BABI NA HAMSIN DA HUƊU ( MAI RABON SHAN DUKA )

10K 653 114
                                    

Ganin irin mummunan kallon da Doctor Hamza yake yi mata bai karya guiwar Sofi ba da zai sa har ta gaza yin wani yunkuri kare kanta ba .

Dan kuwa zuruf ta miƙe bayan ɗan taƙaitatatcen tunanin da ya gifta mata da bata yi ƙasa a guiwa ba ta fara ƙoƙarin tattaro nata makaman yaƙin "ai ba zata bari Yakaka ta ci ta da yaƙi ba haka nan take .ta aiyana hakan a zuciyar ta

"Doctor ka ga'.....

Wata irin tsawa Doctor Hamza yayi da ba ita Sofi kaɗai ba ,hatta Sam sai da yayi zillo yana ɗan kuka ya koma bayan kujera ya laɓe.

"Kar ki ce min kome Sofi , bana buƙatar jin ƙaryar ki ta banza abunda nake so kawai shine ...

Ɗan jim yayi yana kallon ta yadda ta wani irin saƙare cikin rashin madafa matsanancin tashin hankali gami da wani nisassashen yanayi shimfiɗe akan fuskar ta inda take bata motsa ba , ba domin tazarar dake tsakanin su na da ɗan yawa ba da babu abunda zai hana ya iya jin sautin bugun zuciyar ta..

"Ki tafi gida Sofi .

Ya ce da wata irin kakkaurar murya yana ɗauke ganin sa daga kan ta ya zagayo da Yakaka daga bayan sa yana sake bin jikin ta da kallo kamar dai yana yiwa Sofi nuni da mummunan laifin da ta aikat ,yana kallon fuskar Yakaka tamkar ita yake yiwa maganar ya ɗora da cewa.

"Ki je gida akwai buƙatar ki sake samun ƙarin tarbiyya irin ta masu hankali da cikakkiyar koyarwar Islama ko ɗaya ba zan iya sake jimirin ɗaukar salon haukar da kike yi ba .

"Ki tafi gidan ku Sofi.

Ya furta hakan da buɗaɗɗiyar muryar da yasa kuka tahowa Yakaka da sauri ta shige cikin jikin sa tana zagaye shi da hannunwan ta , matsanancin tsoro na ɗarsuwa a ran ta ganin ɓacin ran sa Mai tsanani irin wanda ta daɗe bata gani ba.

"Ga Sofi kenan matar son sa da ita ce ta kora ta layin.

ina ga ita kuma ? Da ta yaga kayan ta da kan ta ? Watakila idan ya gama da Sofi ya dawo kan ta "shikenan Hajja ta jawo mata .

Hannun sa da ya sauke a bayan ta yana ɗan buubbuga ta alamun rarrashi yasa ta ji nutsuwa ta fara dawo.mata da sauri ta ɗago kan ta tana kallon fuskar sa da shi ma ita yake kallo.

Zata yi magana ya hana ta ta hanyar jaan hannun ta zuwa hanyar ɗakin sa ba tare da yace ƙala ba

A ɗan tsorace ta dubi sashin Sofi har lokacin tana nan a tsaye inda take tamkar an dasa ta kallo ɗaya ta yiwa fuskar ta tayi saurin janye idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ta doka da ƙarfi babu shakka ta hango wani lamari mai kaifi daga cikin idanun Sofi da suka tara ruwan hawayen da basu kai ga zuba ba '

"Ki tafi tare da dabban da kika kawo min gida bana so na fito na ga ɗayan ku .

Doctor Hamza ya furta hakan kafin su kai ga shiga ɗaki.

Wani irin tsuma jikin Sofi yake so take Allah ya kawo wani ya wanka mata marin da zai farkar da ita daga mummunan mafarkin da take yi "Doctor Hamza ne da kan sa yau yace ta fita ta bar gidan sa ? Razanar da ta tsinka mata gudun jikin jikin bai wuce dalilin korar ta ta ba " akan wannan kuchakar 'yar gudun hijirar 'Yar talakawa 'yar ƙauyen ne Hamzan ta ya kore ta?

Kai ina ƙarya ne lokaci yayi da zata farka daga gyangyaɗin da take yi da har yasa tayi saken da wankin hula ke shirin kai ta tsakar dare akan Yakaka.

Ihu take son kurmawa amma tana ganin a halin da take ciki babu lokacin ihu , da gudu ta taka ta hau sama ɗakin ta mukullin motar ta kawai ta ɗauka sai fa wani siririn mayafi da ta rufa akai ta fita daga gidan .

Wani irin gudu take yi a kan titi da ya zarce ka'ida tana yi tana dukan kan ta da hannun ta ɗaya .

Lokacin da ta shiga gidan su kai tsaye falon Momy kori ta zarce wacce bata san da shigowar ta ba sai da ta ji ana mata rotse a falo ta yunƙura daga kwanciyar hutun da take yi akan gado ta fito tana cewa "meye haka ? Meke...'

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now