"Wani irin kallo me cike da fasara kala kala Inna ta wurgawa Zanira sannan tace
"kinga magajiya kyaleta, fada min" Ta fada tana matsowa kusa da magajiyar"Yo ai abu ne me sauqi wasu magunguna ne na gargajiya dazu ma na bawa wata, bama se munje asibiti ba dan kudi zasu tsuga mana, karki damu"
Murmushi tayi sannan tace Zanira ta basu waje
Can gefe ta tsuguna tana Kuka, Zainab ta fito daga dakinta ta dago fuskarta
"Na tausaya miki Zanira ina jin duk abinda kukayi, so masifa ne, so mugun abu ne, so makaho ne,nima shi ya kawo ni wannan hali, daga iyayena sunce bazasu aura min wanda nake so ba na fito na shigo duniya bayan shima ya gujeni, amma naji dadi da kika ce bazaki zubda ba, koda sun baki maganin karki yarda, duk wata damuwarki kizo ki dinga fada min kinji"
Gyada kai tayi kawai, Inna tazo ta jata suka tafi gida, washegari ta kawo mata magnanin, Zanira na daki tana istigifari tana kuka Inna ta banko dakin
"Karbi ki sha agabana nasan halinki" ta fada tana mik'a mata kofi cike da ruwan magani
Karba tayi tana kuka , a haka ta sha, mintuna kadan cikinta ya fara murda mata ba shiri ta tashi da sauri ta amayar dashi, a fusace Inna ta karaso"Wallahi duk aman da zakiyi se kinsha maganin nan, cikin nan se ya zube" ta d'ago ta ta sake dura mata
Bata dade da sha ba Ta sake amayar dashi saboda tsananin d'acin maganin, a fusace Inna ta k'araso inda take
"Au sai da kika sake amayar dashi? Bari kiji na fada miki , komai zakiyi se maganin nan ya zauna a cikinki ko yayane" ta k'arasa maganar tana tura mata kofin maganin
Tana kuka ta sake karba ta sha, ba dadewa ta sake amayar dashi, tsugunawa tayi tana kuka me ban tausayi, a birkice Inna ta duma mata dundu, wani irin k'ara tayi tana kuka cike da azaba, duka Inna ta shiga kai mata ta koina , tana kuka amma Inna bata saurara mata ba, sai data gama dukanta sannan ta koma gefe tana kuka kamar ranta ze fita"Na shiga uku kin cuceni Zanira, Allah ya isa tsakanina da wanda ya miki cikinan" ta fada tana rusa kuka
A dadafe Zanira ta karaso ta rungume Inna suka fashe da kuka gabadayansu
Dafe kai Inna tayi
"Ashe duk abinda kayi se ya dawo maka? Kiga yarda nayita gudun daukar ciki sanda ina bariki na, sai gashi akan yata ta cikina, bariki beba, Allah ya tsinewa bariki" ta karasa maganar tana kuka"Na dauki wannan a matsyain kaddara, Allah ya yafe mana" Zanira ta fada da miryar kuka
" ameen, amma Zanira dole ki hakura mu zubda cikina nan"
"Da toh ta amsa mata batare da ta musa ba.A haka ta cigaba da rainan cikinta , dayake bata da kiba kuma kullum cikin hijab take, cikin be fito ba sosaii indai ba lura kayi ba bazaka gane ba, wajen Zainab kullum take zuwa tare suke komai har kayan jarirai take siya tana aje mata, har awo take kaita a boye ba wanda ya sani. Abdulrauf kuwa tuni ya cale ya barta nan, tun tana tsumayinsa har ta gaji.
August 1997
Tana kwance tana bacci kamar a mafarki taji nakuda ta kamata tin tana dauriya har ta kira Inna, Inna tazo tana salati ba yarda ta iya haka ta karbi haihuwar tana zagin Zanira, haka har ta sulobo diyar ta mace kyalyawa me kamada ita sak kamar an tsaga.
Da sassafe Zanirah tasa aka kirawo Zainab, tazo aka shirya diyar bayan Inna ta mata wanka tana yi ta dungure mata kai jaririyar Allah , Bayan ta gama wanka ta mik'awa Zanira, kallanta ta shiga yi kawai sai ta fashe da kuka, tana hango mata rayuwa anan gaba, tana hango mata kalubale dayawa dasuke gabanta, inama, inama , inama bata wannan hanyar ta haifeta ba, me zata ce mata duk sanda ta tambayeta ina mahaifinta? da wani idan zata kalleta, ta fada mata sakarci da makahon so ne ya kai har aka samota, tasani tayi kuskure babba kuma kullum rokin Allah take gafara, amma ta kudurce cewa bazata taba yafewa Abdulrauf ba, domin shine yayi mata kantanga da duk wani farinciki na rayuwarta, Inna ce ta katseta bayan data karaso wajenta tana nuna jaririyar
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...