BABI NA TALATIN DA TARA

6.8K 934 230
                                    

Duk yadda Falmata take tunanin daɗin dake ga mallakar idanu ta tadda shi ya wuce haka , jin kanta take tamkar sabuwar halitta ,

Har bata so bacci ya shiga tsakanin ta da ganin hasken duniya , karambani kuwa babu irin wanda bata yi , har girki take karambanin yi Yousssouf kuwa yana taya ta ,

Shima a ɓangarensa baya gajiya da duk wasu tambayoyi da ko karambanin da zata yi , wani irin son ta yake yana riritata ,

Mama da kanta tasan cewa yanzu Mamarta ta samu waraka saboda wata kulawa na musamman da idanun ta sun hango mata wani ɗan datti a jikin kayan Mama zata yi maza ta gyara ta ta sauya mata wani ,

A kullum ta Allah sai ta miƙa godiyar ta ga Youssouf kamar yadda cikin duk wasu sallolinta sai ta ƙara godewa Allah akan wannan babbar kyauta da ya yi mata na dawo mata da ganin ta ,

Godiyar da take yiwa Youssouf ba a fatar baki kaɗai ta tsaya ba , har a aikace take gwada masa ta yadda take nuna masa ƙauna tare da ɗaukar buƙatun sa ba tare da gajiyawa ko ƙorafi ba .

Kamar yadda likita yace tana cigaba da zuwa ana dubata , babu wata sabuwar matsalar da ta ɓullo tunda aka yi mata aiki .

Idan tana da wata damuwa to ta lafiyar Mama ce wacce kwana biyu ciwon ta yake ƙoƙarin tasowa suna danne shi da tarin magunguna gami da ƙara ƙaimi wajen kulawa da ita , amma duk da haka kallo ɗaya za'a mata a iya hango tarin raunin dake tare da ita tun daga cikin raunanan idanunta da suka ɗan sauya launi zuwa ruwan ɗorawa har zuwa ƙafafunta da hannayenta da suka ɗashe suke yawan ɗaukar sanyi ,

Gaba ɗaya Falmata da shi kansa Biyamuradi Youssouf basa tare da walwala sosai ,

"Baban Mama ko dai za'a sake komawa asibitin nan ne maganar aikin Mama ,

Youssouf wanda yake shafa kan Mama wacce take kwance cikin jikin sa lamo , ya ɗago kan sa yana duban idanun Falmata da suke nuni ƙarara da damuwar da ruhin ta ke ciki ,

"Fatima duk wassu bayanai da zamu sake samu daga Doctora basu wucce batun baya da sunka faɗi muna , wanda kouma mun bar Lamari ga Allah zouwa lokacin da za'a samu damar yin aikin ,

Shiru tayi tana cigaba da kallon sa , cike da damuwa , so take yayi wani yunƙuri kome ƙanƙantar sa ,

Ji yayi gangar jikinsa na karban sakon dake fitowa daga cikin ƙwarar idanunta masu kyaun kallo ,

"idanun ki suna da kyau idan kina kallon Mutum da su Fatima , lokacin da basu da Lafiya kyan su bai kai haka bayyana ba , kina da sassanyan kallo Mai cike da nutsuwa ,

Murmushi tayi kaɗan , kafin ta ƙira sunan sa ,

"Baban Mama ,

Sai kuma tayi shiru ,

Kamo hannunta da yake kusa da shi yayi ya riƙe ,

"Ummh ina jinki menene ?

" daman nace ko zamu je ni ɗin a gwada ni  ?

"gwaji Fatima wanne irin gwaji , akwai damuwa ne ga lafiyar jikin ki ?

Sunkui da kan ta ta sake yi tana jin nawin zancen akan harshen ta , sai dai tana jin zata iya yin kome domin ganin Mama ta samu lafiya , muryar ta a ciki tace ,

"ko Allah zai sa a dace un-un ko wai a jikina akwai abunda da za'a iya amfani da shi wajen yiwa Mama maganin ,

Kiris ya rage Biyamuradi Youssouf ya kwashe da dariya , sai dai ya gintse saboda yana son jaan ta ,

" Fatima kin manta likita yace ke baki iya bada jinin ki ?

Cikin sauri ta katse shi ,

" ai ba jini na ba , wai a auna ko akwai cikin ?

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now