34

384 31 5
                                    

A zubure ya dago ya kalleta
"Kamar yaya doc?"
"Yes a binciken danayi kenan, dont tell me bada amincewarka take sha ba?" Ta fada tana gyra takasun dake gabanta
Bece mata uffan ba yayi mata godiya ya fito.

Zahirah dake zaune a kujerar kofar ta dago tana masa magana beko amsata ba ya wuce wajen daya faka motarsa ba, shiru shiru Zahirah tana jiransa be dawo ba dan a zatanta abu yaje daukowa, side bag dinta data sa a gefenta ta dauko ta makala ta fita zuwa parking space, sai dai babu  shi babu alamunshi, wayarta ta dauko cike da damuwa ta kirashi be dauka ba dagabaya ma katse wayar yayi.

Take idanunta sukai rau alamun kuka, fita tayi ta tsare me napep ya kaita a kofar gidan, tana shiga ta tada motarsa da mamki ta shiga gabanta na faduwa
"Love? Na aza ko mantuwa kayi meya faru dan Allah?" Ta fada tana karasowa dab dashi, bece mata uffan ba illa tashi dayayi ya nufi dakinsa , da sauri ta tashi ta tare masa hanya
"Ba inda zaka seka fada meya faru? Kaine fa kamin alkwarin zaka dena wannan hali na idan nama laifi kamin shiru ba tare da bayani ba, me na maka Love?"
"Love? Ki dena cemin love ki kirani da Ayaan dina zallah zefi"
"Kamar yaya saboda me?"
"Saboda bakya sona Zahirah da kinaso na bazaki taba shan kwayoyin hana haihuwa ba saboda karki dauki d'ana a cikin!"
A zabure ta dago tana kallansa
"Me kace?"
Be amsata ba ya shiga dakinsa ya kulle, dafa kai tayi tana karanta, duk adduar datazo ranta dan kanta gabadaya juya mata yakeyi, sallah tayi ta dade tana rokon Allah har barci ya kwasheta.

A wannan gabar kasa hakuri tayi, dan shekara biyar kenan bata taba kai k'ararsa gida ba ko makamancin haka, duk da sai ta irga irin wannan abun dasuka taba yi,wayarta ta lalubo tana kuka ta fadawa Ummu duk a binda ya faru, jikin Ummu yayi sanyi ta shiga bata baki, Ummi dake gefenta dan Ummu taje gidanta ta karbi wayar bayan taji abinda ya faru
"Ki dena kuka ki share hawayenki Allah na tare dake, matukar ina raye bazan bari a wulakantaki, zan kira Ayaan din kada ki damu kini?"
Da toh ta amsa sannan ta kashe wayar , Ummu ta dauki wayar zuwa dakinta, kai tsaye number din Mummy tayi dailing bugu biyu ta dauka dan wayar na kusa da ita
"Amina bazanyi dogon bayani ba, amma abinda kika kula kiyi gaggawar warwareshi dan kin san matukar ina raye bazan taba bari a ciwa 'yata mutunci ba"
"Me kuke nufi Zainab?"
"Kinsan abinda nake nufi Amina, base na tsaya bata lokacin bayyani ba, alkwari daya zan miki shine har kasa ta rufe idona bazan taba fadawa ko abinda ya faru ba, dagani sai ke se wadda kuka kula tare, sai anjima
Gumi ne ya ketowa Mummy dan karamin tsaki taja
"Wannan kawa dai ta zama masifa Wallahi duk hanyar danayi seta toshe mtsw"
Wayarta ta zaro ta kira doc naja,
"Naja abin da mukai ki warwareshi,"
"Kamar yaya?"
"Tanbayata ma kike?"
"Eh dole na tambaya saboda ina zaune ke kika tsara min yadda zanyi komi yanzu kuma se kice na warware ba tare da kinyi bayani ba"
"Amma dai kece silar kulashi dan haka ki warwareshi  nagode" ta katse wayar tanajan dogon tsaki.

Washegari Zahirah na tashi babu alamun Ayaan, kiranshi tayi kafin tayi magana yace
"Naje Lagos bussiness meeting din dana fada miki"
Da mamaki tace
"Amma kuma ai tare kafe zamu tafi?  3weeks fa kenan zakayi?"
"Yess na canza shawara ne, nama Ya imra magana zata turo miki me aikin ta zata tayaki kwana bye" ya katse wayar
Dafe kanta tayi saboda jirin dayake dibanta a haka ta rarafa ta dauko magani tasha sannan ta kira Ayrah
"Ayrah ya kk? Ya babyna?" Ta fada murya a kasa
"Lafiya lau Zahirah, Babynki gashi nan yanzu yayi bacci"
"Dan Allah temako zaki min, amma inasan dagani sai ke ki rike amana"
"Okay babu matsala,"
Ajiyar zuciyata ta sauke sannan ta fada mata duk abinda yake faruwa itada Ayaan sannan ta dora
"Kinsan abin mamaki? Wallahi alamun dayawa nake gani kamar inada ciki cuz 3months kenan rabon danayi period gashi sai nayita jin kasala jiri ke abubuwa dai dayawa"
Washe baki Ayrah tayi da ihu kamar tana gabanta
"Aikuwa wannan alamomine, bari na miki sending number doc din danake gani ki kirata kije ta dubaki amma idan hakan ne danafi kowa murna"
"Toh nagode amma karki fadawa kowa pleasee.."
"In sha Allah bari na miki sending no din"

Kiranta tayi, ta mata kwatacen asibitin, sai data biya culinary school dinta wadda ta bama Zeenat kawarta manager ita ke kula da komi na wajen seda suka gama  samnan ta wuce asibitin Gwaje gwaje da tambayoyi ta  mata sannan ta tabbatar mata da cewa ciki ne da ita na wata uku da sati1, a lokacin shiru tayi ta rasa mema zatayi godia tayi mata ta biya ta fito ta koma gida tasha kukanta data rasa dalilinsa.

"Whatttt???!! Amma kinsan shashancin nan naki ya kusa jan mutuwar aure? Wannan ya nuna baki san aikin ki na kenan tayaya zaki canza test result ki bani na wata? Kinsa na zargi matata kin tarwatsa min farin cikina" Ayaan ya fada yana huci saboda tsabar bacin rai bayan doc Naja ta kirashi cewa mistake tayi sai yanzu ta duba , ba result din Zahirah ta bashi ba
"Kayi hakuri dan Allah na rokeka, wallahi mistake ne tunda har kaga na kira na sanar dakai pls"
"Kinsan zan iya kaiki kotu? Inada right na shiga da kararki,"
Kafin ya karasa tayi saurin cewa
"Kayi hakuri dan Allah "
Katse wayar yayi tare da jan dogon tsaki, take ya tuno Zahirah da abubuwan dayayi mata wanda sam ya san be kyauta ba, wayarsa ya janyo yayi dailing number din umar
"Umar zan turo ma kudi kayi booking flight ka taho Lagos zakayi representing dina a meeting din nan, ina san komawa gida kuma it's urgent"
"Okay sir ba matsala"
Wayar ya aje a gabansa yana tunanin Zahirah da tunanin da wani yanayi ma ya kamata ya jeta mata?"

Tana zaune a doguwar kujera sai rawar d'ari take kasancewar zazzabi daya rufe mata jiki tun safe, gashi mai aikinta taje gida sai ita kadai
A hankali Ayaan ya turo kofar palour dauke da salama a bakinsa, tanaji da sauri ta kara sunkuyar da kanta tana dafeshi hade da amsa salamar a hankali, gabadaya daya be lura da ita ba, ya wuce daki be ganta ba kitchen da sauran dakunan amma ba alamunta, sai daya sake dawowa palour yaga bargo a kan kujera, da sauri ya karaso inda take yana yaye bargo ganinta tana kakarwa idanunta sunyi ja ga zafi jikinta kamar ana tafasa ruwa, a rikice yace
"Subhanallahi meya faru? Baki da lafiya muje asibiti"
Rufe bakinsa yayi daidai da shigowar Ummi a rikice ta karaso, sai data kusa bigeshi sannan ta gane akwai mutum
"Ayaan saukar yaushe?"
"Ko 30mint banyi ba da dawowa, meya faru da ita?"
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan ta dago Zahirah a hankali, jin haka yasa Zahirah sake kankameta
"Sorry kinji yanzu zamuje asibiti zaki samu sauqi in sha Allah" Ummi ta fada tana shafa fuskarta, galala Ayaan yake kallan Ummi gani tana neman fita da ita ba tare da izininsa ba, da sauri ya kalleta
"Ummi ina zaku?"
"Zan kaita asibiti sannan mu wuce gida"
"Kamar ya? Ummi ai ni keda hakin kaita saboda matata ce"
"Nafika sanin haka, amma for now, kayi min uzuri zuwa bayan magrib se kazo nan gidana ba gida Ummu ba" bata jira amsarshi ba ta kama Zahirah suka fita.

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now