Ga robar" almajirin dake tsaya a gabanta yana kallonta ya fada yana shide hannunsa, firgigit ta dago ta kalleshi
"Yi hakuri dan Malam juye ka ban kwanon"
"Ai na juye tun dazu" ya mika mata kwanan yana Allah ya karba sannan ta shige ciki jiki ba kwari, tama rasa gane meke damunta daga ganin mutum duk ta rikice, a sanyaye ta karasa aikin nata har Ummu sai data fahimci cewa ba qalau take ba
"Zahirah nikam me ya sameki ne?"
"Ummu kaina ne ke ciwo"
Jeki kwanta ki huta toh, da sauri ta tashi ta nufi daki ta kishingida sai dai da zarar ta rufe idananta hotan fuskarsa take gani tayi tayi ta manta amma sam hakan ya gagara. Murginawa tayi sai kuma ta tashi zaune ta saka d'an yatsunta a bakin ta wanda takanyi hakan ne a duk lokacin da abu ya shige mata duhu, mamaki take irin mamakin nan me tafe da damuwa, waye wannan yake neman mata kutse cikin rayuwarta? har yake sakata damuwa cikin yan awani k'alilin data ganshi, awani mafa kenan to zuwa kwanaki wani yanayi kenan zata shiga? ta hadu da maza dayawa tayi hulda da wasu amma sam bata taba jin irin abinda takeji game da wannan bawan Allahn data gani dazu ba, dan haka ta ayyana a ranta lallai akwai wani babban abu tattare da bawan Allahn *kauna ce* amsar data bawa kanta kenan, bazata kira hakan da so ba saboda tasan a baya takan so wasu mazan(crushing) amma kuma lokaci daya se ta nemi san ta rasa, amma bata tunanin hakan ze faru akan wannan bawan Allahn, tasan akwai babanci tsakanin kauna da so, So yakan canza sheka amma Kauna ita bata canzawa. A yanzu dai ita bata da wani abu daya kamata tayi illa addua, wadda itace makamin mumuni bazata iya canza k,addarata ba tasan da hakan. Saboda ita k'addara ba'a iya canzata. Allah daya hallicemu shine kadai keda ikon canza mana k'addararmu.*************
"Abban Asaad wallahi daidai da rana daya ban taba kinka ba, kuma ban taba jin dadin barin ka danai ba, amma dole ce ta saka Abban Asad bazan iya rabuwa da Zahirah ba kai ka sani, wallahi ko yau kace ka yarda zahirah ta zauna a gidanka tokuwa zan yarda a sake daura mana aure na koma gidanka"
Gyran murya Abban Asad yayi ya kalli tshohuwar matar tasa wadda yake balain so duk duniya sannan yace
"Ummu Assad na canza shawarta na kuma yarda da Zahirah ta zauna tare dake a gidana, ba yadda zanyi shekaru danayi babu ke tamkar a kaya nake haka nake jin kaina, ki yafe min kura kuraina na yarda zan dauki Zahirah a matsayin ya zan me mata uban zan bata gatan data rasa na daga mahaifi"
Wani farin ciki ne ya ziyarci Ummu wanda ta dade batayi irinsa ba, jin ta take wata sabuwa
" amma naji dad'i Abban asad irin dadin da bantaji irinsa ba, na yarda kuma na amince ko yanzu ne a daura aurena dakai na koma gidanka"
Cike da farin ciki suka k'arasa hirarsu wanda daga karshe suka tsayar a za'a maida aurensu ran jumma'a me zuwa."Zahirah kin kuwa san mun kusa komawa gidan Abban Asaad" Ummu ta fada cike da murmusmushi
A firgice ta d'ago ta kalleta cike da mamaki tasan sarai irin tsanar da Abban Asad yake mata yanzu kuma Ummu na cewa zasu koma gidansa
"Ummu haddani?"
"hadda ke Zahirah ki kwantar da hankalinki daka sa ya amince da ki zauna tare damu, sai a lokacin ta danji dadi amma duk da haka tana wasu tunanin.Shiryen shiryen komawa gidan Abban Asad ya kankama Tuni aka daura aurensu jummar data wuce gidansa ya gyra tsaf yau saura kwana biyu su koma.
Zahirah na zaune a falo wani dairy da Ya Mubarak ya bata as gift rannar data kamala secoundry daukoshi tay ta tsura masa ido kaf tunaninta be wuce na saurayin data gani ba daukon dairy din tayi ba. Cikin nutsuwa ta dan biro ta fara rubuta kamar haka
02 August
Bansan me so ba ban san kuma abinda yake wakana a duniyar soyayya ba, nidai kamar kowace Budurwace sai dai akwai abubuwa dayawa da suka babanta mu ciki kuwa harda soyayya amma a rannar nan, na san meye so na fada duniyar masoya saidai kash wanda na fadawa bansan shiba bansan asalinsa kuma besan ina yi ba. But duk da haka i still love him kuma bazan dena sonshi ba! inaji k'aunar shi a zuciyata fiye da tunani har nakanji kamar bazan iya rayuwa bashi ba, nayi azarbab'i koh? Lol sai dai kuma bazan kaucewa k'addarata ba, bansan yadda Allah ya tsara min rayuwata anan gaba ba amma inaji a jikina wannan bawan allah ze taka muhimiyar rawa a rayuwata
Lots of love. MR. RIGHTTa saka full stop kenan taji shigowar Ya Mubarak cikin sauri ta rufe littafin hade da kulleshi da dan mukulin dake jikinsa ta aje a gefenta k'okarin kakalo murmushi tayi ta kalleshi
"Ina wuni Ya Mubarak"
Lafiya lau kanwata, ya shirye shiryen tafiya a barni?"
"Lafiya lau Ya Mubarak zanyi missing dinka gaskia"
"Nima haka zanfi missing dinki ai but karki damu ai muna tare"
"Hakane" ta fada tana murmushiShiru sukai nadan lokaci a zuciyarta tanajin kamar ta bashi labarin Mr. Right sai dai kuma kunya takeji duk da ta daukesh kamar yayanta uwa daya uba daya ba abinda yake boye masa amma wanan kam ji take kunya bazata barta ta fadi ba.
Yau ta kasance rannar da Ummu zata koma gidan Abban Asad shirye shiryen sun kankama duk dun dauke kayansu sun maida can, Abban Asad mutum ne me hali dan haka gidan da Ummu zata tare ba karamin gida bane gida ne babban bene me dauke da manyan manyan daukuna kasa shine na Ummu yayin da Sama aka bawa kishiyar Ummu wadda ake kirada Jidda da Abban Asad ya aura bayan rabuwarsu da Ummu. Bayan yar walima da Abban Asad ya shirya tacin abinci wanda sukai a wani baban restuarent dake kano kai tsaye suka wuce gidansu cike da farin ciki. Daki daya aka warewa Zahirah me kyan gaske nan ta sauke ta gyra. Ta zaune tana sake sake har wani nauyayan bacci ya dauketa.
**********
A hankali yake kwankwsa kofar gidan cike da nutuswa tsahon minti daya ganin ba'a bude ba yasashi zaro wayarsa dake aljihunsa kan ya karasa kiran an bude kofar hakan yasashi maida wayar tasa cikin aljinhun ya shiga. Tun daga nesa ta hangoshi da gudun gaske ta yarda Teddy din dake hannunta ta rugumesh, cak ya dauketa ya dagata sama
"cutiee i missed you so much"
Cikin maganarta da bata gama kwaranyewa ba tace
"i Missed you too uncle yaan"
"Baby naga randa zaki iya sunan Fav uncle din naki, Me wani Uncle Yaan kina kara girma har yanu bki iya fadin sunanhi ba Uncle Ayaan ne ba yaan kinji loh? " wata kyakyawar matashiyar mata ta fada fuska dauke da murmushi wadda kalo daya zaka mata ka tabbatar da cewa lallai itace mahaifiyar yarinyarnan kuma tanada alaka sosaii da Ayaan.
Dariya yayi ya sauketa ta shige daki da gudu,
"Ayaan akwai abinda ke damunka"
Matar ta fada tana karantar yanayinsa
"Ya imra... Nothing's wrong am finr" ya fafa yana kirkiro murmurshi.
Cup din dake hannunta ta aje ta zauna sannan ta masa alamar shima ya zauna sauke numfashi tayi ta kalleshi cike da nutsuwa tacr
"Ayyan akwai abinda ke damunka., ko ka manta da cewa hakuwar da mukai tasa cewa aduk sanda kake cikin damuwa kallo daya nak maka nagane haka, nifa yayarkace da muka fito ciki daya dakai tunda kake baka taba boyemin damuwarka, Ayaan ka kalli idona ka fada min cewa ba abinda ke damunka, Look into my eyes and tell me" ta fada tana me kureshi da ido. Kaudar da idansa yayi ya dunkule hannayensa ya dora akan habarsa hade da sauke wani nauyayan numfashi ya kalli Ya Imra ido cikin ido
"Ya Imra akwai matsala. Bansan taya hakan ya faru ba kuma bansan taya anmiki explaining ki gane ba but all i know is im madly in love!"
Murmushi ya kufce mata tare da fad'in"Alhamdllah Ayyan na jima ina jiran wannan lokacin, iyye our Ayyan is now all grown up, meye sunanta? Daga ina take? A ina take schooling?"
"Shine damuwan Ya Imra,I don't know anything about her"........To Fa! Anzo wajen😅 me zakuce game da wannan chapter din?
Ina me cigaba da baku hakuri dagane da rashin samun updates akai akai, abubuwa sunmi yawa ne kuma ina me farin ciki sandar daku cewa yanzu nida hawwadamary a userHawwadamary keyin novel din, ina fatan zaku binmu sannu a hankali dan ganin inda wannan novel ya nufa
Mungode😍
#ZHR018 #Hafsy nd Hawwadamary #Loveyou all😍
YOU ARE READING
ZAHIRAH
Mystery / ThrillerKamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana t...