11

625 57 2
                                    

 
Basu dauki wani lokaci ba suka iso, Su mummy dake jiran isowarsu sukai sauri zuwa hade da rungumeta
"Ayrah baby nayi missing dinki so much" Mummy ta fada bayan ta rungume Ayrah
I missed you more Aunty thank you so much" Ayrah ta fada tana murmushi,
Azeema ta karaso da sauri ta dungure mata kai "stupid girl, tunda ni bakiyi missing dina ba ai ni nayi""
Rungumeta tayi suka fashe da dariya, Ayaan dake tsaye yana kallansu ya shige mota wanda suka bishi a baya suka nufi gida.

*******
Shigar Zahirah dakinta yayi daidai da shigowar Ummu wadda ke jiran isowarta tun dazu, sosa keya Zahirah tayi sannan ta karasa dakin nata
"Sannu Ummu" ta fada tana kallan Ummu.
"Yauwa Zahirah har yanzu banji amsar ki game da zancen Mubarak ba, lokaci nata kurewa tunda kin gana catering school din nan inasan ayi maganar auren ne"
A iya kwanakin nan bata taba jin faduwar gaba irin ta yanzu ba, tai kokarin daidaita kanta amma fuskarta ta nuna k'arara yadda kalaman Ummu suka girgizata, ta sunkyar da kanta cikin nutsuwa
"Ummu ki gafarceni, amma bana jin zan iya auran Ya Mubarak, akwai wanda nakeso Ummu kin san da haka, kiyi hakuri in kalamai na sun bata miki rai"
Dogon numfashi Ummu taja ta runtse idonta
"Kamar yadda na saba gaya miki haka yau ma zan fada miki, kije ki sake tunani"
Bata jiran amsarta ba ta fita ta barta nan ta zubda kwala, k'arar wayar data ji ta duba kuma taga Ayaan ne ya wanke mata komai dake ranta ta dauki wayar cike da farin ciki suka hau hirarsu kamar ba itace ke zubda hawaye yan mintuna kadan da suka wuce ba.

Mummy ce da taimakon me aikinta ke jera breakfast akan dinning, su Azeema dake palour taiwa alamun da suzo abinci is ready dukansu kuwa ba shiri suka zo kan dinning din, kowanne ya zuba abinda ze iya ci suna ci suna hira cike da nishadi mussman Ayrah datake jin wani farin ciki sake haduwarsu.
Ayaan ne ya shigo cike da walwala saida ya gaida Mummy sannan ya kalli ayrah
"Ayrah ya kwanan Nigeria?"
Washe baki tayi "dadi sosaii"
Dan murmushi yayi ba tare da yayi magana ba
"Ka zauna ma kayi joing dinmu" mummy ta fada tana kallanshi
"A'ah munyi da Ya imra zata aiko min da dumame shi nake shaawar ci yau"
Tab'e baki mummy tayi tace okay sannan yabar wajen yayi hanyar dakinshi bayan yaji alamar shigowar sakon karta ta kwana(sms) wanda ya tabbata Zahirah ce ta aiko masa dashi.
Tunda ya zaune yaga lokaci yayi daya kamata su Mummy su san da zaman Zahirah domin shi harga Allah ya kagu sosaii yaga Zahirah ta zama malakinsa, tashi yayi da sauri kamar wanda aka zungura ya nufi dakin Mummy.
A zaune ya ganta gefenta Ayrah ce a zaune suna hira, dan jim yayi kafin ya k'araso
"Barka da yamma Mummy"
"Yauwa barka Ayaan, baka fita bane yau?"
"weekends ne fa yau ki kin manta?"
Dan murmushi tayi hakane fa sannan suka gaisa da Ayrah wadda tayi tsuru tana kallansu, dan tsayawar da yayi yasa Mummy ta fahimci akwai abinda ya kawosa
"Yadai?"
"Dama magana zamuyi amma naga kaman ur busy ne yanzu"
Se a lokacin Ayrah ta dago
"Bari na fita" bata jira amsarsu ba ta fice, dogon numfashi yaja
"Mummy dama na samu wadda nakeso na aura!"
Da dan sauri Mummy tace
"Wacece ita?"
"Sunanta Zahirah, naga mun fahimce juna ne kuma Ya Imra ma tasan komai shine nai deciding bari na fada miki"
"Akwai wadda naso maka Ayaan, amma tunda akwai wadda kakeso shikenan , zan fadawa Daddyn ku zamuyi magana akai, amma kasani dole ya kasance ita din yar manya ce i mean yar masu kudi kagane ai"
Tunda Mummy ke magana yake mamakinta
"Amma Mummy....."
Hannunta ta daga masa wadda suka sha ado da warwaro da zoben gwal
"Dakata! Kadai ji abinda nace zaka iya tafiya"
Jiki a sanyaye ya bar wajen cike da takaicin hali irin na Mummy.

**********************
Tunda ta zauna take ta tunanin masoyin nata jefi jefi takanyi murmushi, cike da nutsuwa Ummu ta turo kofar dakin, murmushi ta sakar mata sannan ta zauna a bakin gadonta
"Zahirah har yanzu banji daga gareki ba"
Dan tabe baki Zahirah tayi
"Ummu ki gane, wallahi bazan iya rabuwa da Ayaan ba! shi nakeso kuma shi nake san aura,baza iya auran Ya Mubarak a matsayin yaya na daukesa dan girman Allah Ummu ki bar maganar nan..,,".
"Koda hakan ze iya zama silar b'acin rai na?" Ummu ta katseta
Sunkuyar dakai Zahirah tayi cikin sanyin murya tace
"Kiyi hakuri Ummu bansan bacin ran ki ke kinsani amma a wannan batin gaskiya...,"
Cike da tsaninin mamaki Ummu ke kallan Zahirah da har ta sami kwarin giwar fada mata wannan kalaman, kenan tana nufi ta fifita wani can daban akanta, bata ce uffan ba ta tashi cikin sanyin ciki ta bar mata dakin.

***********
Yadda Ayaan yaga Mummy kamar bata dauki zance da muhimanci ba ya sashi yanke shawarar tunkarar Daddy dake home office dinsa yana aiki.
Cike da nutsuwa ya gaida Daddy wanda ke signing wasu papers dake gabansa, batare da ya kalli Ayaan din ba ya amsa bayan sun gaisa Ayaan yace
"Daddy dama na samu wata ne mun fahimci juna, shine nakesan maka magana a nemanman auranta"
Biro din Daddy ya aje
"Wacece ita? Kum yar gidan waye?"
Nan ya fada masa iya abinda ya sani game da ita, jim Daddy yayi
"Bakomai zan kira kawunka na masa magana se muyi bincike akai "
"Daddy da kawai zuwa kukai akai maganar auren se naga kaman binciken bata lokaci zeyi"
A dan fusace Daddy ya dago
"Ayaan me yasa kake abu kaman wani k'aramin yaro ? Shekararka talatin amma kana acting kaman dan shekara 10 ina ka taba ganin anyi aure ba tare da anyi bincike ba?"
Sosa keya Ayaan, nan ya gano laifinsa be kamata ya tunkuri Daddy a lokacin dayake tsaka da aiki ba
"To daddy a huta lafiya ya fita.

Ummu tana shiga dakinta ta fashe da kukan daya tsaya mata arai tun tana dakin Zahirah, kuka sosaii take wanda ita kadai tasan dalilin kukan, Asaad dake lab'e yana jin duk abinda ya faru ya biyo Ummu daki a fusace
"Ummu akan waccar abar kike zubda hawayenki? Wallahi se tayi namadar saki zubda hawaye , tunda nake dake Ummu duk hawayenki da zangani dalilinta ne, lokaci yayi da zaki dena zubda hawayeni akan waccar banzar yarinyar, barni da ita yau se tayi dana sani shigowarta duniya"
Yana k'okari fita cikin daga murya Ummu tace
"Asaad!!!!"

Assalamu alaikum, ya kuke ya kwana dayawa, Duba da yadda mutane dayawa ke cewa na cigaba da wannan novel ya sani dawowa dashi tare da dakatar da wanda na fara yan kwanakin da suka wuce, amma ku sani yawan comment da votes dinku shi ze bani kwarin gwiwar cigaba da muku updates akai akai

#NWA
#ZHR
#nagode💖👍🏻

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now