BABI NA GOMA

5.5K 557 57
                                    

Shiri yakaka take sauri-sauri , tana yi tana taya falmata yin nata shirin , cikin mintocin da basu gaza goma ba har sun kammala , duk da dai kayan su na jikin su da suka cire suka sake mayarwa amma bisa ga dukkan alamu da su da kayan nasu sun ɗan samu tsafta domin sun ɗan yi haske , hakan kuwa bai rasa nasaba da wanka da wankin da suka samu damar yi tun a dare jiya bayan da suka tsaida shawarar fara fita neman na kansu cikin gari a ƙarƙashin jagorancin kolo da yagana ,

Kamar yadda kolo ta tsara musu shine su yakaka da yagana kowacce zata fita neman aikatau , yayin da falmata kuma zata zauna a bakin kasuwa tayi bara ,"

Da farko yakaka bata amince da yin barar falmatan ba , turjewa tayi sam tace sai dai falmata ta bita inda zata samu aikin ta zauna ta dunga jiran ta har zuwa lokacin da zata kammala ayukan sai su koma tare , abun da duk ta samu tayi musu hidima tare , kuma abun da duk ta ci , ta bawa falmatan ,

Sai dai ga mamakin ta firr falmata taki ta amince da tsarin ta , ta tsaya kai da fata akan lalle ita ma sai ta nemi hanyar taimakawa kan su wanda kuma hanyar a yanzu ɗaya ce ita ce yin bara , idan har kuwa baza ta amince tayi bara ba toh sai dai tayi zaman ta kawai a cikin camp domin bata ga amfanin bin ta da zata yi kawai ta zauna ba .

Ala tilas ta amince mata domin gudun bacin ran ta, da kuma sanin cewa baza ta iya fita daga camp ɗin ta bar falmatan ba , toh ta bar ta a hannun wa ? Ga larurar da take tare da ita , amincewar ta shi ya zama dole sai dai bisa sharaɗin baza su nisanta da juna ba , dole a tsukin gurin da falmatan zata yi zaman barar ta anan ita ma zata nemi nata aikin .

_____

Yakaka , falmata ku fito mu tafi mana kar muyi rana , kolo ta riga ta gama magana da mai tsaron kofa
,"yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da take ƙarasowa bakin kofar ɗakin da su yakaka suke ,"

Gamu nan yagana mun gama shiri sai tafiya ,"
cewar falmata fuskar ta ɗauke da yalwatatciyar fara'a a karo na farko da yagana ta gan ta cikin farin ciki kwatankwacin wannan , wanda bata raba ɗaya biyu murnar zasu fara dasa harsashin cigaban su ne a karon farko cikin tsananin rayuwar da suka tsinci kansu ,"

Hannunwan su sarƙe da na juna suke sanya kafafun su domin barin cikin sansanin su da suka wanzu a cikin sa tun ranar da suka shigo birnin na maiduguri , yayin da sashi guda na zuciyoyin su ke cike da fata tare da burin zuwa su nemo na kan su ,gefe guda na zuciyoyin nasu kuma fargaba ne tare da taraddadin yadda fitar ta su zata kasance ,

Sansanin su a bakin babban titi yake dan haka basu sha wahala ba wurin samun motar bus da take jigilar mutane zuwa kowanne sashi na garin ,

Kasuwa monday market
Kolo ta furta bayan ta tsaida wata kwaraɓabɓiyar motar bus da take ɗauke da mutane jingim a cikin ta ,"
Shiga muje
Cewar conductor ( karen mota ) wanda ya wangale musu kofar motar ,
Ni ɗaya ce zan zauna akan kujera su akan inji zasu zauna ,"
cewar kolo dai-dai lokacin da take shigewa cikin motar domin yi wa kan ta matsugunni ,"
Wata zamiya kondoktan yayi tare da zabura ya babbake kofar motar ,"
Nai gamma waɗannan ƙattin ƴan matan har su uku ne zasu hau kan inji kut ? ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now