Gabadaya familyn Tafeeda ne ke cin abincin dare( dinner ) akan dinning hadda Ya Imra dan itama tazo gidan a rannan, Daddy ya kalli Ayaan dake cin abincin a hankali
"Ayaan kaga har ka fara maido da jikinka amma da ka saka kanka a damuwa"
"Kaidai bari wallahi, akan wata banzar yarinya yana so ya halakar da kansa a banza" Mummy ta fada cikin fad'a
"Hmm Mummy kawai dai kiyi shiru tunda yanzu dai ai Alhamdulilah" ya Imra ta fada
"Ke rufe min baki na saka dake? Bansan shishigi fa, yanzu sena saba miki wallahi" Ayaan ya kalli Ya Imra yana mata alamun tayi shiru,
"Amina ya isa haka pls" daddy ya fada a daidai lokacin daya dauki wayarsa dake ringing akan table din
"Wa!alaikumus salam Malam audu kana lafiya?"
"Da gaske? A ina ka samo dukan labarin nan?"
"To ba matsala nagode, kayi min sending account details dinka" ya aje wayar idanunsa akan Ayaan
"Dakazo ka sameni akan kama neman aurenan yarinyar nan nace ka fadamin sunanta da unguwar datake, kayi tunanin bazan bincika ba koh?
"Eh daddy cuz naga baka dauki abin da muhinmaci ba"
"To yanzu nasamo dukkan bayanai akanta, Ayaan me ya kaika neman yarinyar da bata da asali?"
Cike da rashin fahimta yake kallan Daddy
"Daddy kamar yaya?"
"Ta taba fada maka waye mahaifinta? Ko ta taba ma magana akan dangin mahaifinta" Daddy ya fada yana kallan Ayaan
"Tace min Mahaifinta ya rasu tun kafin a haifeta, kuma yanzu tana zaune ne a gidan mijin mamanta"
D'an murmushi Daddy yayi
"Maganar gaskiya Ayaan wadda take kira da mahaifiyarta ba itace ta haifeta ba tsintar ta tayi a kango bayan gidanta a Bichi, kuma mahaifiyarta ce ta yarda ita rannar da aka haifeta tare da aje wasika nacewa bata hanyar aure ta sameta ba shiyasa ta yarda ita, tare da rokon duk wanda ya tsince ta da yayi mata tarbiya ta gari gudun karta fada halin da mahaifiyarta ta shiga har ta same"
Gabadaya suka dago a razane jin kalaman daddy, Mummy ta tashi da sauri
"Kana nufin dama duk akan yar shege kake wannan abun?"
Ayaan ya zama speechless ya rasa ma mezeyi abun ya zo masa a bazata zeyi magana daddy ya katseshi
"Karkaga laifinta dan bata sanar dakai ba, domin ita se kwananan ta sani, gudun kar taje inda zaayi mata gori, yasa maman tata ta yanke shawararar aura mata wani makocinsu, wanda tun tana yarinya yake kula da ita a matsayin yayanta"Fahad ya kalli Azeema suka kunshe daria a tare, Ya Imra kuwa rike hannun Ayaan tayi wanda har rawa yake, Daddy ya cigaba
"Yanzu zabi ya rage gareka indan har kana santa har yanzu, zamuje mu nema maka aurenta duk da ance wanda ze aurenta ya kawo kudi, idan sun bamu falilahil hamid idan muka basu bada ba shikenan"
Buga tabble Mummy tayi
"What???!!!! Dan nawa zaaje nemawa auren yar shege? Wallahi baze yaba yiwuw ba, sai dai ko bayan rai na"
"Kinada labarin rabo yana kisa? Ba mamaki se kiga Allah ya dauki ranki kuma anyi auren ba yarda kika iya"
A hasale ta dago ta kalli Daddy
"Ni kaka cewa haka Abdul Tafida? Ni kake ma fatan mutuwa? Ashe da babban makiyi na nake zaune bansani ba , to wallahi Ayaan baze auri yar shege ba bazamu hada zuria da yar shege ba wallahi""Ki fadamin aya ko hadisi wanda ya hana a aauri yar shege? Fadamin Malama Amina ina jinki??!!
"Kaga ni bansani ba, kuma kasan da cewa inada iko akan d'ana koh? Dan haka a matsayina na mahaifiyarsa wadda tasha wuyar nakudarsa ban yarda ba kuma ba wanda ya isa ya sakani na yarda"
"Sai yau kika san Ayaan danki ne Amina? Kin manta da Bakinki kikace mantawa kike Ayaan da Imra 'yayanki ne?"
Tsaki Mummy tayi cike da fushi fuuu tabar dinning din zuwa dakinta.
Imra ta sunkuyar da kai dan abin ya matukar tsaya mata arai ashe duk kiyayayar da Mummy ke nuna musu yafi haka? Tunda har zata budi baki tace mantawa take su 'yayanta ne"
Ayaan daya kasa magana tun dazu ya kalli Daddy yace
"Daddy tunda dai a musulunci ba, inda akace kar a auri yar shege nikam na amince zan aureta, a neman min aurenn nata"
Sai a lokacin Fahad da azeema suka hada baki sukace
"Gaskia Yaa Ayaan baka kyauta ba, muma bamu yarda ba wallahi"
Daddy cike da tsawa yace
"Ku kuma a suwa? Ku bace min dagani" sum sum suka fita suna gunguni.
Ya imra ta kalli Ayaan tace
"Ayaan, kanajina asa zancen asalin Zahirah a agefe, halayenta nada kyau, tana da tarbiya kayi tunani,"
"Nima a yadda aka fadamin yarinya ce me nutsuwa da hankali, zamuje mu nema ma aurenta insha Allah," Daddy ya fada yayin daya tashi daga kujerar ya nufi sink din dake gefen dinning din dan wanke hannunsa"
Ayaan ya tashi ya nufi dakinsa, Ya Imra batayi gagawar binsa ba duk da tanaso suyi magana, amma kuma tasan yanzu time yake bukata shikadai domin yana bukatar nustuwa, dauka key din motarta tayi ta wuce tabar Samha anan dan ta riga ta fara bacci bata san tashinta gashi dama suna hutu.Tunda Mummy ta shiga daki take sake -sake a ranta, gabadaya ta rasa inda zata saka kanta, mamaki yadda Daddy har yake jefarta da wannan kalaman a gaban yaranta takeyi, lallai tayi sake, wayarta ta lalubo ta shiga neman number Maman Ayrah da sauri ta kira bugu uku ta dauka
"Zainab!!! Akwai babbar matsala, yaushe zaki shigo??"
"Nan da 2days in sha Allah, akwai matsala ne?"
"Akwai babba ma kuwa se kin shigo din" ta katse wayar,
Da dan karfi ake buga kofar tata wadda ta kule bayan ta shige a hasale tace
"Waye kuma?"
"Mummy Nine, Ayaan ne"
"Ayaan? Ka bace min dagani banasan ganinka! Duk akanka mahaifinka ke fada min wannan bakaken maganganun, me kuma zaka cemin?"
Runtse ido yayi a hankali ya firta
"Mummy magana nake san muyi, magana me muhinmaci"
"Magana yar shegen can ce me muhinmanci? Nifa na gama magana Ayaan, ka bace min daga kofar daki kona saba maka wallahi"
Ba'asan ransa ya fita ba yana mamaki hali irin na Mummy.Maman Mubarak zaune tana duba wata magazine Mubarak ya shigo, bayan ya gaisheta tace
"Mubarak, bafa zan zuba ma ido hakan nan ba kana min wayo da hankali, duk sa'aninka sunyi aure harda yaya amma kai kana nan, tunda ka janye maganar auren Zahirah banji ka fido wata da zaka aura ba"
Kansa a sunkuye yafe
"Mama ai kinsan gaggawa aikin shedan, na sami wata amma so nake se mun gama fahimtar juna se nazo da maganarta"
Mumrushi sosaii a fuskar Mama tace
"Wacece kuma?"
"Sunanata Hafsat..."
Hafsat kuma? Yar inace?
"Yar maiduguri ce amma kano suke zaune"
"Masha Allah zanma Babanka magana Allah ya tabbatar da alheri"
"Ameen Mama, bari naje wajen Ummu yanzu zan dawo"
"Toh shikenan ka gaisheta"
Ya tashi ya nufi gidan Ummu cikeda murna jin Mama ta aminta da Hafsat, yana shiga a palour ya tadda Ummu da Zahirah harda Asaad suna kallo, Zahirah na ganinsa da murna ta dago tana kallansa, tasan zuwa yanzu dai ya yiwa Ayaan magana, ta k'agu taji yadda sukayi da Ayaan, tana san tambayarsa amma kuma tana jin kunyar tambaya, runtse idanta tayi tace
"Amm Ya Mubarak..."Mummy ya zaki mana haka? Kodayake Daddy yace rabo ajali kila rabon ne ajalin mummy😨🏃🏿♀️
Ya kuka ga chapter din? Comment pls ku fadi raayoyinku, and dont forget to vote
I love you all fisabillahi🥰
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...