33

283 24 3
                                    

Haka nan ta gaji ta aje wayar, gabadaya ta rasa sukuni, kwankwasa kofa akayi, Ayrah ce tare da Azeema suka shigo da murmushi ta tarbe su kamar ba abinda ke damunta, suka shigo, jera musu lemuka da ruwa da snacks tayi a gabansu.
"Ya Zahirah dama kin bashi dinki zamu kai fa muka wuto ta layinku shine muka biyo yanzu ma zamu tafi" cewar Azeema tana gyra mayafinta
"Kai Azeema har ina murna na samu 'yan hira pls ku zauna"
"Tabb ina muka ga ta zama bikin frnd dina zaayi gobe fa shine sai yau zamu kai dinki gashi a yau muke san ya mana" cewar Ayrah
"Lallai to bari na sa snacks din a takeaway ko a mota kwaci, kuma Allah ya kaimu naku musha biki"
"Ameen dai, nidai na kama dahir saura ke Azeema" Ayrah ta fada tana dariya
"To nima aka ce miki ban kama ba? Ai in sha Allah year din nan kan ta kare muna gidan maxajen mu" Azeema ta karasa maganar tana rufe idanta
"Ameen in sha Allahu kuwa" Zahirah ta fada cike da murmushi
Sukayi salama suka tafii.

Sai can yamma Ayaan ya dawo gidan dauke da salama , amsawa tayi da sauri tana karaso wajensa, da sauri ya kauce yayi hanyar dakinsa bece mata uffan ba, a wannan gabar ta kai bango dan abinda ta tsana wulakanci mussaman idan ta hadiye komi ta aje pride a gefe, dakinta ta shiga taji gabadaya komi ya mata zafi ashe dama haka zaman auren yake? Nasihohin Ummu ne suka shiga dawo mata, ajiyar zuciya ta saki ta nufi dakin nasa, yana zaune yana saka wata paper a briefcase dinsa ta shigo, salama tayi ya amsa a fisge, karasowa tayi daf dashi
"Wai dan Allah me na maka? Me yayi zafi haka?" Sai kuma ta fashe da kukan data dade tana rike shi
Rikota yayi a gigice ya fara lallashinta sai dai kuma kamar kata mata yakeyi, dkyar ta danyi shiru
"Kukan me kikeyi?"
"Bakai ne ba" ta sake fashewa sa kuka
"Sorry baby boo yi hakuri kinji, dena kukan toh"
"Ka dena fushin dani?"
"Eh na dena, im sorry pls, dena kuka"
Murmushi ta sakar masa
"Toh muje ga abincinka akan dinning kaci"
Tsgi yayi da sauei ya bi bayanta zuwa dinning din.

BAYAN SHEKARA 4
Abubuwa da dama sun faru na farin ciki da sabin haka, Azeema, fahad da Ayrah sunyi aure suna zaune lafiya a gidajensu, Ya Asad ma  ya auri kyakyawar matarsa Khadija, Matar Ya Mubarak ta haifi kyakyawar 'yarta wadda taci sunan Zahirah, Ya Imra ma ta haihu da na biyu, Ummi kuwa ta dawo Nigeria da zama gabadaya ,dan dama Babansu Ayrah aiki ya kaishi can kuma ya gama, Inna da Baba na zaune na lafiya cikin kulawa, company din Ayaan nata kara habaka, hakan yasa ya bama Zahirah jari itama ta bude  culinary school da kuma restaurant wadda ta samu karbuwa ba kadan ba, Cikin lokaci kankani ta fara samun makudan kudi, anan ne har ta biyama kanta Hajj sukaje itada da Ayaan da Ummu da niyyar tayi ma mahaifiyarta dan ita last year Ayaan ya biya mata sun sauke farali, zama suke cike da so da kaunar juna sai dai kuma har zuwa yanzu Zahirah ko batan wata bata taba yi ba balle ya kai ga haihuwa, tana damuwa sosaii sai dai yadda taga Ayaan din be damu sosaii bane yake sakata k'in damuwa sosaiii.

******

Ayaan na zaune a palour a gefensa Mummy ce zaune akan kujera suna taba hira, kasancewar yazo gaisheta, gyra zaman gilashin ta tayi ta kallesa
"Ayaan nikam lafiya kuwa? Naji shiru har yanzu Zahirah ko batan wata kodai akwai abinda kake boye min bansani ba?"
"Babu komai Mummy, Allah ne beyi ba"
Wani irin kallo ta watsa masa
"Ayaan, inaso ka gane wani abu, baze yiwu fa ka zauna da ita hka nan ba, anya kuwa ba yar gidan kawata Hajiyan Azare zan nema maka ba? yarinya me hankali kaddara ce ta fito da ita gidan miji"

Dagowa yayi da sauri harda razana wadda yasa Mummy ta maida hankalinta kacokan kansa"
"Mummy aure fa kenan kike nufi na k'ara?"
"Eh"
"Mummy kiyi hakuri amma wallahi sam banda niyyr kara aure, besides Allah yace maza su kara aurene idan har sun yarda zasuyi adalci, kiyi hakuri amma ban tunanin zan iya kamanta adalcin nan, da inyi in jefa kaina da halaka gwanda in zauna da matata komai nufine na Allah,"
"Lallai to kuwa indai haka ne, ka dauketa kuje asibiti a duba ku, ko mene zaa gano, zan baka no din Dr Naja ka kirata kaji sai kuje"
Wayarta ta zaro ta shiga duba no din Dr. Naja,  ba dadewa ta turo masa, beyi musu ba ya amsa da toh ze kirata kuma in sha Allahu zasuje wajenta gobe. Nan sukayi sallama ya koma gida.

Tun dare ya fada ma Zahirah yadda sukayi da Mummy, bata yi mamaki balle ta musa, dan dama tayi tsanmain haka daga gareta, da safe suka shirya wajen doctor Naja, bayan sun gaisa, nan da nan ta gane shi test suka je aka musu sannan suka zaune a reception suna jiran sakamakon test din data musu,
Bayan dan lokaci kadan Doctor Naja ta dawo rike da wata paper a hannunta, tare da yiwa Ayaan alamar ya biyota zasu yi magana
"Bari naje take care Baby boo"
"Okay love" ta fada jiki a sanyaye dan kwatakwata tun da suka zo take jin jikinta wani iri.

Dr. Naja ta juya kujerarta sannan ta dan gyra medicated glass din dake fuskatarta sannan ta kalli Ayaan tace
"Mr. Tafida ka san da cewa matarka na shan magungunan hana daukar ciki?"

Assalamu alaikum😊☺️ ya kuke all?

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now