27

376 34 7
                                    

"Aa Zahirah ya zama dole mu nemo mahaifinki, sai dai kiyi hakuri" Ummi ta fadai tana gyra zamanta
Tashi tayi ta bar wajen da gabadaya bata aminta da abinda suke fada ba
" kinga abinda yasa kenan nace su Amina su dakata da turowa har sai mun nemo mahaifin Zahirah, amma banga laifinta ba ya cancanci komai, sai dai zefi ma'ana idan aka gano shi din" Ummi ta fada tana kallan Ummu
"Gskia ne Adda Zainab nima haka nace, amma taya ma zamu fara nemashi?"
"Dan Gombe zamu samu sai mu tambya, Ummi ta fada
"Kai aikuwa kamar na tabajin Asad yanada wani aboki a Gombe har yaje daurin aurensa kwanaki, bari na kira Asad din yazo muji" Ummu ta fada tana dailing number Asaad.

Ya Mubarak ya shigo dauke da cards na biki a hannunsa, bayan sun gaisa dasu Ummu ya tambayi ina Zahirah take, a can falon baki ya taddata tayi uban tagumi ta kurawa Tv ido duk da hankalinta baya kai, salamarsa ce ya sata saurin dagowa

"Hmm Ya Mubarak shikenan daga haduwa da Xoxo sai ka mata dani?" Ta fada bayan ta amsa salamar
"Ba haka bane sis, kaina ya dau chargy ne wallahi kinsan sha'anin biki"
"Hmm kawai dai ka canza amma da kowani irin chargy kan ka ya dauka ai baka mantawa dani"
Dariya yayi
"Kinsan me, Xoxo zatayi bridal shower and i want you to be the planner inasan kiyi min planning komai da kudin da zaa kashe, komai dai duk ke zakiyi"
"Wow, toh ba matsala, for the survivors ta kawo list din wanda zata gayyata sai ayima kowa box da sunanshi, zeyi kyau, abindq zaaci kuma zanyi desserts sai na kira Zeenat ta tayani munyi, kasan inata planing inasan zan bude eatery" Zahirah ta fada cike da murna
"Masha Allah, our chef, shiyasa nake jima Ayaan dadi zeci girki kala kala har sai ya ture, hakan ma yayi, though ina ganin kaman yayi late saura 2weeks fa"
"No ba matsala karka damu"
"Okay then bari na baki no dinta sai ki kirata kuyi magana, ga katin daurin aure nan ki bama Ayaan,"
"Kai ya Mubarak har an bugo card?" Ta fada tana daria
"Ba dole ba," ya fashe da daria
"Bari na miki sending kudin koh"
"Aa ka bari tukuna muyi magana naji komai, karka damu zan kiraka bayan mun gama mgna" ta fada tana murmushi

"Se naji labari mai dadi, ashe ummu ta hadu da yar uwarta?" Ya Mubarak ya fada yana gyra agogon hannunsa
"Har ta bada labarin wacece ni ba" Zahirah tayi saurin fada
Hannu ya daga alamun ta dakata dan shi besan a maimaita zancen sannan yace
"Naji komai"
"Ya Mubarak pls be sincere idan kaine a shoes dina, zaka so mahaifin naka? "
"No.. Not at all... amma Zahirah ki yarda a nemoshi din tunda har su Ummu sunyi insisting"
"Toh shikenan Ya Mubarak amma wallahi bazan taba sanshi ba"
"Na goyi bayanki ta wannan sis"
Zama sukai suka cigaba da tsara bikin Ya Mubarak.
******
Tun bayan da Ummu tama Asad Bayanin komai, ya dauki wayarsa ya shiga dailing number abokinsa Abba Gombe bugu uku ya dauka
"Comrade yane"
"Lafiya lau wallahi , ya amarya?"
"Lafiya qalau"
"Dama bugowa nayi na tambayake ko kasani wani a Gombe nasanka da curda curda"
Dariya yayi sannan yace inajinka
Asad ya kalli Ummi yana tambayarta sunan ta fada masa
"Yauwa Abdulrauf Muaz"

"Hon. Abdulrauf Muaz dan majilisar taraya? to wannan waye be sanshi ba, kodai bashi kke nufi ba?"

"To maybe amma shi wannan yayi service dinsa a anan Bichi"
"Ahhh shine ai mutumin mune,lafiya dai koh?"

"Lafiya lau address dinsa muke san sani idan ba damuwa"

"To gskia yanzu be zama a Gombe yana abuja a gidajen yan majalisu gida na 6 anan yake"

"Toh nagode " Asad ya fada yana kai dubansa gasu Ummu dake saurara

"Toh abin ma yazo da sauqi, yaushe kike gani zaaje?" Ummu ta tambayi Ummi

"Saidai ko bayan bikin Mubarak saboda nan da 2weeks ne, yanzu dai da munje mun karasa siyayyar kayan kitchen din nan, naji kince idan sun tashi tambaya da sa rana duka zaa hada kuma ba wani nisa"

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now