MISAU ,BAUCHI STATE 1997Matashiyar mata ce fara kyakyawa zaune tana jera linkakun kaya a cikin wata yar madaidaiciyar akwati, hannu tasa ta share yar kwalar data digo mata, datijuwar matar dake gefenta wadda suke tsantsar kama da ita ta kalleta hade da yin murmushi
"Ke dai Safiyya naga sanda zaki girma, ace duk sanda kika zo gida in zaki koma se da kuka kike tafiya?"
Hawaye ne suka ziraro mata ta kalli Mamantata
"Mama ai dole nayi kuka, nifa banajin dadin kano tunda kuka dawo nan, dan Allah yaushe zaku dawo?"
"Aikuwa dai hakuri zakiyi Safiyya kinsan dawowar mu kano abin da kaman wuya, tunda har babanku yayi retire banga me ze sake dawowa damu Kano ba, kuma naga kema ai kinyi nesa damu, yanzu da Bichi kuke, maza shirya ki tafi bansan kiyi dare a hanya"
"Eh mama amma ai na dan lokaci ne zamu dawo Kano,"
"Koma mene kedai ki nutsu kiyi zaman aurenki"
"To Mama kin hada kayan Asaad?" Ta tambayeta
"Na hada tun tuni, ai nida naso abarmin shi"
"Tab kema dai Mama kamar bakisan halin Abban Asaad ba, ai da kuwa se ya biyo ya daukeshi komai dare, kofa gidansu baya yadda yaje ya kwana"
"Soyayyar da uba kenan" bari na tashi na hada muku tsabarar a leda, ina Kabriu? Yazo ya kaiki tasha" tana tashi ta tafi tana kwalawa Kabiru kira
Cikin yan mintuna ta hada kayan nata tsaf, kabiru ya shigo falon yana dariya
"To ke ki godewa Allah kano kike, ita Adda Zainabu tace me? Ita dake can london"
Kallansa tayi
"To ai nida ita ba daya ba, ka hada yaddda muka shaku da ku da ita? Ita da tun tana shakeara goma ta barmu"
"Hakane kuma, taso muje ni kaiki tasha, ina my boy?"
"Bacci ma yake sai dai ka daukeshi kasa a mota"
Daki ya shiga ya dauko Asad wanda ke bacci yasa a mota, rungume Mama, Safiyya tayi ta fashe da kuka da kyar mama ta banbareta daga jikinta tana dada jadada mata na tabi mijinta ta zauna lafiya a gidan aurenta , wanda ta saba yi mata haka a duk sanda tazo gida, a haka dai shiga mota har a lokaci tana kuka, shikuwa Kabiru dariya sosaii yake yi har suka isa tasha, sai daya tabbatar ta shiga motar sannan ya wuce yana daga mata hannu har mota ta gushe daga idanuwansa.Suna isa Kano, motar Bichi k'aramar hukumar kano ta hau inda gidan aurenta yake , aiki yakai mijin nata can, lokacin hadari ya hado sosai, taxi ta tare tamai kwatacen gidanta wanda yakaita har kofar gida, ganin a kule ya sata mamaki sosaii, dan mukuli tasa ta bude gidan tana shiga ta tadda gidan fes hade da wata yar takada akan kujerar falon dauka tayi ta karanta
"Naje kano ne Ummu Asaad wani meeting ya taso min da gaggawa ba mamaki nayi dare ku kula da kanku sena dawo" dan murmushi tayi ta kwantar da Asaad aakan kujera, sannan ta aje kayan a daki , ta shiga kitchen dan dafa musu abinda zasu sa a cikinsu, sa'ar ta daya ma ta taho da soyayiyar miya daga gida"
A windown kitchen wanda a waje yake kasancewr gida nasu malakin gwanmati ne, dan karamin estate ne wanda baa kantage gidajen ba, tunda ta shiga takejin kukan jariri, gashi a lokacin ruwa ya fara saukowa kadan kadan,bata damu ba sai tayi tunanin ko dan maqota ne, duk da tasan basu makota kusa dasu
Asaad wanda ya tashi daga bacci ya karaso kitchen yana tabata
"Ummu kukan an baby nake ji ni"
"Nima wallahi Asaad sosaii nakeji, kowacce tabar da ana ruwan nan?"
"Ummu muje duba waje, mugani koh?" Asad ya fada da maganarsa ta yara.
Kamar da wasa seta tsinci kanta da bin shawarar dan nta, lema ta dauko a daki ta sungumeshi rike da candle a hannu suka bude kofar a hankali, a gaban gida basu tada komai ba hakan ya sasu zagaywa, nan sukaji kukan na karuwa, a hankli take tafiya rike da candle din tana dudubawa, can ta hango wani kwali, gabata ne yayi mugun faduwa, ta k'arasa wajen,nan ta tabbatar da sautin kukan na fitowa ne daga wannan kwali, dubawa tayi ta hango jariri wanda daga gani sabon haihuwa ne a kwali, suna hada ido dif kukan ya tsaya, da zumudi duk da tana jin tsoro ta aje Asaad hade da miqa masa candle din ya rike, ta dauki kwalin da sauri suka shiga cikin gida"
Cire jaririn daga cikin kwalin daya gama jike wa tayi, sai dai, sai a lokacin ta ga kyayawar jiririya mace sanya da kaya farare da hula, an dorata akan pink din towel, da hanzari ta rumgumeta , hawaye na kwaranya a idanuwanta, ta rik'ota zuwa hannayenta , take jaririyar ta mata murmushi hade da sakin hannunta dake dunkule, wata yar karamar paper ta fado, da sauri ta dauki paper ta duba, a fili ta karanta a abinda ke kunshe a jikin paper d'inZAHIRAH ABDULRA'UF!!!!!!
Dont forget to vote and comment please🙏🏻😚
Ghost readers ina gaisuwa👻🤨#NWA
#ZHR
#Hafss
#love you all❤️
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...