10

901 61 6
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
    
                _ZAHIRAH_
                        10

*Miss Hafcy*
           &
*Hauwa Damary*

     A haka ta daidaita kanta amma sai tayi shiru tana wasa da yanyatsun ta kamar yana ganinta
    "ya dai? Kinyi shiru" har kasan zuciyarta taji sautin muryanshi ya ratsa take taji ya k'ara shiga zuciyarta
       "ina jinka" ta fada da sanyin murya
    "nasan Ya. Imra ta fada maki komai a kaina kuma naji dadi sosaii da kika amince da buk'ata na kuma gode ina fatan soyayyarmu zata zamo abin kwatace ga kowa"
    "i hope so" ta katseshi
      "olryt then yanzu ina busy ne meeting  zamu shiga i will call you in mun fito take care bye"
      Tsayawa tayi ta kurawa wayar ido abin kamar a mafarki haka take jinsa da murna ta aje wayar tayi tsale a tsakiyar daki tsabar farin ciki,kwata kwata tama manta da zancen Ya Mubark,  sa datai tsallenta iya yinta sanna ta dauko dairy dinta ta hau rubuta abinda ya faru kamar yadda ta saba a kullum.

                      *****
       Dakin yayi shiru sai sautin fan dake wulwulawa a hankali,  Mubarak ne zaune a dakin mahaifiyarsa ya tsura mata ido tun shigowarsa bayan sun gaisa da alama akwai magana a bakinsa amma yana shakkar fada
     "Mubarak kayi shiru kana kallano me zaka fada min ne wai? " mama ta fada tana kure shi da kallo
   "ammm.. Dama"
   "dama me? "
   "maganar d mukayi da dadewa ce ta taso Mama kinga na samu aiki har na kamala ginin gidana to munyi magana da Ummu har ita kanta Zahirah duk da banji ansa daga gareta ba har yanzu na sanar mata,  banda matsala da baba yanzu ta bakinki nakesan ji mamana" ya karashe maganar da adduar Allah yasa ta amince
      " To Mubarak bazan hanaka auren zabinka tunda har ka nuna kanaso nayi nayi dakai kuma ka kasa hakura to ba abinda zance se Allah ya tabbatar da alheri a cikin lamarin nan"
     "Like seriously? Auuu Mama da gaske kin amince" ya fada yana kallanta duk murna ta sashi birkicewa lokaci daya"
       "Eh Mubarak na amince dari bisa dari tun daga kan abinda ya faru akan dan haj faty nagane cewa tursasawa yara auren wanda ba zabinsu ba matukar basa so hadari ne babba dan haka nidai sai dai na maku fatan alheri"
    "nagode sosaii mamama Allah ya bar min ke"
     Ameen ta fada fuskarta cike da fara'ah.
          Da dare ya shirya ya nufi gidasu Zahirah a kofar gidan ya tsaya,  ya ciro wayarsa yayi dailing numberta sai daya kira kusan sau uku  sai ana ukun ta dauka dan tana kallan wayar na ringing amma ta kasa dauka dan bata da ansar tambayarsa har yanzu Ganin kiran yayi yawa ya Sata dauka ta kara a kunneta.
     "ki fito ina kofar gida ina jiranki" be jira answer ba ya kashe wayar.  Tsayawa tayi tana tunani akan ta fita kota shareshi har ta koma ta zauna se kuma ta tuno fa Ya mubarak dinta ne hakan yasata janyo mayafi ta yafa dayake dogowar rigace a jikinta ta fita ba tare ma da sanin ummu ba.
     Yana bakin kofar motar ta jingina yana jiranta ganin ta fito yasasgi saurin dogowa ya kalleta
    "barka da fitowa Princess.. "
    Kunya ma ya bata ta sunkuyar dakai tace "Ya Mubarak..... "
     "princess temako daya zaki min Zahirah ki cire matsayin da kika bani a da ki samamin sabon gurbi a zuciyarki, gurbi na wani daban wanda baki sani ba ya shigo rayuwarki da kokon bararasa yana san ki bashi so da kauna, ni yanzu bakone a gareki Zahirah, ki sani inasoki tun bansan me so ba har nazo nagane mene so ina sanki zahirah bana tunanin akwai wani wnda yake miki irin san da nake miki"
    "Ya Mubarak pleaseee. ........ " ta fashe da kuka, Ya Mubarak ya zanyi ya zanyi?  Bana jin zan iya canza maka gurbin dana maka a baya indan har na fada ma hakan to tabbas nayi karya, bazan iya ba i cant!  Zuciyata yanzu tana dauke  da soyyayar wani daban wanda bana tunani akwai wani wanda ze iya raba soyayyar nan... ya Mubarak kayi hakuri ka zauna a matsayinka na da ina ganin zefiii..  Ta karasa maganar tana share hawayenta.
     "Princess ya kike so nayi?  Duk da dakon sonki dana dauka shekaru da dama amma amsa dazan samu daga wajenki kenan?  Kinsan shekaru nawa nayi da sanki a zuciyata,  kinsan shekaru nawa nayi ina jira ki kawo wannan lokacin sannan na fada miki abinda ke raina,  kinsan duk gwagwarmayar dana sha akanki kuwa?  Kinsan yanmatan dana watsawa kasa a ido duk saboda ke? Amma abinda zakice kenan?  Waye wannan yazo yamin kutse lokaci daya?  Waye shii!!!? " yana gama fadan haka ya dafe kansa yana kokarin matso kwala.
     "Ya Mubarak bansan me zance ba... Amma wannan lamari ne dayake bukatar nutsuwa mu barwa Allah komi duk da bana tunanin hakan zata faru,  zan koma gida  dare nayi...
   Be amsa mata ba illa gyada mata kai da yayi da kuma alamar dayayi mata nata koma gida dan haka tamai salama ta shige bako damuwa daya a ranta.. Shikam jim din dayayi yayi sauri yayi firgigit kamar ya tuni wani abu sai kuma yayi murmushi ya shige motarsa yaja da sauri.

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now