A firgice ya tashi daga mumunan mafarkin dayayi, har a lokacin yana ambatar sunan Zanira, da sauri ta karaso tana kallanshi ganin gumin dake keto mishi dukda sanyayan AC dake dakin
"Mine.. meya faru? Wacece kuma Zanirah?"
"Babu komai kawo min ruwa na sha" ya fada yana sauke ajiyar zuciya
"Babu ruwan da zan kawo maka, sai ka fada min wacecec Zanira da har kake mafarki da ita?" ta fada cike da masifa
"Ke bakida hankali ne wai, ki kawo min ruwa nace"
"Aifa sai kayi wallahi ba ruwan da zan kawo ma, tsabar rainin hankali, gani matarka ka dinga mafarki da wata...." ta fashe da kuka
Da sauri ya karaso murya kasa kasa
"Kukan me kike haka?" Wai ke har yanzu wannan azababen kishi naki na nan?"
"Babu abinda zaka cemin azalumi, ka fada min wacece Zanira" ta fada tana cakumo rigarsa
Wani wawan tsaki ya sakar mata, ya janye bargonsa yayi sauri fita daga dakin, dayan dakin ya shiga ya saka key ya barta nan a kofa tana masifa har ta gaji ta hakura.Tun safe daya tashi ya fito bece mata uffan ba, ita kuma sai balbaleshi da masifa take akan lallai sai ya fada mata wacece yake mafarki da ita, da sauri yaransu uku suka fito daga dinning bayan mai aiki ta gama shirya su sunci abinci, da gudu suka karaso suka rungumeshi
"Good morning Dad"
Janye su yayi kawai ya koma gefe yana hado brief case dinsa, ya fice da sauri ya barta nan ta saki baki tana kallansa.
A office dayaje gabadaya bashida sukuni, tunanin mafarkine kawai yake dawo masa.A gigice ta koma cikin daki ta lalubo wayarta, dailing number tayi ta kara a kunnenta cike da zaquwar dauka,
"Hello, duk abinda kake ka baro kzo gidana akwai matsala babba" tayi sauri katse wayarMintuna kadan ne suka kawoshi, da sauri ta k'arasa tana dubansa
"Femi, asirinmu na gab da tunowa akwai matsala fa"
"Matsalata dake saurin birkicewa zauna muyi magana" ya karasa yana zaunar da ita a kujera
Duk abinda ya faru ta zayyane nasa, daria sosaii yayi wanda har ya fara bata haushi sannan yace
"Masturat kenan, duk abin nan da mukayi ba dan kudi mukayi ba? Kince rabin kaddarorinsa duk da signing dinki a jiki, to ai banga matsalar ba"
"Ga matsala kuwa yaranan sune matsala, femi gabadaya salary dunka bekai 100k ba, bazaka iya daukan nauyinsu ba, ko schoolfees dinsu ya fi salary dinka, gashi duk holidays kasan sun saba ba a nigeria suke yinsa ba, dole kon dan su mu rufe asirin nan"
"Lallai masturat kin raina ni, to amma kinsan da cewa yaya nane kuma babu yadda zaki yi idan na karbesu?"
Dariya ta bushe dashii
"Kaban dariya femi, me zaka iya yi? Babu abinda zaka iya, komai dakake takama dashi nice sila, idan na kwace shikenan ka dawo femi villager dinka na asali, yara kuwa ko zaka kwana kana rantsuwa babu wanda ze yada cewa naka ne, its better kabi duk abinda nace kagane koh?"
"Bangane ba tukuna Masturat nidai yanzu kiban 'yayana kawai can ku k'arata keda mijin naki"Adaidai wannan gabar Kansa ne ya ji gabadaya yana juya masa, kafafuwansa sun kasa daukarsa silalewa kasa yayi ya kasa murda kofar da yafi awa a tsaye, yana saurensu tun bayan dawowa dayayi daga office saboda gabadaya be gane komai, tashi yayi dakyar ya tura kofar ya shiga, gabadaya suka dago suna kallansa mussmaan femi dayafi tsurewa, hannunsa ya daga yana nunata
"Masturat, sakayyar da zaki min kena...." sai kuma ya sulale ya fadi
Da sauri sukayo kansa da taimakon driver suka sashi a mota zuwa asibiti, bayan likata ya dubashi, tana zaune a gefensa idanuwansa a rufe yana hawaye, matso da kujerar tayi kusa dashi sannan ta juya ido ta fara bayani"Abdul'rauf Mu'az nasan da cewa kanaji na, kuma yanzu haka zuciyarka na fada ma abubuwa daban daban, nasan cewa zakayi banma hallaci ba, bayan dauko ni daka yi ina tallar alala, ka rufa min asiri na tashi daga 'yar yarabawa zuwa Masturat Mrs Abdulrauf, bayan ka kaini makaranta har daga baya ka aureni, kana tunanin da duk zaman danake da kai tsakani da Allah ne? Ta fashe da daria tana gyda kai, tunda ka shigo rayuwata nida mahaifiyata mukaje wajen boka akanka, wanda ya tabbatr mana da cewa kanada kyakyawan future a gaba, kuma zaka zama wani hamshakin me kudi, be tsaya anan ba ya tabbatar mana da cewa zakayi yunkurin kara aure nan gaba bayan ka aureni idan har banyi wani abun ba toh dole zaka kara, nan nida mahaifiyata muka rude saboda tsananin kishina dakuma san kudi irin na mahaifiyata, bayan munyi aure nidakai, shekara daya shiru ban samu haihuwa nayi maka maganar sai dai naga baka dauka da muhinmaci ba, hakan yasa nida mahaifiyata muka koma wajen bokan nan anan ne ya tabbatar mana da cewa bazakataba haihuwa har karshen rayuwarka idan kuma mun musa muje ayi gwaji a boye, sannan zakayi yunkurin k'ara aure, nan muka bada kudi akai aiki aka hanaka, bayan nan idan bazaka manta ba , haka na daukeka aka gwada mu sai dai mun hada baki da likitan cewa idan har haka ya gani karda ya fada maka, be fada maka ba kuwa ya fada min a sirrance, tun dana dawo jikina yayi sanyi dan nasan 'yayan ne zasu temaka min sosai wajen mamayar dukiyarka, take tshohon saurayina Femi wanda saboda addininsa yasa bamuyi aure ba ya fado min, nasan cewa yana mugun san kudi, was kuma baze taba kin yarda da abinda zan kawo masa ba, dan haka nanemoshi na fada masa komai ya yarda a haka muke kasancewa dashi kai kuma na kawo maka shi a mtsayin cousin dina wanda ya tashi a gidanmu,amma a zahiri muna boyewa muna cigaba da soyayyarmu, a haka muka sami wadanan yaya guda uku Muaz junior, Aesh, da Baby Safrah idan kama ganin baka yarda ba zamu iya zuwa ayi DNA teat anan ne zaka tabbatar, kodan rashin kamar da sukeyi dakai yaci ace hakan be baka mamaki ba, yanzu nasan zakace zaka rabu dani amma kasani idan ka rabu dani ka rabu da rabin dukiyarka wanda dasu kake takama sannan ka rabu da yayan da ka riga ka saba dasu a matsayin yayanka na cikinki, kuma ka rabu da tsaleliyar mata kamata, idan kuma kace zaka zauna dani ne mu rufawa juna asiri kaga yafi maka rufin asiri, ina jirin zabinka saboda bansan bata lokaci Hon. Abdulrauf muazz"" ta karasa tana fashewa da wata muguwar dariya
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...