma inna sak'o"
  Zahirah tace"haba no wonder shiyasa kullum bani samunki" dai-dai nan wayarta ta k'ara yin k'ara alamar shigowar sak'o,
             _duk ranan da na bayyana miki kaina kinyi bankwana da hawa napep don ina kishin wani d'a namiji ya dinga kallonki_
               _Muhammad M_
Tun kafin ta k'arasa karantawa Ruky ta fizge wayar tana fad'in"waye haka ya d'auke miki hankali ina magana kin shareni" ta shiga karantawa"Hegiya sai kice min new catch kika yi ko Mr right d'inne"ta k'arashe cike da zolaya.
Zahira ta amshe"bani dalla,  tsaya kiyi wallahi wannan bansan ko waye ba"daganan ta bata labarin yanda yake mata text kusan kullum.
   Ruky tace"tabbas ko waye wannan ya sanki sosae farin sani ma, kiyi tunani ko cikin yan uwan umma babu mai suna Muhammad?"
   Tace"akwai mana sai dai bani tunanin cikinsu za'a same shi"
"To muyita Addu'a Allah ya bayyana shi kuma Allah yasa na aure ne"
  "Hmm" kawai Zahira tace a ranta tana tunanin yanda zata iya Auren wani ba Mr right d'inta ba.
   Sun cigaba da fira ta yau da kullun kafin tayi shirin tafiya gida kasancewar mangariba ta fara kunno kai.
                *******
Y'an kwana biyunnan gabaki d'aya ya k'ara susucewa kan tunaninta baya da wani abu da ya wuce tunaninta gashi ko yaje gida ba wani kwanciyar hankali daga mummy tace kaza sai tace kaza, sauk'in da yake samu Idan ya fito aiki dai-dai time d'in da ake tashi su Zahirah yake samu ya tsaya nesa da su yana kallonta har su tafi. Agogon sake bangon office d'in ya kalla saura minti biyar biyu tayi, cikin hanzari ya mik'e gani yake kafin ya sauka ma ta tafi yau gabaki d'aya yayi latti, yana shirin fita akayi knocking k'ofar tare da shigowa ya imraa ce, ya gaisheta da fara'a a fuskarsa, tace"ina zaka ne haka kake ta faman Sauri?"
   Ya shiga sosa k'eya, murmushi tayi ta fiddo sarkar zinari daga cikin Jakarta wacce kud'inta zai kai miliyan ta mik'a masa tace"gashi ka kai ma mummy dama abunda ya biyo dani kenan"
   Ya sa hannu ya amsa amma hankalinsa gabaki d'aya ya tafi ga Zahirah.
   "Wai meke faruwa ne ina maka magana kamar baka saurare kuma wannan raman da kayi ta mecece? Meke damunka? Yanzu ashe har kana da wanda ya fini da bazaka iya zuwa ka fad'a min damuwarka ba?  To nagode" ta juya zata fita a fusace, yayi saurin tararta ya marairaice kamar zaiyi kuka yace"please sis karkiyi fishi dani wallahi nima kwana biyu na rasa meke damuna gabaki d'aya tunaninta ya mamaye min ruhina ko mai nike sai in dinga ganinta,na rasa yanda zanyi please help me out"ya k'arashe yana goge kwallar da ta zubo masa.
   Ba k'aramin tausayi ya ba ya imra ba tace"sorry bro, be a man mana ka share hawayennan yanzu ni zanje na sameta na mata magana ko ya ka gani?"
Saboda murna baisan sanda yayi hugging d'inta ba. Lambar Zahirah ta Amsa tace zata kirata Idan taje gida, ya matsa ta kirata a nan, ba yanda ta iya dole ta kira zahirah ko don ta faranta ran k'anin nata.
        Fitowarsu kenan daga makaranta tana Sauri ta tafi gida don yau basu gama da wuri ba sakamakon yau baking sukayi, kamar kullum yau ma d'anfillo mai napep yana nan yana jiranta itako yanzu har ta gaji da tambayarsa dalilin da yasa baya amsar kud'inta kuma kullum sai yazo d'aukarta, idan ta tambayeshi sai yayi dariya yace zai sanar da ita akwai sauran lokaci.
   Wayarta dake cikin sidebag d'inta ce ta soma ruri tayi saurin fiddowa don a tunaninta umma ce sai dai bak'uwar lamba ce ta d'auka da sallama daga d'aya b'angaren aka Amsa"Sunana Imratu Tafeeda, idan babu damuwa inason yin magana dake ki bani minti biyar ki sanar dani inda kike gani nan zuwa"
Hakanan sai taji matar da ta kira kanta da Imratu tayi mata kwarjini bata iya ce mata a'a sai dai kuma tana so taje gida tun kafin umma ta fara damuwa, sai dai bata san ya akayi ba sai ji tayi tana sanar da matar tana gaban Tafeeda&sons tace to gata nan tafe, wayar ta tsufa ma ido bayan da ya imra ta kashe.
    Ya Imra ta kalli Ayaan wanda tunda ta fara wayan yake Addu'a Allah yasa kada tak'i amincewa  sai gashi cikin ikon Allah ta Amince koda ya Imra zata fita ji yayi Tamar ya bita suje tare, amma yasan ba zata bari.
 
       A nutse ta fito daga office din Ayaan ta nufi wajen motarta ta bud'eta ta shiga,  wayarta ta zaro ta kira Zahirah wadda ta sheda mata tana gindin wata bishiya dake bakin gate din skul dinsu, tada motar tayi ta k'arasa wajen tun daga nesa data hangota take yaban hallitar ta da kuma nutsuwarta wanda kallo daya zaka mata ka gane hakan, fuskarta dauke da walwala ta karaso wajenta
  "Asalamu alaiki" ta fada tana kallon Zahirah wadda ta amsa mata sallamar nan take.
   Miqa mata hannu tayi suka gaisa sannan ta sake gabatar mata da kanta a karo na biyu
   "muje mota muyi magana koh?  Inaga kamar zefi"
   Shirun da Zahirah tayi tana kallanta ne yasa ta cewa
  "kar ki damu,  kuma kada kiji tsoro bazan cutar dake ba namiki alkwarin hakan"
  Murmushi Zahirah tayi sannan tabi bayanta har zuwa gaban motar, wajen driver imra ta shiga yayin da Zahirah ta zauna a wajen me zaman banza.
  
    Dogon numfashi Imra taja sannan ta fara magana kamar haka
   "Nasan zakiyi matuk'ar mamaki ganin wadda baki taba ganinta ba ta kiraki harma tana san kuyi wata magana da ita,  nasan zuciyarki na kawo miki sak'e sak'e dayawa kuma cike take da kaguwa najin abinda nazo miki dashi,  ki kwantar da hankalinki da alheri nazo miki bada sharri ba.
    Na fada miki sunana a baya so ina ganin maimaitash kamar bata lokaci ze xamo mana,  nidai da kika gani inada wani k'ani wanda na dauki san duniya na dora masa,  bazan iya kwatanta miki yadda nakejinsa a zuciyata ba, *MUHAMMAD AYAAN TAFIDA* damuwarsa a duniya daya ce tal itace samunki a matsayin abokiyar zamansa ta dindin a duniya harma da alheri.
    Da sauri Zahirah ta dago ta kalleta cike da mamaki har bata san sanda ta firta
    "waye haka kuma? Aina ya sanni?
   "na daure ki da jijiyoyin wuya koh?  Imra ta fada yayin data dafa kafardarta
    "eh na kasa gane abinda kike nufi kimin bayyani dala dala ta yadda zan gane please... " Zahirah ta fada tana kallon Imra.

    Cikin nutsuwa tayi mata bayyani komai da komai sai dai kuma a bangaren Zahirah an barta cikeda da tunane tunane kalla kalla a zuciyarta waye kuma haka?  Abinda ya bata mamaki shine yadda itama a nata bangaren takeyiwa Mr. Right dinta, labarin su yana shige sedai kawai banbanci da aka samu,  ikon Allah ashe itama tana da wanda yake mata irin san datakeyiwa Mr. Right?  Abun ya bata mamaki matuqa. Ganin shirun datai ne yasa Imra dan taba ta yadai?
    "banma san me zancen ba wallahi,  zuciyata ta kasa tsaida magana d'aya danake ganin zan fada har ta gamsar dake,  sai dai watakila idan na samu nutsuwa zan sami amsar datai daidai da abinda kike son ji daga gareni,  ki bani lokaci zanyi tunani akai nagode"

  Murmushu Imra tayi "dole dama zan baki lokaci Zahirah saboda abinda nake tafe dashi babban lamari ne wanda yake bukatar tunani da kuma nutsuwa, nasan kamarki bazeyiwu ace baki da tsayyaye wanda kikeso ko yake sanki ba, amma fa ki sani ita kadddara bata duba ra'ayin mutim takan zo a kowani hali, bazan miki fatan rabuwa da masoyinki ba bakuma Zan miki fatan rasa gwarzon namiji kamar Ayaan ba, bawai ina yaban sa ne saboda kasantuwata yaruwa a gareshi ba,  ko kadan!  Ina fadan abinda mutane da dama wanda suke makusanta da wanda basu da alaka da kuma kusanci dashi ke fada,  Ayaan namijine!  Wanda ko wacce mace zatai fatan samu"
    Bude jakkarta tayi ta dauko wani envelope me kyan gaske wanda a kasansa ansa *AYAAN TAFEEDA* ta mika mata wannan ya kunshe wasu yan bayanai akan Ayaan ki nustu ki karanta a duk sanda kika yanke shawara zaki iya kirana am always available nagode sosaii da kika bani time dinki,  thank you so much. Zaki iya tafiya sai anjima" ta fada tana murmushi.

    Jiki a sabule ta mata sallama ta fito daga motar abubuwa kala kala zuciyar ke saka mata,  hakik'a yau tazamo wata rana da zata sa a kundin tarihinta wanda take tunanin bazata taba mantawa da ita ba. Danpillo me adaidaita dinta data hangone ya katse mata tunani ta karasa wajenshi ta shige bata sake cewa uffan ba tun bayyan gaisawarsu.

   Tana shiga ta tadda Ummu bata nan wanda ba karamin dadi hakan ya mata ba dan bata san ta gane irin yanayin data shiga direct dakinta ta shiga ta shiga tiolet ta watsa ruwa sannan ta fito tayi sallah taci abinci envelope din nan ta dauko tana me yabansa duba da yadda aka tsareshi ggwanin ban shaawa,  gabantane ya fadi a daidai lokacin datake kok'arin budewa d'an complimentary card tagani wanda ke kunshe da sunansa da kuma rank dinsa wato CEO na Tafeeda and sons ltd.  Wani abu ta gani kamar hoto da sauri ta janyo shi ta duba,  k'ara kallon hoton tayi a karo na biyu ta zaro ido
   "  *What!!! Wannan ai..*

   __We are back, yes mun dawo da karfinmu insha Allah ze dinga zuwar muku akai akai ku cigabada hakuri.  Love you all._
     Dont forget to vote and comment 💖💖🌹

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now