Kansa ya sunkuyar ba tare da ya kalli Zahirah ba, Kabiru ya miqo mata ita, shafa kanta tayi
"Ka kaima Hajiyan mama ita ai anyi yaye, abincin yayenta na dakin danake.Washegari email ya shigowa Abban Asad na wani aiki daaka tura shi US wanda ya dade yana jira, a rannar sukayi salama da Safiyya ya wuce, da kyar Asad ya yarda ya rabu da Ummunsa saida Hajiya tayi da gaske sannan ya tafi.
Safiyya bata samu ta warware ba har sai da Baba sukayi kwana5 da rasuwa , nan aka salameta daga asibiti , duk yan zaman makoki suka watse, Safiyya gabadaya taji Misau ya fita a ranta, nan dai suka yanke shawara saida gidansu na nan susuyi wani acan kano , su koma can tare da Hajiyan Mama wadda ita kadai ta rage musu, se Adda yayarsu wadda basu san ma duniyar datake ba,
Kabiru, Safiyya da Zahirah suka koma kano, kabiru ya cigaba da karatunsa yayinda Zahirah take zaune tare da Hajiyar, a haka dai suka cigaba da rayuwa cikin rufin asiri, Abban Asad kuwa tuno ya cala Us shida Asad da sabuwar amaryarsa Zainabu wadda ya aura bisa umarnin Hajiyarsa.Zahirah nata wayo abinta , babu wanda zeyi zaton ba yar Ummun Asad bace, rannan ta fita suna wasa wata yarinya sa'arta, ta dake ta, tuni yayanta ya shigo ya k'ara dukan Zahirah, wani dan saurayi wanda ze kai shekaru 15 ya karaso da sauri ya tallafo Zahirah
"Dena kuka kinji? Kinyi sabon yaya, matukar ina nan ba wanda ya isa ya tabaki, duk wanda yace miki bakida yaya kice musu kinada shi, kinada YA MUBARAK Kinji,"
hawayenta ta share tace toh da kanshi ya kaita gida suka gaisa da Ummu, tun daga nan wata shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin su, seka rantse da Allah yayan Zahirah ne, duk da mahaifiyarsa bata so amma haka nan ta hakura, duk wani abu daya shafi Zahirah wanda uba zeyi Ya mubarak keyi se ya zamana ya maye mata gurbi biyu , na uba da kuma yaya, duk da Kabiru baya wani shiga harkar Zahirah haka nan ma ji yayi ya tsaneta, duk da Ummu tana iya bakin kokarinta wajen ganin ya dena.Duk wani hanya da Ummu zata bi ngani cewa Zahirah batayi kukan uba ba Ummu da Ya Mubarak sunyi , duk da shidin yasan wace ita amma koda wasa betaba nuna mata ba, a haka ta taso da zanta cewar mahaifin ta ya rasu kuma bashida wasu dangi da suka rage a raye, Abban Asad kuma mijin Ummu ne wanda suka rabu, haka sukayi ta fadi tashi da ita har ta girma ta kawo yanzu, Hajiya Mama kuwa Zahirah na shekara 10 Allah ya karbi rayuwarta, Abban Asad kuwa dan dole seda Hajiyarsa ta tursasa masa ya aikowa da ummu takadar saki daya.
Ummu ta juyo ta kalli Zahirah, idanuwanta cike da kwala, sai dai gabanta ne ya fadi yayin data ga Zahirah kwance ta suma sakamakon tarihinta dataji, da sauri ta karaso ta dagata, basu tsaya bata lokaci wajen kiran Dr ba suka dauketa se asibiti, dakyar ta samu ta farfado idan banda kuka ba abinda takeyi
"Ummu dan girman Allah kice min duk abinda naji abaya mafarki ne, kizo ki tasheni kice min mafarki nakeyi ,duk abinda naji ba gaskiya bane, dan Allah ki fada,"
Hannunta ta saka a nata cikin nutsuwa ta fara magana
"Zahirah duk abinda kika ji daidai ne bani na haifeki ba bansan kowa naki ba, tsintar ki nayi a kangon bayan gida"
Wani ihu Zahirah ta saki, ta dafe kanta
"Nikuma k'addarata kenan? Ashe ni ba yar halak bace kenan? Ni wace irin mutum ce me butulci? Nayi kuskure babba ashe Ummu har mijin da kikeso kika rabu dashi saboda ni? Ko wadda ta haifeni bataji tausayina ba daga zuwana duniya jefar dani tayi ta tafi, ke da bakisan koni wace ba kikayi kasadar daukana, amma nake saba miki?, to su waye iyayena? Wacca mara imanin ce mahaifiyata? Na shiga uku"
"Kada ki saka damuwa a ranki, har yanzu a matsayin mahaifiyarki nake Zahirah, haifarkine kawai banba amma komai naki nice, Abu daya zaki min ki burgeni, ki manta da duk abinda na fada miki, nice dai har yanzu mahaifiyarki baki da wata bayani ni kinji?"
"Nasan wannan Ummu, banda wata uwa bayan ke, amma kinsani dole na damu.." ta fashe da kuka"Dalilin dayasa nace se kin auri Mubarak bawani dalili bane ila tsoron kada asalinki ya bayana, na tabbata idan har wani bare zaki aura dole ne se an bankado sirrin da duk duniya banso ya bayyana, Nace ki auri Mubarak ne bawai dan banasanki ba Zahirah ,sai dan gudun kada watarana ki gane wacece ke, banyi haka ba dan bana sanki ba, amma kuma nima da laifi na, kamata yayi na zaunar dake na fadi komai na ganar dake cewa wannan k'addara ce , kuma bawa baya wuce k'addararsa, Allah shi ne yayo ki a haka kuma ya barwa kansa dalilin, be kamata ace dan wannan dalilin mun hana ki zabin ranki ba, kamata yayi, mu nuna miki duk da cewa ga ta yarda akayi har aka samo ki, kema 'ya ce kamar sauran yara ,amma kuma idona ya rufe domin duk duniya abinda nake tsoro shine rannar da zaki gane bani na haifeki ba, keba kowa bace ila yar da aka haifa ba ta hanyar aure ba domin wasiikar mahaifiyarki ya tabbatar da haka, kiyi hakuri Zahirah ki kuma dauki kaddara, wannan itace kaddararki!!!" Ta karashe maganar tana kuka.
In banda innalalahi ba abinda Zahirah ke fada, wani irin abu take ji a zuciyarta ji take dama Allah ya dauko ranta yanzu kowa ya huta, gabadaya duniyar da komai ma isheta, kuka sosaii taci har tana shesheka, numfashinta na neman daukewa, lallashinta Ummu take itama tana kuka, sai da aka kirawo Dr ya sake dubata had'e da mata allurar bacci, da sauran magunguna, ya kuma gargadi Ummu da ta dinga kula da ita dan komai na iya faruwa, wannan dalilin yasa ko barci tare sukeyi da Ummu kullum cikin rarrashi da bata hakuri take.
Sai da Zahirah tayi sati 1 sannan ta dawo daidai duk da taimakon Ummu, ita kunyar ummun ma takeji ,ji take ba abinda zata yi mata wanda zata saka mata, Ayaan kuwa tuni ta dena daukar wayarsa ta kuduri niyyar zata auri ya mubarak koda kuwa hakan ze iya zama ajalinta, daya isheta ma cire layinta tayi koda yazo ma ta gargadi me gadi da cewar yace batana man, yau ma kamar kullum tana zaune ta zabga uban tunani Ummu ta shigo, gefen gadon ta zauna ta tallafo hannuwanta
"Lokaci yayi da zaki dena wannan damuwar Zahirah , komai ya wuce "
Fashewa tayida kuka ta rungume Ummu
"Ummu na amince wallahi zan auri Ya mubarak ina matukar sansa dan banda wani masoyi a duniya bayan shii"
Shiru Ummu tayi, salamar daya ji ne ya sta saurin tashi tana amsa salamar, zaune ta taddata cikin shiga ta kamala doguwar riga ce ash ta nanade kanta da mayafinta, tun daga nesa take mata kallan sani, sai dai kuma ta kasa gane a inda ta san fuskar, karaswa tayi ta zauna, a take ta rusunar da kanta ta gaisheta, kasancewar akan carpet din take a zaune, bayan sun gaisa tayi ajiyar zuciya
"Sunana Imra ni yayar Ayaan ce wadda yake neman diyarki zahirahh'
Sai a lokacin Ummu ta gane ashe kamar da sukayi da Ayaan ne ya sata take mata kallan sani
Cike da mamaki wanda ta lulubeshi da murmushi ta kalleta
"Sannunki da zuwa, ina fatan dai lafiya koh?"
"Lafiya ba lafiya ba, dan uwa ya kasa samun nustuwa a yanzu haka ma bashida lfy yana kwance duk dan ta dalilin Zahirah, ya kira bata shiga yazo yafi a irga ance bata nan, to dalinlin haka ne nazo naji ko lafiya tunda dai da lafiya lau suke ba wata matsala"
Jikin Ummu yayi sanyi sosaii ta rasa me zatace , cikin sanyi murya tace
"Bari na kira miki Zahiran ina zuwa"
Tashi tayi ta nufi dakin Zahirah din tana kwance idanunta sunyi jawur ,ayan kwanakin ta rame ta canza tayi baqi, dafata tayi
"Zahirah bakyajin magana koh? Yanzu kuma kukan me kikayi?"
Hannu tasa ta share hawayenta
"Nakanyi kukana duk lokacin dana tuno yadda nayi kokarin saba miki Ummu, baki cancanci haka ba Ummu baki cancanci haka ba.... ta sake fashewa da kuka, dakyar Ummun ta rarrasheta tayi shiru sannan tace
"Ga yayar Ayaan can a falo tana jiranki, bance ki fada mata komai dangane dake ba, amma duk abinda yake zuciyarki game da Ayaan ki fada, kina sanshi karki azabtar da kanki, na fada miki kowa kika zaba daidai ne, na kuma tabbatar koda yaji wacece ke baze taba gudar ki ba, yana sanki Zahirah"
"Nasan yana sona Ummu amma duk yadda yake sona bekai yadda Ya Mubarak keso na, dan haka bazan aureshi ba, Ya Mubarak zan aura"
Shiru Ummu tayi, itakam ta rasa yadda zata shawo kan alamuran nan, Zahirah ta tashi ta wanke fuskarta hade da shafa hoda da lip balm, tayi rolling da dankwalin abayar dake jikinta ta sauke nauyayan ajiyar zuciya kamar ba itace tayi kuka dazu ba, a Falo ta tadda Ya Imra zaune tana jiranta da murmushi ta karasa wajenta gade da gaisheta
"Sorry Ya Imra ina sallah ne,"
Shiru tayi tana kallanta
"Ba lafiya ba Zahirah dan uwana yana can rai a hannun Allah duk ta sanadiyarki!!!Assalamu alaikum ya kuke? Dafatan duk kuna lafiya, dont forget to vote and comments ku fadi raayoyinku pls yawan comments dinku shine ze bani kwarin gwiwar na cigaba da muku typing a kan kari Nagode💕💕💕
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...