21

396 39 4
                                    

Wayarsa dake aljihunsa da tayi ruri ne ya katseta, dauka yayi, murmushi fal a fuskarsa
"My xoxo" ya fada yana murmushi kamar tana kallansa
Dan far da ido Hafsat tayi
"Bayan tun dazu nake kiranka wayarka batashiga kasani damuwa fa, ina ka shiga?"
"Lfy lau Xoxo, yanzu ina dan wani abu ne i'ill call you back, take care" ya katse wayar da sauri
Zahirah sakin baki tayi tana kallansa cike da mamakin wacece kuma xoxo? Duk da yanzu ba komai tsakaninsu amma se dataji dan kishina ranta, Ummu cike da murmuhi take kallansa tun sanda ya fara wayar
"Kamar fa d'an  nawa yayi sabon kamu banida labari, abani labarin wacece Xoxo?"
"Ummu ai Labari nazo baki, a cikin frnds dina duk wanda muka dan shaku dasu, naga duk ciki xoxo tafi hankali takuma fi dacewa dana aura, lucky me ashe itama tana sona shikenan an wuce wajen"
Ba karamin murna Ummu tayi ba dan ya bayyana karara akan fuskarta, Zahirah kuwa da d'an sauri ta wuce daki zuciyarta na mata wani iri, Salama yayi wa Ummu bayan su dan gaisa dan shi yama manta da Zahiran na daki kwata kwata.
*****
Mummy ce zaune tayi tagumi a d'akinta tana tuno abinda ya faru, gaskiya tayi sake tunda har yanzu Daddy yana iya fada mata kalamai gatsal, amma yanzu kam zatayi using da dabarata a matsayinta na mace ba boka ba malam zata gwada taga ko zatayi nasara, kitchen ta shiga ta hada coffe ta nufi home office dinsa dan tasan yana can
A zaune ta tadda shi a home office dinsa yana duba takadun company ta karaso murna fal a cikinta rike da mug din coffe a hannunta
"'My dear"
Daria sosaii ta bashi ya gumtse daria hade da fadin
"Amina kenan"
Da dan bata rai tayi
"Haba ya zaayi nace ma my dear kacemin Amina gatsal"
"Ok to my wife, ya akai"
"Gaskia abinda kayi min agaban yaran nan banji dadi ba, baka kyauta ba ko kadan, hadda fatan mutuwa fa ka min"
Dan murmushi yayi
"Kece baki kyauta ba my wife, tun farko baki jasu a jiki ba taya kike expecting zasu  miki biyaya besides wannan fa abinda zaki hana sunnar mazan Allah ce, ni kinma tuna min bari na kira Alhaji Lawan naji ko yana gari idan yaso se suje neman auren weekends din nan"
Kamar an buga mata guduma haka taji, tana san magana amma ganin har yayi dailing yasata tsayawa tana kallan ikon Allah, bayan ya gama wayar ya juyo ya kalleta
"To kinji ma ashe tafiya zeyi gobe, se nan da 3months ze dawo amma yana insisting wai aje ko bayanan amma zan jirashi nan da 3months ai kamar yau ne,"
Da murna Mummy tace
"Eh gaskiya abari ya dawo din sannan. Ma kila Ayaan din ya canza raayinsa"
"Amina bazaki taba canzawa ba,"
Dariya tayi ta koma dakinta cike da murna, Ayaan ta tada zaune a kujerar dakin ina jiranta  da sauri ya dago
"Mummy dan Allah ki tsaya muyi magana"
Zama tayi a gefen gado
"Inajinka"
"Mummy me yasa kike haka? Mummy yanzu ashe har mantawa kike ma kece kika haifemu? Mummy pls ki fada min gaskiya kece kika haifemu kuwa?"

Wani irin kallo take aikawa Ayaan, bata san yadda akai ba kawai sai ya bata tausayi, tasani cewa abinda duk take musu sam bata kyautawa amma kuma ai tun farko sune sillar koma me ya faru, yadda Ayaan din ya marairace kamar wani maraya ya taba mata zuciya matuka, hannunta tasa a kan kafadarshi

"Ayaan nice na haifeku, amma tun farko ai ku kuka gujeni, kune  kuka nuna sam bakwa sona dan haka yasa nima na fita a shirginku"

"Me laifinmu Mummy? Mummy kece da laifi koma mene, kishi ya rufemiki ido kin manta da nauyin tarbiya da kula damu da Allah ya dora miki, yanzu ki kalli su Fahad, kwata kwata rayuwarmu da tasu ba iri daya bace, tarbiyar ma daban,"

"Dakata Ayaan "ta fada dan karfi
"Kna nufi kace ni ban iya bada tarbiya ba kenan? To in ba haka ba me kake nufi? Kaga please tashi ka fita karka batan rai"
"Babu inda zani Mummy sai anyi saita komai, ko abinda kike wa Daddy shima be kamta ba karki manta mijinkine fa"
"Kaga Ayaan duk wannan kanayi ne dan na hanaka auren yar shege can koh? To kasani ba gudu ba ja da baya bazan taba yarda ayi auren nan ba"
Dan murmushi yayi
"Duk yadda kikace mummy all i know its inda Allah ya riga ya rubuta matatace dole zan aureta, zaman takewar mu nake san gyarawa, nagaji da wannan rayuwar da mukeyi"
"Me kake so ka gyra Ayaan? Ai duk me faruwa ta riga ta faru, amma tunda ankai ga haka na amince zan gyra na amsa laifina amma fa da sharadi"
Cike da zakuwa yake jiran abinda Mummy zatace
"Ka hakura da auren yarinyar can"
Na hakura mummy indai har wannan ze daidaita komai na hakura"
Murmushi mummy tayi me sauti cike da farin ciki tace
"Allah ya shi maka albarkaa Ayaan" ta rungumeshi tana dariya.
****
Tunda ta shiga daki take ta juya abinda Ya Mubarak ya mata palour, ta tabbata yana sane yayi mata komai, ita rasa dalili duk se takejin ba dadi, yamaso raina mata hankali tana nan tana expecting yaje yayi ma Ayaan magana ashe shi yana can ma ya manta da halin data shiga, duk saboda shi, kallan agogon dake mane a dakinta tayi karfe 3 daidai ta tabbata yanzu Ayaan be tashi daga office ba, dan wani time din  har past 5 ma yana kaiwa, mirrow ta kalla taga fuskanta tayi normal mayafi ta dauka a cikin drower dinta tare da daukar jakarta dake jikin bag hanger dinta,   ta fito palour
"Zahirah ina zuwa ne?" Asad yana fada yana kallanta
"Wallahi Ruks ce ta kirani wai batada lafiya shine zanje dubata, amma yanzu zan dawo ina Ummu?"

"Sun fita da Abba amma bazasu dade ba zasu dawo"

"Ok Ya Asad pls idan ta dawo kace mata na fita
bazan dade ba zan dawo"

"Okay sai kindawo sis"

Da sauri ta fita get tana waige waige ko zata ga dan sahu aikuwa cikin sa'a ta samu kwatacen company su Ayaan tayi masa ta shiga batare da ko sunyi ciniki ba.
Basu dauki lokaci me tsoho ha suka iso miqa masa 1k tayi, cikin  sauri ta shiga company, duba motanci tayi taga ba ta Ayaan amma bata ko damu ba ta shiga cikin company, mutane wajen se gaisheta suke cikin girmama dan dayawa daga cikinsu sun santa, adaidai kofar office din Ayaan ta tsaya tana knocking cike da kaguwa Ayaan din yazo ya bude dan yau idan bata ganshi ba da matsala, tayi knocking har sau biyar shiru, Umar sectary dinsa ne fito fuskarsa cike da murmushi
"Ahhh Madam an wuni lafiya kwana dayawa"
"Lafiya lau, ogan naka baya nan ne?"
"Ahh Madam ai ya dade rabansa da office tun bayan rashin lafiyarsa jefi jefi yake zuwa, amma ki kirashi mana"
"Da zan kirashi ai bazan bata time dina nazo nan har ina tambayar ka ba" ta fada a hasale
"Sorry Madam, yi hakuri idan na bata miki rai"
"Miko min pen da paper"
Da sauri ya miqo mata ta fara rubutu kamar haka

"Can you hear this sound? Do you feel this beat? It is my heart. It is always beating for you. I wish you were with me. I miss you so much. I'm waiting for you roohi. Dan Allah kazo ko sau daya naganka kar zuciyata ta fashe. i love you Ya roohii
Zahirah A.
Ta rufe ta mik'awa Umar dake gefe 
"Ka tabbata ka bashi please kaje ka kai masa nagode"
"Toh shikenan Madam in sha Allah muna tashi zan biya gida na kai masa, ki gaida gida"
Da to ta amsa da sauri ta tari adaidaita ta hau ta koma gida gudun karsu Ummu su dawo bata nan.

Tunda Ayaan ya koma d'akinsa, zama yayi yana tunanin duk yadda sukayi da Mummy dazu,  yaji dadi yadda tace komai ya wuce harma da shi masa albarka, abu daya ne daya daukar mata alkwari baze cika ba shine na rabuwa da Zahirah, yasan kawai ya fada ne amma deep down baze taba iyawa ba, tunani Zahirah ya shiga yi yana tuna soyayyarsu da yadda suke bala'in san juna, tausayi ma Zahirah ke bashi wanda ya kara masa santa, hakika yasani ,rashin sani asali babban gibi ne a rayuwa  mussaman ita data rigada ta san ita ba yar sunnah bace, akwai wani abu boyayye game da lamarin da Allah ya tsara domin shi tun kafin ma ya ganta ido da ido yake ganinta a mafarkinsa, yadda yake ji santa ma har tsoro yake basa, adduarsa be wuce burinsq ya cika na aurenta ba, dan shikadai ne ya rage masa, wayarsa ce ta shiga ruri wanda bussiness line dinsa ne a ciki yaga sunan Umar a jikin screen din, tabe baki yayi dan yasan baze wuce zancen office ba, kuma Umar din yasani sarai yadau hutu na 2weeks, a kasale ya daga wayar
"Umar ya akayi?"
"Gani a kofar gidanku, Madam ta bada sako a kawo maka"
Da sauri ya zubura jin ance Madam yasan Zahirah Umar kecewa Madam, gajeren wando ne da riga armless a jikinsa haka ya fita da sauri , be tsaya sun gaisa da Umar din bama ya karbi paper din ya koma gida, cike da zumudi ya karanta abinda ke cika, rungume paper din yayi yana murmushi me sauti
"I love you more baby Boo" ya firta da k'arfi

Kayansa ya canza zuwa shadda blue yasa hula, key din motarsa dake bedside ya dauka ya fita cike da murna da anashuwa ya nufi gidansu Zahirah.

"Ashe da rai nake sanki jaruma ba da zuciyata ba👯‍♀️👯‍♀️ komai ruwa da iska akanki ba zana dena kewa ba 🎼🎼 jamirin jiran ki nayi dan nazo na kalleki gimbiyar hausa 🎼🎼 sirri na rayuwata kece da kin kira dana amsa💃🏻🎼 tilas ganinmu tilas barinmu🎼🎼 kaunarki tunda nai nisa ,💕 sam ba batun na fasa koda ace zana bada rai fansa... ~ Hamisu breaker

Yau kun gani harda wak'a koh😂💃🏻 naga Ayaan na cikin anushuwa dole na rera waka🌚

Banajin ra'ayoyinku fa 😟 pls ku dinga comments mutane na💕💕

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now