32

544 33 7
                                    

A wannan gabar gabadaya kwakwalwarsa ta shiga juya masa, ya kasa tantace abinda yaji, gaske ne ko kuwa duk a mafarki ne? da karfi ya bude idanuwansa yayin da itakuma tayi masa wata shu'umar dariya, dakyar muryarsa ke fita amma duk da haka ya firta
"Kinci amanata Masturat, duk hallacin da na miki abinda zaki saka min dashi kenan?"
"Hahahaha ni dakace cin amana sai ka tuna min da yarinyar da kayiwa ciki a lokacin kana bautar kasa ka tafi ka barta ta haife yar har ta girma aka kawo ta ka musanta? ko duk a tunaninka bansan da wannan labarin ba?" Ta fada tana k'afeshi da ido
A firgice ya dago ya kalleta cike da mamakin inda tasan wannan duk kuwa hanyoyin daya bi wajen boye mata
"Amma ai duk dan ke nayi hakan Masturat"
"Karya kake yi, tun kafin ka hadu dani ka aikata abinka, kuma ni a tunanina abinda na maka ko kwatankwacin wannan beyi ba, dan haka ka girbi abinda ka shuka ne"
Kuka ne subce masa ganin yadda gabadaya rayuwa ta juya masa a rana daya, koda mugun mafarkin dayayi aka barshi ya isheshi, balle kuma jin cin amanar da matarsa wadda ya dau san duniya ya dorawa tayi masa, tuno yadda yakeji da yaran nan nasu, dan gani yake su suka rage masa makusanta sosaii a wajensa saboda, ana shagalin bikinsu bayan sun koma iyayensa da duk makusantansa sukayi hatsrin mota suka mutu, ya rage bashida wani dan uwa na jini sai Babale wanda shima Masturat sai data rabusu tukuna, kuka da bakin ciki ashe rainin yayan wani katan arnen banza yayi? Tabbas. Rayuwa ta juya masa baya

"Ka tsaya kana kuka kamar wani k'aramin yaro, nifa kana bata min lokaci" Masturat ta katse kukan nashi
"Kije na sakeki saki uku kuma Allah ya isa ban yafe miki ba"
Tashi tayi taci damara tana rawa
"Haka nakeso, yanzu ne zanyi rayuwa me yanci ga kudi, kai kuwa bakin ciki ne nasan ze kashe ka a asibitin nan, idan ka mutu ka yafe min kaji sai anjima"
Taja Femi sukayi gaba.

****
Washegari da safe Zahirah tasha shan albarka wajen Ayaan, bayan sun yi wanka sun kimtsa Zahirah ta fito cikin shigarta ta atamfa riga da skirt dinkin ya zauna a jikinta dass, light makeup tayi tare da bazo gashinta ta daura dankwali akai, tana fitowa Ayaan ya kura mata ido yana yaban irin kyan data zuba, kwankwasa kofa akayi, Ayaan yayi saurin budewa Mai aikin Ya. Imra ce ta shigo rike da warmers da teaflask a hannunta, Zahirah tayi saurin karba ta jera a dinning sannan ta wuce bayan sun bata sakon godiya da zata kaima Ya Imra.
Kitchen ta shiga wanda yasha uban kaya masha Allah, ta dauko cups da spoons da kuma flates ta dauraye sannan ta aje ta fara bude warmers din, na farko chips ne sai farfesun rago, sai plantain da egg sauce, zuba musu tayi ta hada musu tea din suna sha
"Ashe dai da rabon zamu ga rannar nan Baby boo?"
"Gata kuwa sai dai muce Alhamdulilah"
Bayan sun gama ci , sun dan yi baki wanda basu zo kai amarya ba, bayan ya dawo da masaalin yace ta shirya suje sungaida su Mummy dasu Ummu
"Okay love bari na canza kayan nan"
"Tohm muje mu canza"
"Kai da wa?" Ta fada tana hararasa
"Dake mana muje na canza miki"
Dariya tayi kawai ta shige daki aikuwa ya biyo ta, kayan ya shiga dubawa ya hango wata doguwar riga ta material
"Wannan zamu saka tafi kyau"
Toh shikenan"
Bayan ta saka ta ya dauko dankwali
"Bari na daura miki"
"Toh a daura"
Zama yayi ya daura mata.
Suna tafe yana tsokanarta har suka isa gidan nasu, Mummy na palour tana salamar wata yaruwarsu zata koma gidansu, har Kasa Zahirah, ta tsuguna ta gaisheta ta amsa cike da murmushi nasiha ta dan musu sannan suka wuce gidan Ya Imra nan ma sun dan jima suna hira sannan sukayi salama suka fito, wayar Zahirah ce tayi kara tana shirin bude mota ta shiga ganin Ummu ce ya sata washe baki
"Ummu gamu nan zamu zo yanzu i cant waittt to see you" ta fafa cike da murna
"Zaku zo ina? Ke Zahirah jiya akai ki kizo kinin me? Kina zauna a gidanki bansan yarinta"
"Haba Ummu bakya san gani na ne?" Ta fada cike da shagwaba
"Eh banaso kiyi zamanki nan da 1month kyazo daga aure jiya to kika bari Adda Taji ma ai fadan da zata miki se yafi haka, bansan shashanci kiyi zaman ki a gidanki Allah ya miki albarka" kitt ta kashe wayar
Juyo tayi suka hada ido da Ayaan sai kawai ta share yar kwalarta suka wuce gidansu.
Sati me zuwa suka wuce umrabdaga nan suka wuce honeymoon dinsu Turkey sati biyu sukayi suka dawo.

Zama suke me cike da so da kauna da kuma mutunta juna, yauma suna zaune a palour bayan Ayaan yabdawo daga office suna kallan videos din bikinsu, na kamu suka saka, a daidai wajen data kwanto kafardar Ya Mubarak Ayaan ya saka pause ya dago yana kallanta
"Miye haka?"
"Me fa?" Ta fada cikin rashin damuwa
Murya a hasala yace "Au tambayara kike? Shi mubarak din muharaminki ne da zaki dinga kwanciya a kafadarsa? Kina matar aure ke yanzu hakan yayi miki kyau kenan?"
Da mamaki take kallansa ganin yadda ya birkice a dan abinda take gani ba komai dan ita tama manta gabadaya
"To miye a ciki Love, ko ba muharamina bane ai kamar yaya yake a wajena, kuma naga rannar kamu ne ai lokacin baa daura aure ba, so banga abinda tada jijiyar wuya anan ba"
Tashi yayi ya kashe tv din hade da daka tsaki sannan fuuu ya bar palour zuwa dakinsa a hasale
Sakaka ta tsaya tana kallansa, ganin yadda akan abu kankani duk ya tada jiniyar wuyarsa hada tsaki? Tunda suke watani kenan da aurensu amma bata taba fuskanta haka ba, tashi tayi ta koma dakinta a tunaninta zezo amma shiru haka tayi addua ta kwanta.

Tun safe data tashi ta duba wayam babu alamunsa, tashi tayi ta duba dakinsa shima wayam, labule ta daga ta hango babu motarsa wanda ya tabbatar mata da cewa fita yayi ba tare da yayi breakfast ba balle ya mata salama, kanta ne ya shiga juya mata ta koma ta gyra gidan sannan ta dauko wayarta da zumar kiransa sai dai har sau biyu kenan tana kiransa beko dauka ba.

"Not edited!!

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now