Shirye shiryen biki nata kankama, a yau ne su Mummy suka dawo daga dubai hade da kayan lefe, Ayaan na zaune yana duba kayan, hankalinsa nakan night gowns da English wears , murmushi yayi dan yasan aikin Ya. Imra ne saboda sanda suna list din kayan lefe yace a sakosu dayawa, duba kayan yake yana yabon kyansu duk da yasan kudin daya bada ko rabinsu bazasu siya ba, kallan Aunt Jiddo yayi dake zuba kayan cikin akwatinsu
"Amma dai Aunt Jiddo kun kara kudi, cuz kudin dana bada nasan beze sai wadanan ba"
"Tab Ayan jiranka zamuyi? haba Ayaan wani ma yayi rawa bare dan makadi?"
Murmushi kawai yayi ya cigaba duba kayayakin.A cikin satin ne aka kai lefe na alfarma wanda ya dau magana ba kadan ba, duk abin mutum dole idan yagani sai ya yaba, akwatinanma daaka saka kayan daban ne designers ne nagani na fada, Su Ummi se zirga zirga ake, aikuwa suma su Aunt Jiddo da suka kai lefen anyi musu goma ta arziqi, akai abu cikin kwanciyar hankali aka watse bayan an saka biki nan da sati1"
Ayrah da Zahirah zaune a dakin Ummu suna duba kayan, dan su sanda ma aka kawo basa nan, sunje booking me lalle da zata zo har gida ta musu, bayan sun dawo daga wajen me gyran jiki datake mata kullum.
Zahirah kawai tsayawa tayi tana kallan kayan ita mamaki ma take wadanan duk nata ne? dan ita ko a mafarki batayi tunanin lefen ze kai haka ba, Ayrah ta bude akwatin sleeping gowns da English wears tana dubawa,
"Kaii lallai Ya Ayaan dagaske yake, toke se ki shirya irin wadanan arnan night gowns haka?" Ta karasa maganar tana dariya
Sai a lokacin Zahirah ta kare musu kallo
"Tabdi lalllai ni ina zan iya saka wadanan?"
Dan bugar ta Ayrah tayi cikin wasa
"Malama sanda zaki sama baki sani ba, kedai ki fadi gaskiya"
"Ke bawani nidai bazan iya sakawa ba, besides ke duk cikin uban kayanan abinda ya tsone miki ido kenan? To rufe ga kayan makeup nan a duba" ta karasa maganar tana rufe akwatin
Dariya kawai Ayrah tayi suka cigaba da duba kayan.Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji bahaushe
Yau ne za'a fara events, wanda zaa fara shi da Kamu, mai makeup Ummi ta dauko har gida tayima amarya sannan tayiwa su Ayrah, dan Ummi tace bikinsu ne komai su zasuyi, Inna ta fara warwarewa tun safiyar ranar take kuka, kukan farin ciki da murna da kuma idan ta tuno Zanira sai da Ummi tazo da Baba suka bata baki sannan tayi shiru, Zahirah tayi bala'in kyau cikin shigarta ta maroon da milk colour, tayi kyau kamar ba ita ba, ana gama makeup Ayrah ta dauketa a pic tayima Ayaan sending.Yana zaune a kan mota yana jiran JB yazo suje karasa raba IV din daurin aure, yayi saurin saukowa hadda tsale, ganin Zahirah yadda tayi bala'in kyau, da sauri yayi dailing number din Ayrah bugu daya ta dauka dan dama expecting kiransa take tasan dole ze kira.
"Ayrahh thank you so much, ki turo min account number dinki. I have a suprise for you, sannan do me a favour pls"
Ayrah ta juya ido cike da murna
"Wow! yanzu zan turo maka, wani favour kenan?"
"Pls kafin kuje wajen event din ki bari na ganta tukuna, pleasee"
"Kai Ya Ayaan tunda kagani a waya shikenan, zaka bata mana lokaci"
"Ayrah kar muyi haka dake ... please " ya fada yana marairaicewa
"Tohm shikenan idan mun fito kafin muzo wajen event din seka taho amma kayi sauri kar su Ummi su gane"
"Gani nan" yayi sauri shigewa motar tare da bata key yama manta da Jb. Minti kadan ya kawo shi wajen da sukayi zasu hadu dan ba nisa da inda yake, bedade ba sai ga motarsu Ayrah na driving Ruks a gaba sai zahirah a baya ita kadai dan Zeenat tace saurayinta ne ze kawo ta"Da sauri ya fita ya karaso motar, Ayrah ta dana key yayi saurin shiga,
Da sauri ya daga mayafin daaka rufe mata kanta, wani murmurshi ta sakar masa me kwantar da hankali
"Wowwwwww Baby Boooo, am speechless, kinyi kyau kinyi kyauuu" yaja maganar cike da farin ciki
Dariya tayi
"Nagode Love"
"Wallahi kamar na zauna naita kallanki, pls a tafi dani wajen kamun"
Da sauri Ayrah tace
"Kamar ya? Ai ba dakai aka tsara ba ka bari gobe kuna tare, yanzu dai Ya Ayaan ka taimaka ka tafi muje tun dazu Ummi ke fada wai mu kadai ake jira"
Badan yaso ba haka ya hakura ya fita ya koma motarsa zuciyaraa ba dadi haka dai ya hakura.Taro yayi taro sai amarya ake jira, Inna anci daurin ture kaga tsiya an tuno da da tana zaune ta hakimce a kujerar gaba itada mutanenta dan ta koma danzabuwa ta gayyaci kawayenta da suka rage, a lokacin da aka shigo da amarya saida Inna tayi hawaye mussaman data tuno kalaman data fadawa Zanira nacewa dole bazata rayu ba, sai gashi Allah ya raya abarsa har takai ga aure astagafirullah tayi sannan ta share hawayenta.
Anci ansha an kuma cashe, Ummu sai data taka dan ita rannar datake tajira ce yau Allah ya nuna mata, a lokacin da aka kira Ya Mubarak da ya Asaad a matsayin brothers din amarya, su fito sumata kara, bandir din dari biyar Asaad ya lika mata yayin da shikuma Ya Mubarak ya shiga lika mata yan dubu, yana lika mata kawai taji hawaye bata san sanda ta jingina a kafadarsa ba ta fara kuka, Hafsat Xoxo matarsa da tunda yake likin take kula dasu tayi sauri tasowa had'e da had'e fuska, tana zaro kudi a jakarta, dan ta kare kishin nata da liki, tana zuwa duk da haka Zahirah bata dago ba sai kukan da bata san dalilinshi ba take, yayinda shikuma yake bata hakuri, Xoxo ta dan sha kunu ta fara mata liki , sai tayi saurin dagowa. Tana kakalo murmushi, Mubarak da sauri ya karasa daidai kunen Zahirah yace
"kukan me kikeyi? Stop crying kinji amaryar Ayaan"
Bata san sanda ta fashe da dariya ba, shima dariyar yayi, a haka yaja matarsa suka koma kujerrsu.Su Ayrah da Ruks aje home training sukai suka baje rawarsu, sunyi rawa sun cashe akayi kamu aka gama lafiya..
Washegari ya kama rannar dinner....Ban tsaya editing sosaii ba, kuyi hakuri pls
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...