07

956 71 15
                                    

© *MISS HAFCY AND HAWWA DAMARY*

7⃣

Shigarta gida keda wuya tayi kicibis da Asaad a palour duk yan gidan sun zagayesu suna murna da dawowarsa sai a lokacin ta tuna ashe fa yau ne ze dawo, da murnanta ta karaso wajen, daidai kujerar dayake ta tunkura ta zauna a kasan carpert
"Yaa Asaad sannu da zuwa"
Wata muguwar harara ya wirga mata wadda tasata matukar mamaki, shiru tayi tana jiran amsa daga gareshi, yayin da shikuma ya dauke kai yana wasa shida step sister dinsa Suhaima. Murmushin yak'e tayi ta k'ara maimatwa a karo na biyu sai dai wannan karon Ummu ce tai saurin Amsa mata a yayin datake shigowa falon
" Asaad wai bazaka amsa Mata bane? Kanaji tana maka sannu da zuwa? "
"na amsa mata ai, jinai da bakiyi ba amma ita taji"
"wai haka Zahirah? "
"Eh Ummu ya amsa bari na shiga ciki nayi sallah banyi Azahar ba" ta shige cikin dakinta zuciyrta cike da tunanin kala kala.
Shikuwa Asaad har ta shiga yana kallanta cike da tsana, shidai a duk mutanen daya sani be taba jin tsanar bawa kamar yadda yakejin tsanar Zahirah ba, a duk lokacin daya mata rashin mutunci yakan ji tausayinta amma kuma zuciyarshi bazata manta da abinda ya faru dashi ba duk ta sanadiyarta, itace sanadiyar raba shi da maifiyarsa, itace sanadiyar wahala dayasha a wajen kishiyar mahaifiyarsa a baya, itace sanadiyar rashin shakuwar dayayi da mahaifiyarsa.... Itace.. Kai itace taja masa duk abinda ze faru dashi, tayama ze sota? Never! A duk sanda zuciyarsa ta ayyana masa ya dena mata abinda ke mata wata zuciyar kuma se ta hanashi yi haka ta hanyar tunano masa abubuwan da suka faru dashi duk a dalilinta.

Ummu tagane hakaan takan yi kokarin nusar da shi amma ina ya kasa ganewa hakan ne yasa ta kyaleshi ta kuma yi kokarin wajen ganin zahirah ta nesanta dashi hakan yasa sam bashiga harkarsarta take ba wani hutu daya dawo kwanaki yayi wata 1 maganar fatar baki bata taba hadasu ba sai sau daya har ya gama hutunsa ya tafi. Zahirah tana jure komai amma sam ta gaza wajen jure wulakanci dan haka shiyasa ma bata shiga harkarsa.

Bayan ta watsa ruwa tayi sallah tana zaune tana karatun Alkurani taji shigowar sako wayata, d'auka tayi ta duba sako kamar haka
_Manzan Allah Swa yace "in gaya muku wanda ya fi karfi daga cikinku? To shine wanda ya mallaki kansa lokacin fushi kada kiyi fushi princess ki kara hakuri_
_Muhammad M_

Tsurawa wayar ido tayi cike da mamaki, taya akai yasan tana cikin fushi? Bata ba kanta amsa ba domin bata da ita dan haka ta aje a wayar a gefe ta cigaba da karayun kuranin ta.

****************
Yana tashi daga office be zame ko'ina ba sai gida, shigarsa keda wuya yaji ringing din wayarsa, zaro ta yayi a hankali ya dauka cike da girmamawa
"Mummy ina wuni? "
"lafiya lau Ayaan, na kira Imra bata dauka ba dama ina san cemuku ne ku shirya kuzo ku daukemu daga airport anjima kadan tun dazu muna Nigeria mun tsaya a Abuja ne Babanku zeyi meeting, yanzu muka zamu taho Kano"
Bata jira amsarshi bata katse wayar, murmushi yayi
"Mummy kenan"
Kiran Ya. Imra yayi bugu daya ta dauko
"Ya imra su Mummy ashe sunzo Nigeria wai suna Abuja yanzu jirginsu ze taso zuwa Kano muje mu daukesu"
"amma kuma shine se yanzu zasu fada mana ko sun manta ba zaman kaina nake ba? Inada mijina kuma dole sai da izininsa zan fita, in ita Mummy bata kiramu su azeema wai sai su kira mu"
"tace wai ta kiraki baki dauka ba, nima shigiwata gida kenan ta kirani bari na dauko key din square sai nazo na daukeki mu tafi, kar muyi laifi"
"to shikenan bari na kira Daddy Samha na tambayeshi "
kashe wayar yayi ya shiga ya dauko mukulin motar ya fita, horn biyu ya mata ta fito rik'e da Baby Samha suka shiga motar yaja suka tafi.

Slow music ya kunna suna tafiya shiru sukai gabaďayansu kowannesu da abinda yake sak'awa a ransa , shirun da sukai ne yabawa Ya Imra damar tuno da rayuwarsu a baya tun daga kuruciyarsu har zuwa yanzu.

Mahaifinsu Alhaju Abdul Tafida shahararen mai kudi ne wanda ya tara dukiyarsa ta hanyar kasuwanci, abu ne me wuya in ana ambatar sunayen masu kudi dakeji da kudi a Kano harma da Nigeria baa ambaci sunanshi ba, Mutum ne me hidimomi dayawa wanda bashida lokacin kansa dayawa, matarsa Hajiya Amina wadda mahaifinsa ya hadashi aure da ita, wani iri hali da ita me wuyar ganewa tanada girman kai, ga isa ga kuma kyamar talaka ga kuma kishin tsiya, a cikin hallayenta kadan ne zaka dauka ka sashi acikin halaye masu kyau.
.
Bayan aurensu da Alh. Tafida ne ta fahimce cewa ba mazauni bane abune me wuyar gaske yayi wata daya cir a Nigeria batareda ya fita waje harkar kasuwanci saba, Haj Amina nada kishi irin kishin nan da mutane ke kira mahaukacin kishi dan haka yasa ta aje komai take binsa duk inda zashi, shi ba damuwarsa bane domin shiba kule-kule matan banza ke kaishi ba kamar yadda take zato.

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now