Suna sauka, taxi suka samu ya kaisu hotel din da zasu sauka bayan sunci abinci sun huta, Asaad ya shigo
"Idan kun shirya muje ko, na kira uber har yazo"
Gaban Zahirah ya fadi amma bata san nunawa, a haka suka kimtsa suka shiga zuwa gidan Hon. Abdulrauf.A bakin gate suka tsaya suna bugawa, mai gadin da hausarsa bata shiga yayi sauri ya karasowa da wani dan littafi a hannunsa
"Senunku, how may i help you?l
"Munzo wajen mai gidan ne" Ummi ta fada
"Okay your names?"
"Kamar yaya? Zainab toh" Ummi ta fada a hasale
Duba littafin yayi
"Gaskeyi babu sunan anan, duk wanda zasuyi visting dinsu yau ga sunansu kuma babu naku a ciki"
"Kamar yaya kenan? Toh wannan urgent ne"
"Babu zancen Urgent, wannan shine kaidar danake bi,"
"Kaga ba wani doka, kadai ganmu, bamuyi kalar maula ba kuma bamuyi kalar wanda zasu cutar dashi ba, ka barmu mu shiga" Ummi ta fada tana harararsa
"Babake kofar yayi
"Sorry madam amma baze yiwu ku shiga ba"
Zahirah tayi saurin dagowa tana kallan Ummi idanta duk ya cuko da kwala
"Ummi pls... mu tafi kawai tunda baze bari mu shiga ba"
"Zahirah kenan, rabu dashi, kai kalleni dakayau daga London nake, so nayi dealing da wanda suka fika ma, ka bude min na wuce in peace bansan hayaniya"
Dariya yayi
"Madam beze yiwu ba aikina ne, so bazaki batamin aiki ba"
Wani tsaki tayi a daidai lokacin da wayarsa tayi k'ara, da sauri ya dauka wayar a handsfree
"Samuel kai dawaye ne? ina hangoku ta CCTV meke faruwa ne?"
Durkusawa yayi da sauri
"Oga wesu ne sunce wai suna san ganinka urgently
"Okay barsu su shigo"
Hararara Ummi ta sake maka masa, ya bude suka shiga Asaad kuwa tunda suka fara dramar yake dariya yazo wucewa yace
"Samuel take it easy! Naga kaman zakayi kuka" Sannan ya wuceSuna shiga mai aiki ta musu iso, a falon baki ta kaisu sannan ta kawo musu ruwa da snacks, tare da cewa ga ogan nan zuwa, sai da sukayi kusan minti 15 sannan suka juyo gyran murya wanda ya tabbatar musu da cewa shine, da sauri ya karaso sanye da jalabiya maroon da farin glass a fuskarshi mutum ne fari, mai saje duk da wani sashen na sajen ya dan fara fari alamun furfura.
Zahirah na dagowa ta ganshi gabanta yayi tsananin faduwa, kanta ya sara hakan yasata riko kan nata ta sunkuyar dakai, Ummu ta tsaya tana kallansa, akwai abubuwa dayawa data gani a tattare dashi dasu kayi kamanceceniya da Zahirah duk da bawai kama suke sosaii ba, karasowa yayi ya zauna, gabadaya suka gaida shi banda Zahirah dake sunkuye da kai ta dafe kan"
"Sannunku sai dai ban gane suwaye ku ba?"
Ummi ce tayi sauri cafewa da cewa
"Eh gaskiya bazaka gane ko mu suwaye ba, amma kila ka gane wannan" ta fada tana nuna Zahirah
Rufe bakin ta yayi daidai da shigowar wata mata, sanye da wani tsadaden lace green, hannunta rike da waya, fara ce sal amma kana gani kasan da karin farin kanti, karasowa tayi kujerarsa ta zauna daf dashi sannan tace
". Mine.. baki mukayi ne?"
"Eh na kuna CcTv ne naga sunata hayaniya da samuel yaki bari su shigo shine nace a shigo dasu"
Dan tabe baki tayi
"Okay sannunku"
"Zahirah dago fuskar ki mana" Ummi ta fada tana kallan Zahirah
Dagowa Zahirah tayi suka hada ido, gabansa yayi tsananin faduwa, gumi ne ya shiga keto masa duk da sanyi Ac dake dakin, Ummi ta cigaba
"Nasan ko baka ganeta ba, ka gane me kama da ita?"
Sai da ya dau tsahon 1mint sannan yace
"Gaskiya ban ganeta ba wacece?"
"Amma dai nasan baka manta da Zanira Hashimu ba ta danzubuwa bichi lg?
"Eh tabbas nayi NYSC dina acan amma ban gane taba"
Gabadayansu suka dago da mamaki suna kallanshi, wani abu ya tsaya ma Zahirah a maqoshi, Ummi ta cigaba
"Kaji tsoron Allah, Zahirah hashimu daka yaudara ka mata ciki? To ga yarka nan itace wadda ta haifa" ta karasa maganar tana nuna Zahirah
Dan murmushi yayi sannan ya kalli matar tasa
"Mine kinjisu fa? Ke Malama dakata akan mene zaki zo har cikin gidana kimin sharrri? Kawai saboda kunga Allah ya daukakani shine kuka zo ta wannan hanyar? To kinga matata nan, 'yayana uku su kadai ne 'yayana ni bansan wata Zanira hashimu ba balle wata yarta, can dai ku nemo mahaifinta" ya karashe maganar yana huci
"Thank God mun fahinci juna da mijina da sai ku sa na zargeshi kunga ku tashi ku fita dan Wlh zan iya sakawa azo a tafu da ku station "
Zahirah ta dago da sauri ta karaso wajensa
"To nima meza ka amfaneni dashi? Me zanyi da azzalumi irin ka? Koda ka amsa kai mahaifina ne bazan taba sanka ba, kaje duniya ce ta ishi kowa riga da wando, fuuuu ta fita daga falon
Ummu ta jiyo
"Kinga Adda Zainab, rabu dashi, kowa yayi nagari kansa"
"Ke banasan wani zancen banza, wallahi shine mahaifinta, kuma wallahi Zahirah yarka ce jininaka ce, idan ka musu anan ai baka isa ka musa a gaban Allah ba, kuma da kake maganar maula, kalleni dakyau nafi karfin kudinka wallahi, baka san wacece ni ba, dan dan majilisa kake takama ba? Wata tsiyar ce a dan majilisa bayan zaben ma magudi kayi?"
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...