BABI NA ƊAYA

27.1K 1.1K 92
                                    


بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ
الرَّحِيْم.......

In The Name Of Allah, The Beneficent, The Merciful.

Da Sunan Allah Mai rahama Mai Jinƙai .

.

1

SHIMFIƊA

Ƙauyen Mairambiri , wani ƙauye ne , ko kuwa "ƙaramar Alƙarya" da yake tsakanin ƙananan hukumomin bama da konduga, wanda suke a karkashin jahar ( BORNO )
Mutanen garin mafi akasarin su barebari ne " kanurai", sai kuma shuwa, da fulani, tsilla-tsilla, babbar sana'ar mutanen garin shine noma, suna da makarantun primary da secondry na gomnati, sai kuma makarantun allo da mafiya yawan yaran garin shi suka fi zuwa ,tsiraru ne suke zuwa bokon da suke kira karatun "Malam nasara", kasancewar garin nasu yana tsakanin manyan-manyan hukumomi biyu ya sanya suke da kasuwar su a bakin babban titin da yake tsakanin garin bama da konduga" wacce take ci duk ranar Alhamis.

**************

Cikin wani ƙwarababben gidan kasa , wasu yara ne su uku mata, suna cin wani zazzafan damalmalallen tuwon hatsi miyar kuka shar cikin wani tsohon kwanon da duk lamba da tsatsa suka gama munana shi , babbar baza ta wuce shekaru 16 ba ,sai ta tsakiyar me kimanin shekaru 14, sai kuma ƙaramar su me kimanin shekaru 8.

Cikin nutsuwa babbar ta ke kai lomar tuwon bakin ta bayan ta sanyawa ƙaramar su ita ma a bakin ta ,saboda zafin tuwon ta kasa sanya hannu taci ,"alama yanzu aka sauke dumamen tuwon daga wuta "duk da yanzun farar safiya ne ko 6:30am bai cika ba.

Wata doguwar mace siririya me ɗauke da wata irin farar fata sol-sol kamar ta so ta zama zabiya " Albinism"dan hasken ta yayi irin nasu, wacce da ganin ramar da take da shi na tsabar wahala da talauci ne ,tana zaune kofar wani taƙwarƙwasashiyar rumfa da alama madafi ne ganin yadda duhun wajen yafi na ko'ina a gidan, hannunta riƙe da wani jariri namiji kansa tanƙwal da aski , ta ciro yamushashen siririn maman ta tana kokarin cusawa yaron a baki shi kuma daga ya kama yayi tsotsa ɗaya-biyu yake sakewa ya cigaba da tsala kukan da yake da alamun yunwa ce ke addabar sa .

Wani baƙin dogon mutum ne, ya bullo daga bayan durkusassun ɗakunan nasu guda biyu ,hannun sa rike da babbar robar ruwa (table water ), wacce aka yanke daga wuyan ta zuwa sama gefen ta daga kasa yana ɗan ɗigar da ruwan ciki daidai inda ya ɓule aka toshe da bakar leda .

Duƙawa yayi tare da wanke baƙaƙen kafafuwan sa da suke sanye cikin waɗansu ratattakakkun silifa (da guntun ruwan ) ,ya ɗago tare da kallon sashin da ƴaran nan suke zaune ya ɗan ɗauki wasu daƙiƙai yana kallon su cikin nazarin yadda babbar cikin take ta ciyar da kannan nata domin ya zuwa yanzu dai su duka biyun ita take sanya hannu tana zaƙulo tuwon da ya dilmiye cikin tsululun ruwan miyar da ta haura tuwon yawa har ta shaa kansa ,tana zaƙulo shi sannan ta hura iskar bakin ta ta gutsurawa ɗayar a hannu ta sanyawa karamar sauran abakin ta ,
kuma a take ta sake mayar da hannun ta cikin kwanon da hanzari tamkar dai ita bata jin zafin tuwon .

Yakaka "nyidin biri bun" baa ? Duwan "bii lanyen wande kausuzuin (yakaka ke baza ki ci abincin bane ? Kiyi sauri ki ci mu tafi kar rana ta yi ) cewar wannan mutumin ga babbar ɗiyar ta sa da ya kira da suna yakaka cikin yaren su na "KANURI .

Amsa masa tayi da "toh" ,dai-dai lokacin da ta miƙe da hanzari ta zagaya ta bayan matar nan da hasken fatar su yake yanayi ɗaya da nata ,ta ɗauko wani bakikkirin ɗin tiren kwano da yayi fatsa-fatsa da lamba ta nufi fasashiyar randar su da take binne a kasa sai iya fasashen bakin ta ake gani a waje "wanda za'a iya zaton rami ne" ta sunkuya tayi goho ta kwarfi ruwa a chan kasa ta ɗauraye farantin ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now