12

604 56 2
                                    

   Rik'e hannuwansa tayi , ta dago jajjayen idanuwanta , cikin sanyin murya tace
   "Bansaka cikin maganan nan ba Asaad, karka k'ara shiga babu ruwanka, nagode da yadda kake kula dani, yadda baka san bacin rai na, amma in har ka kara sa baki a maganar nan to ba da yawu naba"
    Durkusawa Asaad yayi ya fashe da kuka.
     "Kiyi hakuri Ummu amma bazan iya jure ganinkina wannan hali ba bazan iya ba..."
   "To ka cigaba tunda dai hakane"
    Damke hannunsa yayi cike da bakin ciki da kuma tsanar Zahirah wadda ta k'ara k'aruwa a zuciyarsa,
share hawayensa yayi "Shikenan Ummu insha Allahu bazan sake magana akan hakan ba, dan Allah kiyi hakuri ki dena kuka"
    D'an murmushi tayi ta share hawayenta hade'e da cewa "na dena insha Allah"nan ya zauna ya cigaba da lallashinta

   Zahirah tunda Ummu ta fita ta durkusa take kuka, mamakin yadda Ummu take neman cusa mata wanda koda wasa bataso, wanda ya santa kokonton anya kuwa Ummun na santa? jin wayarta tana ruri ta tabbatar daa cewa Mubarak ne da sauri ta dauka batare da ta jira me zece ba
   "Ka kyauta Ya mubarak tunda har ka ke neman raba tsakaninmu da Ummu, baka san cewa hakan dakake k'ara sa na tsaneka yakeyi ba?"
  D'an murmushi yayi
  "Zahirah ni kike jefa da wannan kalaman?"
    "Abinda yafi haka ma zan iya, dan Allah ka rabu dani kaje ka sami Ummu ka fada mata cewa bansanka dan haka ka rabu dani"
   Wani tiriri yaji zuciyarsa nayi, take tsananin mamaki ya cikasa a lokaci guda kuma yana mamaki yadda Zahirah ta canza lokaci guda, dogon numfashi yaja sannan ya katse wayar cike da tsantsar bakin ciki,
    Jin sms ya shigo ya sashi sake dubawa da sauri a tunaninsa sakon ban hakuri Zahiran zata turo masa, hannunsa har rawa yake, ya bude sakon, sedai mamaki a cikashi ba kadan ba sanda yaga abinda sakon ya kunsa
"Dan ka kashe wayar wannan ba abin mamaki bane a waje na, amma ina ma tuni kayi gaggawar cire sona a ranka ka kuma je ka samu Ummu ka fada mata cewa ka hakura dani, nagode"
   Wular da wayar yayi ya runtse idansa cike da takaici.
************
Yadda Ummu ta zauna tayi shiru yasa Abban Asaad wanda yayi tafiya sai yau din ya dawo kuma akai saa itace da girki, ya damu matuka
"Safiyya!"
Firgigit ta amsa, ya kauda kai cike da mamaki
"Wai Safiyya so kike ki halaka kanki akan tunanin banza?"
"Ba haka bane Abban Asad, komai ya tabarbare,"
Kwashe duk abinda ya faru tayi ta fada masa, mamaki da kuma takaici da haushin Zahirah wanda dama danewa yake dan kawai ya sami farin ciki a wajen Ummun
"To kuwa tunda hakane, inaga lokaci yayi da zaki fayyace mata komai ta sani!"
Da sauri Ummu ta dago had'e da zare ido
"Kasan ne kake fada kuwa Abban Asaad?!"
"Nasani Safiyya, amma ki yadda da maganata tunda har takai ga ta neman bijere miki, akan abinda ke kinayi ne dan kare martabarta, to kuwa inaga lokaci yayi da zata fahimci komai"
"Amma bakaga ganin hakan ze iya jawo mata matsala gagarima?"
Gefen gado ya karaso inda Ummu ke zaune ya dafata
"Boye sirrin nan da kike, inaga bayyana shi ze zamo dalilin yaye dukan damuwarki,"
"Baka tunani ita kuma shi ze zamo mata silar bakin ciki wanda har abada bazata dena ba?"
"Meyasa kike fifita farin cikinta fiye da naki? Wanda na tabbata ita bata damu da naki ba! Ki dai yi tunani, kuma bance ki hana idanuwanki bacci ba, ki kwanta ki huta dare nayi"
Runtse idanta tayi tana tunanin kalaman Abban Asaad har wani nauyayan bacci ya dauketa
          Washegari shiru Zahirah bata fito breakfast ba, Asaad na zaune da Ummu sai Suhaima data shigo part dinsu suna breakfast, Ummu ta kalli Suhaima
   "Je ki kira Zahirah"
  Da dan gudu ta nufi dakin Zahirah ta taddata zaune rike da Dairy dinta tana dubawa
     "Ya Zahirah kije inji Ummu"
   Da to ta amsa sannan ta bi bayan Suhaima sai da ta gaishe da Ummu dake shirin tashi sannan ta gaida Asad ko kallan inda take beyi ba balle ma akai ga amsawa, ta zauna
    "Ga abincinki nan in kin gama kizo ki sameni a daki"
    Jim tayi tana tunanin dalilin kiran nata da Ummun tayi sai dai tasan tatsuniyar gizo baya wuce na koki, da sauri ta zuba abinci tana ci tana tunanin kalaman da zatayi amfani dasu wajen nusar da Ummu ta gane cewa ita bata san Mubarak ,Ayaan take so, dan haka ya zama dole yau ta kawo karshe komai..

         Ayaan ya fito cikin shigarsa ta bakar suit rike da glasses a hannunsa

  da sauri ya had'a tea ya kurbi kadan sannan ya kalli Mummy da itama ke yin breakfast   "Ka ci chips din mana" ta fada tana kallansa   "Aa mummy sauri nake wlh munda meeting ne,"   "To shikenan gashi yau zanyi tafiya"    "Mummy ina zaki?"      "Z...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.



da sauri ya had'a tea ya kurbi kadan sannan ya kalli Mummy da itama ke yin breakfast
  "Ka ci chips din mana" ta fada tana kallansa
   "Aa mummy sauri nake wlh munda meeting ne,"
   "To shikenan gashi yau zanyi tafiya"
    "Mummy ina zaki?"
      "Zanje Lagos ne kwana2 kawai zanyi akwai wasu kaya danai order zan je nagani, 2flight dinmu ze tashi nasan lokacin baka tashi ba, zamuyi waya kawai"
   "Okay Mummy Allah ya kaiku lafiya, keda su Azeema zaku?"
   "Aa nikadai zani"
    Toh Allah ya kiyaye se munyi waya ya fita da sauri
    Azeema ta kalli Ayra ta dan kifta mata ido a hankali ta ce
    "Crush ze tafi office, bako adawo lafiya?"
      Dan murmushi tayi tana juya teaspoon dake cikin mug din kanta a sunkuye tace
      "Shut up"
   Mummy dake lura dasu tace
    "Me ya faru?"
  Azeema tayi caraf tace
    "Nidai kam yau zan tona wallahi,"
    Harararta Ayrah tayi
      "Azeema me haka please!"
      Me ke faruwa wai? Mummy ta fada cike da tsarguwa
   "Mummy dama..."
    "Azeema pleasee..." Ayrah ta fada a marairaice
   "Dama cewa zanyi Ayrah tace wai tana san zuwaa park yau"
   Dogon numfashi Ayrah tace a zuciyarta tace
     "Thank God!"
    Dariya mummy tayi
    Akan wannan ne da kuke haka? ku dauki atm dina kuje ba matsala
     Da murna azeema tace yawwa.

       Suna shiga daki, cikin fushi Ayrah ta kalli Azeema
    "Azeema please... ki dena banso fa"
K'arasowa wajen ta Azeema tayi ta rike hannuwanta,
   "Okay kinfi son kiyi ta dakon so kenan?"

Wai shin wani sirri ne wannan da Ummu ke b'oyewa 🤔

One word for Zahirah please🤣😧

Me Azeemah ke nufi? Kodai Ayrah son Ayaan take bamu sani😳🤔

Ku biyoni cikin Next chapter muga komai

Vote , comment comment ku fadi ra'ayoyinku👌🏻 kar ku zama Ghost readers kunji👻
Ina sanku fisabilillah, kundai sani koh?😍🌹
#ZHR
#Hafsss
#NWA

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now