*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAHIRAH**MISS HAFCY AND HAUWWA DAMARY*
6⃣
Da sauri ya kash motarsa ya rufe ya fito sai dai kafin ya karasa har ta hau napep tayi gaba
"Ya Allah" ya fada yayin daya dafe kansa.
Zuciyarsa ta ayyana masa ya shiga mota ya bi me napep din tun kan su masa nisa sai kuma wani abu ya fado masa, bashida tabbaci nacewa budurwa ce ko matar aure ce be kamata ya tunkareta kai tsaye ba tare da yasan wasu bayyanai akanta ba, dan haka sai ya juyo jiki bakwari yayi hanyar motarsa
"Ranka ya dade barka da fitowa" Habibu me saida kayan fruits dake kusa da company dinsu ya fada cikin girmamawa
"yauwa malam Habibu ya kasuwa? "
"Kasuwa Alhamdulilah ranka ya dade, amma wani abun kake nema ne na ganka a tsaye a nan? "
Ayaan ya shafa sumar kanshi
"Amm ba komai, amma dan allah kaga wata mata nan da hijab milk ta shiga napep yanzu koh? "
" eh naganta yallabai, wani abun ne? "Habibu yana fada yana kallan Ayaan
"inasan sanin bayyanai akanta ne, bansani ba ko zaka nemo min" Ayaan ya fada yana duban agogo
"sosaii ma yallabai, aiko Sambisa take zan nemo ma ita, na dai ganeta nan excellent catering school take zuwa, ai abin bazeyi wahala ba ka bani na da gobe zan nemo ma komai akanta yallabai"
Cike da farin ciki Ayaan yace to ba matsala hade da mika masa kudi a dunkule wanda dama ya saba da bashi tuntuni sannan ya koma motarsa cike da zullumin gobe."Ummu am sooo tired wallahi, rannan fa ba sauki" Zahirahh ta fada a daidai lokacin data cire hijab dinta
"Ai dole sannu ya gajiya, yau kuma me kukayi?
"Chicken meeryland, gashi dandana kiji tayi dadi? " ta zaro takeaway din ta mikawa Ummu, dandanawa tayi ta kuma yaba da yadda yayi dadi,
"bari na watsa ruwa Ummu" Ta shige cikin dakinta.K'arar shigowar sakon karta kwana(massage) taji a wayarta a daidai lokacin datake kokarin shiga toilet har zata shiga sai kuma ta dauko ta duba
"nasan ma wannan Muhammad M din ne, "
Budewa tayi taga sako a haku_Nasan kin gaji da dayawa ki huta My All banda yadda zanyi ne da bazan taba bari ki dinga shan wahala ba, go and have some rest please_
_Muhammad M_
Tsurawa wayar ido tayi tana kara karanta text din, lallai ko waye wannan bibiyarta yake taya akai yasan tana shan wahala haka? Bata taba yi masa reply ba duk da tsahon lokutan daya dauka yana mata text amma yau kuwa ya zaman dole ta mashi reply, dana wajen reply tayi ta fara rubutu kamat haka
_Koma waye kai, inaso in har ka cika masoyina na gaskiya kuma ka tabbatar da cewa kanasona to inaso ka bayyana min kanka in ganka ido da ido, inaga shine kadai hanayar da zata tabbatar da cewa da gaske kana sona_
_Zahirah Abdulra'uf_
Tana yin sending ta shiga wanka ta ajje wayar anan ta shige bandaki.
BAYAN KWANA2" _Ai garin masoyi baya nisa Zahirah ki kara hakuri lokuta kadan ne suka rage a cikin kwanakin dana debar miki kafin ki gani, zanzo gareki, zaki gani zan kuma hada kwayar idanuwana da naki na kuma furta miki cewa ina sanki, duk da bansan amsar da zan samu daga gareki ba buh bazan iya barin sakin ya zamo shine ajalina ba... Kwanaki kadan suka rage. The Countdown begins..... Insha allahu yau saura 20 days kiyi ido hudu da masoyinki na hakika .._
Ki kara hakuri
_Muhammad M_Wannan text din shi ta fara arba dashi data tashi karantawa tayi tayi tsaki ita yanzu ma ya fara bata haushi
"laifina ne dana mai text din ma se ya zata na damu dashi ai..." ta fada a kufule. Ganij lokacin yasata saurin tashi ta shirya cikij sauri sannan tayiwa Ummu salama ta nufi ECCS(excellent chef catering school)."Baiwar Allah Mintin daya dan Allah" Habibu ya dakatar da ita wanda hakan yasa saurin juyowa fuskarta dauke da murmushi dan akwai watarana da wani ya so fizge mata jaka anan bakin titin shine yayi iya bakin kokarinsa ya komashi ya kuma dankashi ga hukuma shiyasa kullum take ganin girmansa
"ina wuni malam"
"lafiya lau Hajiya kwana2
"lafiya lau wallahi"
"yauwa nikam kallo sani nake miki kamar kece Zahra ko da kike zaune a Jaen? "
Cikeda mamaki zahirah ta kalleshi
'Zahirah dai koh? Ai tun yaushe muka bar Jaen din"
Shi kanshi yayi mamaki dan kawai gueesing yayi ashe yaso yayi daidai da faraa yace
"Oh Zahirah kinsan sunan naki ne na yan gayu, Amma yaushe kukabar Jaen din bansani ba?
"mun dade amma bamuyi shekara ba"
"Allah sarki kinsan ni na dade da barin unguwar, amma yanzu kuna wata unguwar ne? "
"yanzu mu nan hotoro Gra"
"okay Allah sarki ya Ummu? " ya sake guessing
Mumshi zahirah tayi
"Tana lafiya wallahi,
"to in kinje kice Habibu na gaisheta, bani number dinki ma dinga zumunci zan kiraki sai ki bawa Ummu mu gaisa naga kamar har yanzu baki idasa gane niba"
"gaskia kam, amma ban haddace numberta ba" ta fadi hakan dan sam batasan ba maza numberta
"to kawo na saka miki tawa"
Ta mika masa wayar batareda ta so ba. Aikuwa yasa numberta ya mata wayo ya kira layin nasa seda ya tabbatar ta shigo sannan ya mika mata yana godia.
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...