30

360 33 3
                                    

Tun safe suke shirye shirye, Mummy da Aunt Jiddo ba zama, Ya Imra ce da kanta ta kawo me makeup, da kayan da zata saka domin event dinsu ne komai su zasuyi, Amarya tayi kyau fatarta luwai kamar ta yar baby.
K'arfe uku daidaii motar Ya Imra tayi parking a kofar gidansu Zahirah, a gurguje ta shiga tare da me makeup da kayan da Zahirah zata saka, gaisawa sukayi sannan ta wuce dan itama me makup dinsu tana jiranta, take me makeup ta zage ta fito da Zahirah dass kamar ba ita ba. Itama Ayrah ma dasu Ruks
Karfe shida na yamma motar daukan yan dinner ta k'araso, basu dauki lokaci ba suka fito aka tafi wajen dinner a motar tsakayi wanda su Zahirah ke cike tun bayan data shiga ya kura mata ido kamar ze cinyeta, dagowata tayi tana dan tabe baki
"Ni se kallona ake tun ana ganin kyauna kar a hango muni na"
Murmushi yayi har a lokacin yana kallanta
"Ai sai dai ma na kara ganin kyan badai muni ba" dariya sukayi gaba daya
Wajen dinner yayi dan an kayata wajen ba kadan ba, wajen ya tara duk wasu matan manyan hamshakan masu kudi dan Mummy akwai mutane gata da san hulda da masu kudi. anci ansha an cashe kamar ba gobe.

Washegari da safe aka daura aure MUHAMMAD AYAAN ABDUL TAFIDA DA ZAHIRAH ABDULRAUF akan sadaki naira dubu hamsin, waje ne daya tara manya mutane akayi reception aka gama lfy.
Tunda bayan daura aure Zahirah tayi tsuru jikinta duk yayi sanyi, ganin dai da gaske yanzu ta zama matar aure daki ta shige ita kadai tanata kuka, wayarta tayi ringing taga Ayaan, kin dauka tayi har ta katse se daya saka kira sannan ta dauka ta kara a kunnenta ba tare da tace komi ba
"Mrs. Ayaan Tafida.. yanzu kin zama tawa har abada  in sha Allah "
D'an murmushi kawai tayi ba tare da tace uffan ba
"Kinyi shiru matata lfy dai koh.."
"Lafiya lau mijina," tayi saurin katse wayar cike da kunya.

Da yamma yan daukan amarya suka zo, nan fa Zahirah ta hau kuka kamar ba gobe, Ummu da Ummi harda Inna suka jawota daki, Ummu ta fara

"Zahirah yanzu nauyi ya hau kanki ba kamar da ba, yanzu ke matar aurece zakije ibada gidan mujinki, nasan iya tarbiyar dana baki inada confidence akanki, yanzu ne zakuyi zama na gaskiya da gaskiya, karki dauka wai yadda kuke da kafin aurenku haka zaki tada idan kinje gidan mijinki, a'a ki dauki kinje ibada ne, ki kula da mijinki duk wani hakkinsa ki bashi, yanuwansa da mahaifiyarsa ki jasu a jiki, shima zeji dadi, duk abinda kika lura bayaso to ki guji wannan abu, sannan zaman tare zo mu zauna zumu saba ne, idan kun samu sabani shi, kinga ya hau yayi fushi sosaii, danne zuciyarki ke ki sauko, kar dan kinga shima yayi fushi kice kema zaki biye kuyi ta yi, aa da ciwo amma haka zaki daure,  watarana sai labari, babu ruwanki da bin gurguwar shawarar kawaye duk da nasan ke ba me takarcen kawaye bace, sirrin mijinki dana gidanki bance koni ki fadawa ba, idan ba yakai makura ba ba yarda zakiyi yi, tsafta da gyran gida duk da nasan ke badaga nan ba amma ki kara akan nada, Allah ya baku zaman lafiya ya kore duk wata fitina, Allah ya jiqan mahaifiyarki... ta karashe maganar tana kuka"
Kan Zahirah a rufe haka ta dinga zubda hawaye ta rike Ummu gam dkyra aka banbarota aka sata a mota tana kuka babu kaukautawa

Bayan an kaita kowa ya tafi an gama adduoi ya rage daga ita se angon nata Ayaan, k'arasowa yayi inda take zaune tana ta kuka ya daga mayafinta yaga  dai bilhaqi kukan take, runtse ido yayi sannan yace
"Wai har yanzu kuka kike Baby Boo? kodai kin dena so nane?"
Girgiza kai tayi kawai ba tare da tace komai ba
"Toh indai har kina sona please ki dena kuka, yau ne fa rannar farincikin muce be kamata ki bata shi da kuka ba, smile kinji baby boo"
Bata san sanda murmushi me sauti ya subce mata ba, rikota yayi yana bubuga bayanta alamun rarrashi
"Karki damu zan rikeki amana as promised baby boo, nima ki rike ni amana Allah ya sanya albarka a rayuwar aurenmu"
"Ameen " ta fada cikin sheshekar kuka
"Yanzu ki tashi kiyi alwala muyi sallah, sai mu dan ci  kazar nan i know kina jin yunwa" ya fada yana gyrawa ledojin zama.
Share hawayenta tayi ta miqe ta shiga bandaki ta dauro alwala ta tadda shi a gefe yana jiranta, tana fitowa ya tada salla suka tada.

********
Wani makeken fili ne cike da namomin daji masu a hadari, garin bakikirin sai walkiya dake haskakashi jefi jefi. Gudu yakeyi duk da raunin da ke gabadaya gabobin jikinsa, wanda hakan yasa farin kayan dake jikinsa ya sauya launi daga fari  zuwa ja saboda jinin dake fita daga dukkanin gabobinsa,  gudu yake yi kamar ransa ze fita, ya duba gabas ya duba yamma kudu da arewa babu ko alamun wani waje daze kebe ya gujewa fusatatun namin dawan nan, daga kansa keda wuya ya hango wani farin haske wanda ke fita daga wani makeken gate da'aka bude, wata ajiyar zuciya ya saki tare da bude baki yana hamdala, da gudun gaske ya karasa  gate din sai dai wani haske dayagani da gudu yazo ya rufe gate din, karasawa yayi yana kuka , duba da yadda murguza murguza  fusatatun zakuna ke karatoshi, bubugawa ya cigaba dayi yana ihu amma shiru, can gate din yadan motsa alamun ana shirin budewa,
A hankali ta karaso cikin shigarta ta farar abaya da farin mayafi, cike da murmushi tana kallanshi, dagowar da zeyi suka hada ido ya zaro jayayen idanuwansa da suka gaji da kuka yana kallanta, murmushi kawai tayi ta koma ciki ta rufe gate din take hasken ya gushe, kuka sosaii yayi cikin azaba yace
"ZANIRAHHHHHHH"

Kuyi hakuri na jina kwana biyu shiru da kukayi wallahi nayi rashin lafiya ne amma yanzu kam Alhamdulilah kuyi hakuri da wannan zan sake wani update din soon nagode🙏🏻🥰

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now