Cak Baban ya tsaya yana kare mata kallo
"Haka kika ce Safiyya?"
Kasa magana tayi sai sunkuyar da kanta da tayi, jinjina kai yayi
"To shikenan Safiyya, tashi ki shiga Allah ya dafa maki"
Wani irin kallo Mama kewa Baba
"Amma gaskiya be kamata mu kyale yarinyar nan ba, ta koma gidan mijinta shine kawai"
"Ki barta dai, Allah ya kyauta" ya shiga ciki abinsaKomai da komai ta hado na jarirai, ta cigaba da rainan Zahirah cike da so da kuma kulawa, Mama kuwa wani sabo sukai sosaii da Zahirah har wani sain ma ita take rainanta, sau dayawa ma mantawa take ba jikarta bace
Zaune yake a gaban mahaifiyarsa datijuwa fara tana zaune a kan daduma, a gefensa kuwa Asaad ne yana wasa, bayan sun gaisa cike da girmamawa, ya kwashe duk abinda ya faru ya fada mata, carbin dake hannunta tana zikiri ta cigaba da juyawa, ba tare da ta kalleshi ba tace
"Me ya hanaka sakinta? Ai beta cancin kalmar nan ta taje gida sai ka nemeta ba!"
"Ammm Hajiya dama cewa nayi wai adan bata lokaci"
"Wani lokaci take bukata Auwal? Nifa dama kasan cewa sam bana san yarinyar nan kai ka dage sai ka aureta, tunda har tayi maka haka, ka sawake mata kawai"
"Eh hajiya amma...."
"Bansan jin komai. Akwai diyar kawata Zainabu itama kwanaki aurenta ya mutu sai kaje ka sameta ku sassanta"
"Hajiya da kin tsaya....."
"Aje min Asaad anan ni zan cigaba da kula dashi, ka kawo min kayansa duka, zan baka adireshin Zainabun"
Jiki a sabule ya tashi ya fita, a dakinsa dake gidansu ya zauna ya fara tunanin rayuwarsu a baya"
Su biyu ne wajen mahafiyarsu wanda babanshi ya rasu suna qanana hajiya mahaifiyarsu ita ta kula dasu har suka girma anan ne Abban Asaad Auwal ua hadu da Safiyya wadda su yan asalin misau ne dake bauchi, aiki ya kawo babanta Kano, ta kamala sakandire dinta duk anan kano mahaifinta nada hali, su hadu ne ta dalilin wani abokinsa anan har suka saba maganar aure ta shigo, sai dai kuma Auwal besanda cewa Tuni hajiya mahaifiyarsa ta samo masa wadda ze aura ba ansha abu sannan mahaifiyarsa ta amince aka daura aure aka kawo ta nan da zama, bayan sun haifi Asad ne aiki ya komar dashi Bichi, anan ne har ta sami wani cikin ta haifeshi saidai a rannar ya koma ga mahalicinsa. Da wannan tunanin yayita juye juye a haka har bacci me nauyi ya kwasheshi.Can bangaren Safiyya kuwa tana can tana kula da Zahirah har ta isa yaye, tuni kuwa Abban Asaad ya amince da auren Zainabu.
Kwanci tashi har Zahirah ta isa yayye , Mama zaune a falo tareda Safiyya ta kalleta cikeda murmushi tace
"Wai yaushe ne zaa yaye wannan tsohuwar?"
"Aikuwa yau ma Mama tare zaku kwana"
Murmushi maman tayi "to ai shikenan se ta zo mu kwanan"
Sallamar Baba ce ta sa duk suka juyo, da sauri Safiyya ta tashi ta riko yar jakar dake hannunsa
"A'a barshi nagode" ya fada yana murmushi, zama yayi a kusa da Mama bayan ya dan huta ya kalli Maman
"Wannan filin danake ce miki zan siyar nasai gidan gonar nan ta Alhaji Lawan, to filin na saida kinga kudin ma, yayi albarka kam dan ciko kadan zanyi na siya gonar, sai kuma aji da sauran gyra gyre.
Sosaii Mama tayi murmmushi hade da yi masha fatan alheri, kudin ya dauka ya kai dakinsa a cikin drower ya sakasu ya rufe.Safiyya ta manta shaf da batun Zahirah zata kwanan wajen mama yaye dan haka kai tsaye ta wuce dakinta ta kwnata bayan tayiwa su Mama sai da safe, da misalon karfe 2 na dare, su Mama basu yi aune ba ba kuma su san ta yadda akai ba se tsintar maza hudu sukai a kansu kowanne fuska a rufe dauke da zabgegiyar wuka a Hanunsa, iya firgita sun firgita mussam Mama
"Alhaji ina kudin da ka shigo dasu dazu"
A rikice Baba yace be san da wasu kudi ba, juyin diniya sukayi amma yaki fada musu, ganin haka ne yasa suka tunkari Mama tare da saita mata wuqa a wuya a firgice ya dauko kudin ya danka musu, ogan nasu ya juyo hade da kada musu kai, da hanzari suka daba musu wuka wanda ya sasu kwala kara da salati, kamar a mafarki Safiyya taji abin, dankwalinta daya zame ta daura ta fito jin alamun magana da tafiya mutane ya sata firgita ta maida kofar a hankali ta wuce, da hanzari suka bar gidan, a rikice ta fito bata nufi koina ba sai dakin, ganinsh kwance jina jina ba alamun rai, ya sakata faduwa ta suma a wajen.Bata san ya akai ba sai tsintar kanta tayi a asibiti, Kabiru yana kanta idanu sunyi ja har a lokacin kuka yake, bakinta na rawa ta kalleshi
"Kabiru ina su Mama?"
Dafata yayi ya riko hannuwanta
"Sai dai kiyi hakuri Safiyya, sun kashe mana su mama innalalahi waina ilaihi rajun "
Wani kuka ta saki tana jijiga gadan da kyar hajiya babar mama ta lallasheta, ta cigaba da kuka a hankali.
Mutuwar Alhaji Muhd da Hajiya Maimuna ya ratsa mutane matuka mussam yadda aka san cewa kisan gila yan fashi sukai musu, tuni yan sanda suka fara bincike akan case din, mutane da dama nata tururwa zuwa yin gaisuwa, sai dai kansancewar Baba bamai dangi bane bashida kowa inban kanon babansa se sauran yan uwa na nesa, Mama ce ma me yanuwa dan mahaifiyarta ma na raye. Mutuwar ba karamin girgiza Abban Asad tayi ba yayi kuka har ya gaji hatta hajiyarsa seta kuka, a take suka shiryo suka taho misau.A lokacin da suka isa ganin cewa Safiyya na asibiti can suka nufa, tana kwance har a lokacin kuka take sosaii, duk ta fita hayyacinta, A sanda Abban Asaad ya ganta wani tausayinta ya kamashi yana san matarsa so me tsanani, ita kanta hajiyarsa sedata koka, tana kukan nan kallonta kawai yake, yasan a yanzu tana bukatarsa tana bukatar ya rungumeta ya fada mata cewa yana tare da ita kuma dukan me rai mamacine, yana bukarar ta a tare da shi, Hajiyarshi data fahinci haka tace
"Auwal bari Audu ya kaimu can gidan nasu muyi musu gaiswu tunda babar maman tana can"
"Nifa?" Ya fada murya can ciki"
Ka zauna kaida ita bari muje mu dawo"
Kabiru yaje rakasu daga shi se ita a dakin, da hanzari ya karaso kafin ya kai hannu ta dago ta rungumeshi da karfi hade da sake fashewa da kuka
"Banda kowa Abban Asaad, sun kashe min iyayena, na shiga uku innalalahi waina ilaihi rajun"
Kara rungumeta yayi tsan sannan yasa hannu ya goge mata hawayen
"Kina da kowa mana Ummu Assad, gani nan mijinki abin alfarinki, ki sani duk rintsi ina tare dake bame raba mu insha Allah"
Kabiru ne ya shigo rike da Zahirah tana kuka a hannunsa, Gabadaya hankalinsu ya koma kanta, Safiyya ta kalli Abban Asad ta kalli Zahirah kawai se ta fashe da wani kukan.****Not edited 🥺
Am out of words😫😫🤭🤭 tun February kenan rabon danayi updates, abubuwa sunmin yawa dukda labarin yana raina, kuyi hakuri pls 🤦🏼♀️🤦🏼♀️
Masu tambayana ko lafiya nagode kwarai lafiyata lau Alhamdulilah ❤️ sai dai kawai na shiga busy ne, amma yanzu in sha Allahu zanyi kokari naga na kamala kusani a addua please thank you soo much 1 love😍
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...