19

373 40 0
                                    

Shiru tayi batace komai ba,duk da yadda zuciyarta ke buga mata, gabadaya jikinta yayi sanyi, amma kwata kwata bata san koda wasa Ya Imra ta gane, shiyasa ta dane ta dan yi murmushi
"Komai da kika gani a rayuwa ya Imra yana tafiya ne da kaddarar mutum, Allah ya riga ya rubutu komai daze faru damu tun kafin muzo duniya, na dauki rabuwata da Ayaan a matsayin kaddara duk da wallahi ina san Ayaan, so ba na wasa ba , ko kadan banso yashiga wani hali ta sanadiyata ba, amma iyayena sun min zabin wanda zan aura, shiyasa na nesanta kaina dashi a tunanina haka zesa shima ya cireni a ransa, banyi tunanin ze sa shi cuta ba, dan Allah ki fadawa Ayaan yayi hakuri indai har Allah ya rubuta ni matarsa ce to wallahi ba wanda ya isa ya hanashi  aurena, yayi hakuri muyita addua"
Ya Imra tayi shiru jikinta tayi sanyi,
"To shikenan Zahirah Allah ya zaba mana mafi alheri" bata jira amsar zahirah ba tayi mata salama ta fita, tana fita Zahirah ta fashe da kukan data dade tana rikewa tun farkon hada idanta da Ya Imra, kuka sosaii me cike da tausayi, tashi tayi tayi alwala hade da sallah tana rokon Allah ya kawo mata mafita....

Ayaan.......
Kallo daya zaka masa kasan yana cikin tsantsar damuwa, yayi baqi ya rame kamar wanda ya shekara yana jinya, Mummy ce a gefensa tana zuba madara a cikin oat din dake mug din hannunta, dan tunda ya fara cutar becin komai se da kyar ma yake shan oats shima se ta tilasta masa, mika masa oats din tayi ,yayi saurin kauda kaii
"Ayaan dan girman Allah kasha, so kake ka kashe kanka lokacinka beyi ba? Bangaji dakai ba Ayaan duk ka samu a damuwa saboda wata banzar yarinya? Wani irin so ne wannan?"
"Ya imra ta dawo?" Ya fada yana kallan kofa
"Bata dawo ba, wallahi tun kafin nasan yarinyar nan har naji na tsaneta, yar gidan ubanwa ce ita da har zata saka a wannan damuwa? So take ta karasa mana kai na shiga uku ni Aminatu!" A daidai lokacin ya Imra ta shigo ganin ba faraa a fuskarta yasa shi dogon numfashi, tashi yayi da sauri ya rikota
"Kinganta Ya imra? Tana lafiya? Meya faru da ita?"
"Tanan nan lafiya Ayaan, amma tace kayi hakuri iyayenta sun zaba mata wani daban ka manta da ita a rayuwarka, kasani indai matarkace tokuwa seka aureta kadena damuwa kaji kanina,"
Shiru yayi take yaji sanyi a ransa koma dai mene tunda lafiyarta lau da sauqi, fita yayi da sauri yabarsu Mummy baki sake suna kallanshi"
Dafe kansa yayi a dakinsa daya shiga, take ya fashe da wani kuka me tsantsani, dole ne yaje ya ganta, akwai tambayoyi dayawa a ransa da ze mata, ina alkwarin dake tsakaninsu? Ina duk soyayyar tashi ta tafi? yasan cewa tana sanshi so me tsanani amma meyasa ta yadda zata rabu dashi? Anya kuwa? Wayarsa ya zaro  ya sake dailing numberta a kashe, dafe kansa yayi
"Ya rabbiii!!" Ya furta da dan karfi.
Key din motarsa ya dauko , rabon daya fita tun sanda ya fara cuta, bekoyiwa Mummy salama ba ya wuce me gadi ya bude masa kofa ya fita da sauri, a kofar gidansu Zahirah ya tsaida motarsa, da sauri ya fito beko kula mai gadinsu dake gyangyadi ba, ya wuce kai tsaye cikin gidan.
  Tana zaune kawai taji zaman dakin ya isheta, dan haka ta fito tsakar gidan tana tafe tanajin Alkuran karatun sheik Mahir, ta saka earpiece, tana rike da waya a hannunta, hangoshi tayi yana tafiya, ta kasa gasgata abinda idanunta suka gani, hakan ya sata sake murza idanta
Da sauri ya karaso inda take, jikinsa har rawa yake tsabar murna yama rasa me zeyi, da sauri ya karaso wajenta
"Zahirah da gaske kike kin fasa aurena? Da gaske zaki iya zama da wani a matsayin miji bayan ni?"
Hawaye ne ke rige zirara a kuncinta, batayi expecting ganinsa ba, duk da tana balain san ganin nasa amma ba yarda zatayi, hannu tasa ta share hawayenta, kanta a kasa tace
"Eh Ayaan kayi hakuri Allah ya zaba mana mafi alheri" da sauri ta juya zata tafi, batayi zato ba sai gani tayi ya cafko hannunta da sauri ta juyo tana kokarin kwatar hannun nata amma ta kasa
"No Zahirah! Kinasona bazaki iya rabuwa dani ba, Meyasa kike  azabtar da kanki ki azbatar dani ne? Bazamu rabu ba Zahirah, bazamu Rabu ba"
Kuka ne ya sake subce mata
"Inasanka Ayaan,wallahi ina sanka, amma kagane baze yiwu mu kasance tare ba, mu hakura da juna zefi"
"Meyasa zamu hakura da juna?"
"Saboda iyayena sun zabar min wanda zan aura bazan iya bijere musu ba, muyi hakuri"
Da sauri ta zame hannunta da gudu ta koma ciki, akan gadonta ta fada tana kuka kamar ranta ze fita, wani sabon so da shaukin soyayyar Ayaan take a halin yanzu, tayi kuka har ta gaji, itakam da me zataji, ga radadin rashin sanin asalinta da har yau dashi take kwana take tashi, abinda yafi firgita mata tunaninta shine in ta tuno ita ba ta hanyar aure aka haifeta ba, ga rabuwa da masoyinta wanda take kauna takeso dame zataji? Abin ya mata yawa, tashi tayi ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta dawo gado ta kwanta tana zubda hawaye.

Ayaan kuwa wani dishi dishi yake gani dakyar ya samu yakoma mota yanzauna yana zubda hawaye, ji yayi dama bezo ba dan sake ganinta dayayi ya sake rikita masa tunaninsa, kuna motar yayi yaga baze iya tukin ba, gudun kar yaje ma yayi accident a hanya, wayarsa ya dauko ya kira drivernsa yamai kwatacen inda yake , baa dauki lokaci me yawa ba ya karaso ya maidashi gida, dakinsa ya shiga ya kule ,bandaki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya yayi alwala yayi sallar isha dan a lokacin har ta dan gota an idar a mosque haka ya dade akan prayer mat yana kai kukansa ga Allah.

Mummy na zaune tana tunanin mafita akan Ayaan ayra ta shigo dakin itada Azeema, tambayar Mummy sukai ya jikin Ayaan ta amsa da da sauki ya shiga daki, Ayrah ta kalli Mummy
"Mummy dama Ummina ta kirani, wai next week zata shigo Nigeria takira wayarki bata shiga, nima kuma zan koma gidan Uncle hutun nawa na nan ya kare"
Ba karamin dadi Mummy taji ba, jin kawarta kuma abokiyar shawarta Zainab zata zo, dan kuwa koda bazata zoba tuni ta yanke shawarar taje har London din ta sameta, dan tana bukatar shawarata akan Ayaan, ta rasa yadda zata bulowa alamarin.
Dan ita da a kullum tunaninta be wuce ta aura mata Ayaan ba, ta kuma san koda wasa baze taba yarda ba, Fahad kuma kusan sa'anta ne balle a hadasu dan haka ta hakura ma ta dena wannan tunanin,

  BAYAN KWANA BIYU.
Shirye shiryen auren Zahirah da Ya Mubarak ya kankanma tuni dagin baban Ya Mubarak suka kawo kudi, Zahirah zaune ita da Ruks sunata tattaunawa akan events din da zaayi,
"Amma dai kinsan se munyi bridal shower koh? Naji kina cewa bakyaso" Ruks ta fada tana kallanta

"Bawani bridal shower ke daga Kamu se mothers eve, dinner ma dan Ya Asad yace ze hada ne amma ni bata wani dameni ba, besides ina nake da wasu kawayen da zamuyi bridal shower?" Zahirah ta fada tana tabe baki
   "Ke kuwa kike da kawaye, kin manta mates dinmu? Kece dai kika gujesu"
A daidai lokacin Ya Mubarak ya shigo gidan, Ruks cike da murmushi tace
"Ango ango""
Dariya yayi kedai Ruks bakya rabo da tsokana, Zahirah idan kun gama kizo inasan muyi magana
"Kawai dai kace na tafi sena baku guri, kaga dama ni tafiya zanyi nawa ango nata kirana" ruks tana tana daria ta fita, suma dariyar sukayi

   Mubarak yana kallan Zahirah yace
"Princess ki fada min gaskiya from the buttom of your heart, kinasan Ayaan har yanzu ko kuwa?"
Ajiyar zuciya zahirah tayi
"Ya Mubarak bazan boye maka, a kullum kokarin rage san Ayaan nake a raina amma na kasa, wallahi Allah idan da adduar dana kagu Allah ya biya min be wuce na cire Ayaan a zuciyata ba, kayi hakuri ya Mubarak kace na fada maka gaskia iya gaskiyata kenan" ta fashe da kuka
Murmushi Ya Mubarak yayi, abinda yayi expecting kenan dama so kawai yake ya ji ta bakin ta, cike da murmushi yace
"Go for your love princess..... na janye maganar aurenki danake nema, zanje na sami Ayaan dakaina"
A zubure ta dago ta kalleshi, daga mata kai yayi alamaun eh da gaske yake

"Ya Mubarak kar muyi haka dakai please, kaine kace na fada maka gaskia shiyasa na fada, dan Allah Ya mubarak kayi hakuri kar ka janye maganar aurenmu"
"Zahirah!! Ki gane abu daya, rayuwar aurenmu bazata taba dadi ba, bakyasona a matsayin yaya kika daukeni, shikenan nan kuma dan wani dalili daban,  se akace dole se ni zan aureki? Look nida Ummu munyi mistake babba, kuma ita kanta Ummu ta gane dagabaya, dan wasu da bama ki sansu ba sun aikata laifi har aka sameki shikenan se mu dora laifin akan ki? Bakida laifi Zahirah.. ko a gurin Allah bakida kaifi, bazan boye miki ba Zahirah na soki so bana wasa ba, ina tausayinki sosaii shiyasa sanki kullum yake  karuwa a zuciyata, amma yanzu na cire sanki a zuciyata na dawo matsayina na Ya Mubarak naki, zan sami Ayaan na fada masa komai, zaki aureshi in sha Allah "
"Ya Mubarak amma...."
Hannunsa yasa a sama labbansa yana mata alamun tayi shiru
"Kar ki sake cewa komai tashi kije Allah ya tabbatar da alheri"
da gudu tankoma dakinta  kasan banbace me zatayi, murna ko kuka? wani tsalle tayi ta doro akan gado hawaye ne a idanta amma fuskarta dauke da murmushi, Ummu taje ta samu ta fada mata komai, ita kanta tayi murna sai dai abu daya data tuno ne ya ruguza mata murnar datakeyi
"Idan aka gano asalin Zahirah fa? Yaya kenan!!!!!?????

Don't forget to Vote and comment 💕💕💕

ZAHIRAHWhere stories live. Discover now