24

475 33 0
                                    

DANZABUWA, BICHI LG 1996

Yau ta kasance Laraba wadda hausawa kewa kirari da tabawa rannar rannar samu.
A cikin tashar garin, daga can kudu, a gefe wata yar rumfa ce ta saida abinci, malakin wata datijuwar mata  wadda ake kira da A'ilo, yau ma zaune take akan kujerar mata, ta buga daurin ture kaga tsiya, fuskar nan tasha kwaliyya irin ta kauye, kana ganinta kaga tsohuwar karuwa, zaune tana juya abinci a wata coler, gefenta mai kid'an gurmi ne yanata bugawa

"A'ilo duniya, sun buga dake sun bar miki, A'ilo mai abincin yan gayu duk abincin dabana a'ilo ba wannan ba sunansa abunci ba"
Cikeda alhafari take dan murmushi tana k'ada kai, daga gefenta kuwa,  wata yar budurwa ce wadda bazata wuce shekaru sha shida ba, kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewa jini d'aya na yawo a gangar jikunsu, duk da ba sosaii suke kama ba, amma kana ganinta ka san 'yarta ce ta cikinta , zaune da kayan uniform tana karantun littafi, juyowa tayi cikin tsawa wanda har ya sa mai gurmin dakatawa, tace

"Ke Zanira me kike yi anan? Wa kike tunanin ze salamin kusomas(customers) din nawa?"

Tashi tayi da sauri tana rufe littafin
"Inna yi hakuri, jarabawa zamuyi anjima
shine nake karatu"

"Wai bana hanaki zuwa makarantar ba? miqo min littafin nan yanzu zan qoneshi kowa ya huta"

Zabura tayi tana ja da baya, da karfi ta janyota tana kokarin kwace littafin

"Yi hakuri hajiya, me yayi zafi haka?!"

Wani matashi sanye da khaki kayan bautar kasa(NYSC) ya fada cikin muryarsa ta kamala, gabadaya suka dago suka kalleshi, galala Zanira ta tsaya tana kallanshi, fari ne amma ba sosaii ba kyakyawa na ajin k'arshen kana ganinsa kaga asalin bafulatani, duk da shi ba siriri bane sosaii

A'ilo ta saki baki sannan tace
"Kai kuma fa, ina ruwanka?"

"Dan Allah hajiya ki taimaka kar ki kwace mata littafinta ki barta tayi karatunta"

"To ubanwa ze zubawa kusomas(customers) din nawa abinci?" Ta k'arashe maganar tana gala masa harara

Hannunsa yasa ya nuna kansa
"Ni zan zuba"

Zanira dake gefe ta dan yi murmushi,
"To muje dan shishigi" Inna ta fada tana yatsine fuska

Nuna masa yadda zai zuba Zaniran tayi , sannan ta koma gefe tana duba littafin, duk da hankalinta  baya kan littafin yana kan matashin , a haka ya dinga zubawa customers din abinci ita kuma A'ilo kawai kallansa take, jira take yayi wani kuskuren ta balbeshi da masifa, dan dama a wuyanta yake, sanin yau ne rana ta farko da suka taba haduwa yasa ta raga masa.

Sai daya gama tsaf ya zamana duk customers din yayi serving dinsu, sannan ya duba agogon dake mak'-ale a hannunsa
"Time yayi, kiyi karatun ki Allah ya bada sa'ar exams se na dawo wataran"
Be jira amsarta ba ya fice ya barta galala tana kallansa
"To mahaukaciya daga ganinsa se ki hau kallansa?ai kin gama karatun, tashi kije ki wanke kwanunkan muzo mu tafi gida
"To Inna" ta fada da dan murmushi sannan ta koma ta fara wanke wanken

Bayan ta gama wanke -wanken, ta maida uniform dinta, rataye da  jakarta zata tafi
"Inna zan tafi"
"Toh jarabibiya  boko, saura ki dade"
"Bata damu ba dan dama tasan amsar da zata samu kenan daga wajenta ta wuce

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now