35

567 35 12
                                    

Shiru yayi ya rasa ta cewa, yasani cewa komai ya faru shine sila kuma ya cancanci fiye da haka, abu daya da idan ya tuno yake jin duk jikinsa ba dadi shine yasan tabbas ta dalilinsa Zahirah take wannan cutar,a hankali ya shige tiolet ya watsa ruwa ko ya dan ji dadin jikinsa.

Da murmushi Nurse ta karaso rike da paper a hannunta tana dosu su Ummi,
"Hajiya Ummi congratulations, Tana dauke da juna biyu na wata uku, gaskiya Haj Ummi na cancani kyauta cuz da cikin Ayrah ma nice na fada miki"
Washe baki Ummi tayi ta janyo Zahirah datayi galala tana sauraron Nurse tace
"Alhamdulilah!!! allah me iko Allah maji rokon bawansa tabbas me hakuri da dogaro da Allah yana tare da naasara, Alhamdulilah ya rabbi, ke kuma Nurse tabbas kin cancanci kyauta send me ur account details Asap nasan kinada no dina"
Da murna tace
"Okay toh Haj Ummi godia nake, ku shiga wajen Dr sauran karin bayanin zata muku".

Tun bayan da suka fito daga asibitin suka shiga mota dan kama hanyar gida, tayi shiru ko uffan bata ce ba, ta rasa gane me zatayi kuka ko kuma murna? Ummi dake lura da ita tun dazu tace
"Nasan abinda ke ranki, ki saki jikinki kar komai ya dameki komi ya wuce shima Ayaan din zan masa magana, yanzu bake kadai bace se kin dinga kula.
Da toh ta amsa sannan ta runtse idonta.

Da salama Ayaan ya turo kofar palorn Ummi, Abban Ayrah ne zaune yana kallan news cike da girmamawa ya gaisheshi, Ummi na shigowa rike da flask din tea ta kawowa Abban Ayrah zesha tea suka hada ido da Ayaan dake sunkunye yana zaro ido
"Ahhh Ayaan sannu da zuwa"
"Yauwa Ummi ina wuni ya jikin Zahirah?" Ya fada da gaggawa danshi abinda yafi damunsa kenan
"Lafiya lau bacci ma take"
"Toh Allah ya kara sauqi"
"Ameen"
"Uhm dama, in sha Allah ai taji sauqin da zamu iya tafiya gida koh Ummi?"
Wani kallo ta watsa mishi, Abban Ayrah yana kokarin daukan flask yace
"Bari inje palourn sama kawai"
"Ok toh ai da ka bari nakai maka flask din"
"No karki damu ba matsala"
Juyowa tayi ta kalli Ayaan
"Nasan kasan kai kanka baka kyauta ba abinda kayi, kawai akan abinda baka da tabbaci akai, sai ka kulaci yarinya?"
"Nasani Ummi amma dan Allah komai ya wuce, Dr din da kanta ta kira tace mistake ne, dan Allah komi ya wuce abani ita mu tafi gida"
'Yar daria Ummi tayi
"Toh shikenan, bari na duba ko ta tashi"
Tashi tayi ta shiga daki ya barshi nan ya jiran fitowarta
A gefen gado ta tadata tana duba wata jarida dake bayanta, da sauri ta karaso
"Yauwwa Ashe kin tashi ga Ayaan can na jiranki maza ki tashi ku tafi"
Da sauri ta zaro ido
"Aa Ummi dan Allah kice masa barci nake ni gaskiya ban shirya tafiya ba"
"Banasan shiririta tashi ki shirya kibi mijinki"
Rau rau tayi da ido
"Ummiii please..."
Jikin Ummin yayi sanyi ganin duk irin san da Zahirah kewa Ayaan yau da kanta tace bazata bishi ba , lallai akwai babban abinda ya faru, gudun ko idan taje can din bata huce ba azo a sake samun matsala yasa ta kyaleta, Ayaan tayi wa bayanin cewa bacci take gobe da kanta zata kawota, jiki a sanyaye ya koma gida.

A sanyaye ya aje keys dinsa a kan kujera, karo na farko da yaji duk gidan ya fita a ransa, dan tamkar kango haka ya zame masa yau, remote ya dauka yana kokarin nemo channels ko ze samu inda ake dan abu da ze kwnatar masa zuciya, hannunsa yakai kan wata channel ta music, a lokacin sun saka wakar surrender ta Natalia tylor

We let the waters rise
We drifted to survive
I needed you to stay
But I let you drift away
My love where are you?
My love where are you?
Whenever you're ready, whenever you're ready
Whenever you're ready, whenever you're ready
Can we, can we surrender?
Can we, can we surrender?
I surrender"
Shiru yayi yana sauraron wakar yana lumshe ido, tana karewa ya kashe ya koma daki alwala yayi, yayi nafila sannan yabi lafiyar gado cike da kewar Zahirah.

Washegari Ummi da safe ta lallaba Zahirah hade da nasiha me ratsa jiki, ta dauko komai tayiwa Ummi godia suka kama hanyar gidan.

A lokacin da sukaje ayaan ya fita, zagewa Zahirah taui duk da jikinta datake ji ba dadi, ta gyra gidan hade da wanke tiolets din sannan ta shiga kitchen favorite dish dinsa tayi masa ta jera a kan dinning sannan itama tayi wanka tayi kwaliya ta zauna tana jiran dawowarsa.

A hankalin ya turo kofar zuciyarsa cike da kunci dan koda wasa beyi expecting zega Zahirah ta dawo ba, yana tura kofar suka hada ido yayi saurin wurga da brief case dinsa yana kallanta,
"Babe.. "
"Yes sannu da zuwa" ta fada cike da murmushi
"Sorry for.."
"Shhhh... muje ka dan watsa ruwa ga abincinka nan akan dinning albishir din da zan maka"
"Oka babe". Ya fada cike da anashuwa. Sanda ta masa albishir tana da ciki kyautar sabuwa mota yayi mata gal me tsada.

Haka rayuwarsa ta cigaba cike da so da kaunar juna, wata kulawa ta mussaman yake mata mussaman daya ga ba ita kadai bace, k'ememe taki yarda ayi scanning, balle tasan ma me zata haifa, Inna da Ummu kullum cikin tsiya suke mata wai yan biyu zata haifa ganin yadda cikin nata yayi tulele duk da ko wata 7 be kai ba.

Suna kwance karfe 12 na dare ta motsa, tabo Ayaan tayi daya shula yana barcinsa hankalin kwance
"Dan tashi kaji love" ta fada tana dan bubugarsa, da sauri ya tashi yana micina ido
"Meya faru babe?"
"Ni... ni wallahi danwake nake san ci, kuma ba wanda na girka ba"
Zaro ido yayi yana kallanta
"Danwake babe? Da tsohon Darren nan, past 12 fa yanzu, ina zamu samu danwake?"
"To kayi min mana"
Daria yayi har yana neman tsintirewa
"Ni kuma?"
"Eh kai kuma ko k'anshinsa bansan ji sedai kawai naga an kawo min, pleasess Love idan ban ci ba bazan iya barci ba"
Wayarsa dake kan bedside ya dauka sannan ya fita zuwa kitchen, browsing yayi na yarda ake danwake ya bi procedures din yayi, wasu burkuta burkutan danwake abin daria , ya soya mai ya dauko yaji ya kawo mata, da murna sosaii har tana neman tsalle ta karba ta fara ci, loma uku kawai tayi ta janye shi daga gabanta alamun ta koshi, haka ya hakura ya maida kitchen sannan ya koma suka kwanta.

Bayan Watani.

Zahirah na zaune kusa da Inna dan tun da cikin ya shiga wata 9 Inna ta dawo wajenta, suna zaune taji bayanta ya kage sai ciwo, wani ihu ta kwala wadda ya firgita Inna ta tashi ganin cewa haihuwar ce tazo dan EDD dinta ma har ya dan gota, daki ta shiga ta dauko akwatin haihuwar da suka shirya sannan ta kira driver yazo ya kaisu asibiti, ba yadda zatayi ta fadawa Ayaan, duk da cewa yasha koya maya yadda zatayi operating waya amma har yanzu ba abinda ta iya ita tsoron wayar ma take.

Sai da suka je asibiti sannan tasaka nurse din ta kira Ayaan dasu Ummi dan dama sun saba tanada no dinsu already, mintuna sha biyu ya kasosu asibiti a gigice hadda Ummu.
Awani shida kenan tana abu daya har yanzu haihuwa bata zo ba, Ayaan duk ya rikice idon nan yayi ja, Mummy ce da ya Imra dayake suma sunzo suke lallabarsa, a gajiye Nurse din ta fito tana  dosu su Ayaan
"Ayaan biyoni Dr nasan ganinka"
Da sauri ya bita a kidime, nan dr ke sanar dashi sedai ayi mata CS dan sunyi iya bakin kokarinsu amma ba lallai ta iya haihuwa da kanta ba, beyi musu ba ya amince dan shi yanzu burinshi shine ta haihu lafiya. Shiga dakin datakeyi yayi, tana kwance duk ta galabaita da sauri ta riko hannunwansa

"Ayaan ka yafemin.... mutuwa zanyi Ayaan ka yafe min please, idan na haihu baby ya rayu kace yadinga min addua kar ka bari yayi maraici kaji, pls kace su Ummu suma su yafe min kaji mutuwa zanyi..." ta karasa maganar tana fashewa da kuka.

🥺🥺🥺💔💔

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now