22

397 33 12
                                    

Zahirah da Asaad na zaune suna hira jefi jefi Ummu ta shigo, sannu da zuwa suka mata gabadaya sannan ta zauna
"Duk nagaji wallahi" ta fada tana sauke numfashi
"Ummu ina kikaje?"
"Munje kasuwa ne hada kayan lefen Mubarak, inda ma Allah ya temaka mun gama komai lefe yayi kyau masha Allah, yaushe zakije gani kafin akai?"
Cike da mamaki ta kalli Ummu
"To har abin ya matso kenan? Kafin akai lefen zanje na gani"
"To kuwa se ya kasance cikin week din nan saboda  wani week din zaa kai"
"Ohh ashe abu ya matso haka, amma Ya Mubarak ko labari?"
Iro me gadi ne ya katse su bayan ya fara kwankwasa kofar, Asad ya bude yana sauraronsa
"Ya akayi?"
"Ina Zahira wani ne ke salama da ita"
Kan Asad yayi magana tayi caraf ta tashi
"Waye?"
"Wannan wanda yake zuwa wajenki, ya sunansa ne? ni sunan ya kwantamin"
Tasan Ayaan ne cike da murna ta kalli Ummu wadda tayi mata alamun taje
Bata ko duba mirrow ba take kokarin fita Ummu tayi saurin tareta
"Haka zaki fita Zahirah? Je ki dan gyra fuskar mana"
"Bashi Ummu kawai" ta fita da suri

A jikin motarsa ta hangosa ya hade hannuwansa yana jiranta, da dan gudu ta k'arasa wajenshi sai kuma ta tsaya cak bayan ta gasgata shine din, ta fashe da kuka,
"Oooo kukan me kike please? Ba gani ba" ya fada cike da kulawa
"Kawai kukan naganka ne, ban taba tunanin zan sake ganinka ba"
"Sai kuma Allah yayi gani nan gabanki,  shiyasa nake yawan fada miki Zahirah komai nada mafita, kar ki saba da fadin bankwana"
Sunkuyar da kanta tayi
"Inasan in fada maka koni ...."
Hannunsa yasa a saman labbansa
"Shiiiii, nasan komai mu bar maganar nan, aurenki ne ba fashi in sha Allah se nayi Zahirah"
D'an murmushi tayi wanda ya bayyana farararn hakoranta
"Ayaan ina sanka wallahi so ba na wasa ba, karka gujeni please"
"Duk yadda kikeso na yafi san dana ke miki baby Boo, will u marry me?" Hannunsa yasa a kirjinasa saitin zuciyarsa ya cigaba
"Ki bani wannan damar Zahirah, zan killace ki ana tsahon rayuwata"
"Yess Ayaan zan aureka kuma na baka duk wata dama" ta fada da sheshek'a
"Then in sha Allah kafin nan da 3months maganar aurenmu ta kankama, i cant wait anymore,"
Rufe idanunanta tayi alamun kunya tana kokari tafiya ya jawo mayafinta
"Ina zaki je? Hira nazo muyi hira ta soyayya, ki fada min yadda kikayi surviving a yan watanin da bama tare, tell me uhmm ina jinki"
Runtse idanuwanta tayi, siraren hawaye ne ke zirara a hankali ta furta
"Kamar zan mutu haka naji, inda mun rabu, ina kyautata zatan da yanzu sedai a bada lbrna dan na gushe"

Tausayi ta bashi, hakan ya sashi tuno da halin daya shiga shima, hannunsa yasa ya janyo hannunta ya damke a hankali, tana kokarin janyewa ya kalleta
"Kisani Zahirah bazan taba gudunki ba, baza mu rabu in sha Allah mutuwa ce zata rabamu"
Cikin inda inda tace
"Ehh amma ka sakar min hannuna pls "
Janye hannun yayi da sauri
"Am sorry please.. baby boo"
Murmushi tayi tana masa kallo me cike da so da kauna
Sunfi 1hour suna hira, bayan sunyi salama har zata shiga yayi saurin kiran sunanta, hakan ya sata ta juyo tana kallanshi
"I almost forget , zoki karba"
Tsayawa tayi taba kallanshi har ya dauko wani dan karamin gift box ya miqo mata, da murmushi ta tsaya tana kallanshi, miqo matayi
"Bude kiga"
Tana budewa taga kwalin sabuwar waya me tsada gal a ciki, da mamaki ta dago tana kallanshi tana juya kwalin
"Waya?"
"Yes ina fatan ta miki, akwai registered line a ciki, nasata a charge nayi komai ya rage kawai ki kuna i'ill call you idan na koma gida, take care baby boo"

Ya shige mota yaja ya barta galala tana kallansa cike da mamki har yanzu bata dena juya kwalin ba, tana shiga ta tadda Ummu har tayi barci, kasancewar Abban Asad a dakin Ummu yake dan haka batayi garajen shiga bama, ta koma daki ta kuna wayar, text ta hada na godiya me cike da soyayya ta tura masa baa dade ba kuwa ya kira suka sha hirarsu.
*****

Cike da murna da farin ciki Mummy ke kallan Maman Ayra wadda saukarta kenan daga airport
"Sannu Zainab, finally yau kinzo Nigeria" Mummy ta fada cike da murna tana riko hannunta
Murmushin yak'e tayi
"Wallahi kam bayan shekaru masu yawa rabona da Nigeria!"
"Hakane dole kiyi murna muje"
Fuskarta sam ba alamun walwala cike da kulawa mummy ke tambayarta dalili kai kawai ta gyda mata alamun babu komai.

Bayan sun ci abinci ta huta, Mummy ta bijoro mata da matsalarta
"Hmm Amina duk laifinki ne ki gwada jan su a jiki zaki sha mamaki" tana fada tana gyra zaman daurinta
"Wai wani jiki kuma? Ciki zan maidasu ko kuwa me? Nifa mafita zaki nemo min kamar yadda kike nema min a baya"
Dan murmushi Maman Ayrah tayi ta dafa kafadun Mummy
"Nifa Amina yanzu duk na ajiye makamai na nabar komai ga Allah, na tuba Amina , bin malaman nan ba abinda yake ja mana sai zunubi, gwanda na gyra rayuwata " tana fada tana kafe Mummy da ido

"Au da shiyasa tunda kikazo kike cin fuska harda murmushin yak'e? Aikuwa Zainab baki isa ba, ke kika sani a harkar bin malaman nan yanzu kuma se ki zame?" Mummy ta fada cike da masifa

"Nidai Amina tunda ni nasaki yanzu ki fita , baki san wace ni ba tunda na farko, ko zunuban dana aikata a baya baki sani ba, tunda na ce miki mu koma ga Allah ke kisan akwai dalili"
"Dalilin me Zainab?" Ta fada cike da zakuwar san jin dalilin
"Zan fada miki amma ba yanzu ba, nidai yanzu dan Allah kisa driver yakaini gidan kawun Ayrah dan tun kan nazo suke ta kirana na biyo"
"Toh shikenan Idan kika dawo mayi magana"
****
Wayar ta karewa kallo sannan tace
"Kyautar wannan waya me tsada? Kuma kika karba ba ko kunya?"
"Wallahi Ummu shiyasa ni karba, amma banyi niyya ba"
"Toh shikenan Allah ya sanya alheri"
"Yauwa Ummu ina taron world food day dana ce miki Madam ta gayyacemu? Anjima ne fa, saida Zeenat ta sake tuna min dazu da har na manta"

"Hakane kuma gashi Asaad da driver duk basu nan balle su aje ki, ko dan sahu zaki hau?" Ummu ta fada tana dafa Zahirah

Eh" ta fada da sauri, kudi ta miqo mata ta fita cike da zak'uwa zasu hadu da Ayaan, dan tun jiya ta fada masa zezo su hadu, sai da suka gama event din, sannan ta kirashi be dau lokaci ba ya karaso wajen.

Ummin Ayrah na bayan mota tana ta waige waige dan ganin Nigeria tayi ta dawo mata sabuwa, Tana waige waige idanuwanta suka hango mata Zahirah na kokarin shiga mota, bayan Ayaan ya bude mata motar ta shiga, Bata kula da wanda ya bude motar ba, domin hankalinta kacokan nakan Zahirah, a zabure ta dago ta kalleta tuni ta birkice, mamaki da firgici da tsoro duk ya kamata, hannu, baki , jiki na rawa tayi wa driver nuni da motar Ayaan
"Yi sauri kasha gaban motar can dan girman Allah karka bari su wuce mu"
Da sauri yaje yasha gaban motar da Ayaan ke kokarin tada ta su tafi, da mamaki Ayaan din ya tsaya ,sauke glass yayi har ta gefen Zahirah wanda ya kara bata damar kallanta, tabbas itace ta fada da d'an karfi, a hargitse ta fito daga motar, idanuwanta nakan Zahirah dake gaban motar tana kallan Ayaan suna magana da driver, Ummin Ayarah tayi sauri karasowa tana nunata
"ZA...NI..RAHHH!?!!!!!!"

Ignore typing errors pls

Ghen ghen ghen, tofa wata sabuwa😳

meke shirin faruwa ne kuma?🤷🏼‍♀️

Gaskia bakwa fadin ra'ayoyinku, kamar dai bakwaso, idan bakwaso sena dena typing din😫😠🤷🏼‍♀️

Include me in your prayers please, zan fara final exams gobe in sha Allah nagode🙏🏻💕

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now