14

573 57 2
                                    

A rikice Asaad ya karaso dakin Ummu, ganinta kwance ya sashi rikicewa sosaii , da hanzari ya tallafota
"Ummu meya sameki?"
Kasa magana tayi sai hawaye masu dumi dake sakowa a kan kuncinta, wayarsa ya dauko dake aljihu, ya shiga neman number Dr. khamees, yaci saa kuwa yana kusa da wayar take ya dauka hade da alkwarin cewa gashi nan tahowa
Yan mintuna kadan ya dauka kafin ya karaso ya shiga duba Ummu,

A fusace Assad ya banko dakin Zahirah, dake zaune tana waya da Ayaan, wani irin kallo yayi mata sannan yace
"Kinji dad'i burinki ya cika! Ga Ummu nan kwance ba lafiya kuma duk ta dalilinki!" Yana fad'an haka yayi wani tsaki yabar dakin.
wani irin tashin hankali ne ya ziyarceta, lokaci daya ta kidime, Ayaan dayaji shiru batai magana yace
"Are u alright?"
Bata bashi amsa ba, illa fashewa da kuka da tayi wanda ya sashi a cikin tashin hankali shima, a rikice yake tambayarta dalilin kukanta nata amma ta kasa magana, ta dan saisaita kanta cikin sheshekar kuka tace
"Ummm Ummu"
"Meya sameta?"
Wular da wayar tayi ta nufi dakin Ummun"

Ayaan ya zama speechless tun had'uwarsu be tab'a ganinta a irin wannan halin ba, gashi kuma tana kiran Ummu, Anya lafiya kuwa? kashe wayar yayi yafito cike da damuwa.

"Ya Ayaan, please kazo ka kaimu shopping din, kaga driver baya nan, nikuma wannan motar tamin girma bazan iya tukawa ba" muryar Azeema kenan data dakatar dashi, gefenta Ayrah ce sunci uban kwaliya kaman ba gobe
"Akwai inda zani , kingane?"
"Ya Ayaan dan Allah ka temaka, ke Ayrah ki sa baki mana" ta fada tana kallan ayrah
Dariya ma tabashi,
"Ke kinga nifa nagama magana" ya wuce motarsa da zumnar zuwa gidansu Zahirah ya barsu nan suna gungimi mussaman Azeema da take ta cika tana batsewa, an bata mata plan din data shirya

Yana isa gidan, mai gadi daya tarar a kofa ya gaisa dashi cikin girmanawa yace
"Sannu Baba meya faru a gidan ne?"
"Ai Ummu ce ba lafiya,"
Dogon ajiyar zuciya yayi
"Subhnallahi!Allah ya bata lafiya"
Mota ya koma ya nufi gida cike da tausayin Zahirah, yana san kiranta, amma yasan a yanayin data ke , abu ne me wuyar gaske ta iya daukan wayarsa dan haka ya nufi gida da niyyar anjima ya sake kirata ko kuma ya koma ya duba jikin Ummun.

"Damuwa ce ta mata yawa, gashi jininta ya hau sosaii, ta rage damuwa gaskiya in ba haka ba komai ze iya faruwa" kalaman Dr Khamees datayi karo dasu a daidai lokacin data shiga dakin,
Hankalin kowa ya dawo kanta, Asaad dake gefen Ummu wadda ke kwance tana bacci, yayi saurin tashi yana nuna Ta
"Ai duk ga dalilin damuwar tata nan, Abba kayi wani abu akai gaskiya ina gani wata can bazata zo ta saka mahaifiyara shiga damuwa ba!"
Dif hawayenta ya tsaya cike da fushi ta kalli Assadd.
"ya Assad ya isa please! Me kake cewa haka? Naga dai nima Mahaifiyata ce koh? Akan wani dalili zaka dinga fadar haka?"
Wata dariya yayi ta takaici, ya kalli Abba wanda ya dawo daga kiran da Dr. khames ya masa kafin ya tafi.
"Abba kana jinta koh? Nidai Abba gaskiya na gaji da wannan boye boyen a fad'awa kowa matsayinsa ya sani kawai"
Da fushi Abba ya kallesa
"Assad baka jine wai? Akan me zakuzo kan mara lafiya kuna mata hayaniya? Fice man dagani" a fusace Asaad ya fita daga dakin.
Da gudu Zahirah ta karasa wajen Ummu dake bacci , hannuwanta ta saka a cikin nata tana share hawayenta, tabbas tana san Ummu so ba na kadan ba, amma meyasa Asaad ke fada mata wad'anan kalaman? Maganganunsa ne suka dinga yawo a kwakwalwarta, me ya ke nifi da a fad'awa kowa matsayinsa? Meyasa duk ya dora abinda ya faru da Ummu akanta? Dole akwai waji boyenyen abu, jin motsin Ummu ne ya katse mata tunaninta, da sauri Abba ya karaso hade da tallafota
"Ya jikin naki Ummu Asaad?"
Murya can k'asa k'asa tace
"Da sauki, Zahirah yaushe kika dawo?".
"Sannu Ummu, dazu nandawo"
Shigowa Asaad ne yasa suka maida hankalinsu kansa, da sauri ya karaso ya rik'e hannunwan Ummu yana mata sannu
"Ummu Dr yace damuwa ce ta maki yawa, Nasan damuwarki duk akan Zahirah ne, yadda take neman bijeri miki , bayan ke kuma duk kinayi ne saboda farin cikinta, da kuma halin da kike tunanin zata shiga in har tasan abinda muke boye mata, Ummu a fada mata komai ko kya samu sassaucin damuwar da kike yi"
Wani kallo Zahirah kewa Assad duk notinan kanta sun kunce, ta kalli Ummu data sunkuyar da kanta tana hawaye
"Ummu dama akwai wani sirri da kike boyemin?"
Akwai!" Ummu ta fada da gaggawa
Wani irin kallo Zahirah ta yiwa Ummu me cike da mamaki gabadaya ta zama speechless
"Ummu me kike cewa newai,? kun sani a duhu! Ku taimaka ku fito dani, a min bayyani"
Hawaye ne suka shiga ririgen saukowa kuncin Ummu, taja dogon numfashi idanuwanta nakan Zahirah
"Tabbas akwai abinda muke boye miki Zahirah! Nayi duk iya bakin k'okarin na na ganin na kauda duk wani abu da ze sa har kiyi kokonton muna boye miki wani abu, amma yau... tunda har Asaad yayi sanadin kinsan cewa akwai abinda muke boye miki, inaga lokaci yayi da zan fada maki komai Zahirah..." ta karasa maganar tana hawayen
Tunda taji maganar daga bakin Ummu ya sata tabbatar da cewa tabbas Abinda Asaad din ya fada gaskiya ne, amma wani abu ne wannan me girma wanda ake boye mata shi tsohon shekaru? Duk a iya tunanin data yi , ta kasa samo hasashe guda daya wanda yayi daidai da abinda take ciki, kuka ta saki, kuka sosai me cike da tausayin kanta
"Ummu me kuke boye min da bansani ba?"
Dogon numfashi Ummu taja ta share hawayenta, shiru tayi tana tuno kwanan watan yau wanda ya kama ashirin da uku ga watan afirilu na shekara dubu biyu da goma sha bakwai(23/04/2017) gabadaya tunanin ta jefata baya , take duk abubuwan da suka faru shekara ishirin da suka wuce , suka dawo mata sabo......

To fa.... anzo wajen🙌🏻🙌🏻
A ganinku wani sirri ne wannan??🤔🤔


Kuna aje min raayoyinku please😁 shi ze kara bani gwiwa

#NWA
#ZHR
#Hafss
#love you all❤️

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now