TALATIN DA HUƊU

11.1K 996 255
                                    

Fiye da awa ɗaya Samy baby ta kwashe tana shirya Yakaka , wacce ta sha fama da kanta kafin ta iya tsayar da hawayenta batare da bari Samy baby ta fahimci cewa ta san manufar ta ba ,

Wacce ta shagaltu wajen shirya ta tana jaan ta da hirararrakin da suka shafi jin daɗin duniya , wankan da kansa so tayi ta wanke ta sai dan ganin ba fuska ya sanya ta tsayawa daga bakin ƙofar banɗakin tana sake jaddada mata ta fa yi wankan nan siral ta fita , domin inda zasu tafi waje ne na manyan ƴan gayu kar ta sake tayi abinda zata jawa kan ta raini ,

Daga cikin banɗakin nan ta ci kukan ta a ƙarshe ta tattara duk wani tunani nata da Allah ya mata baiwar sa ,ta matse ƙwaƙwalwar ta, ta haɗa kai da bango akan tunanin hanyar da zata bi ta samarwa da kan ta mafita .

Ƙarfe baƙwai na dare suka fita a motar Samy baby dukkanin su sun ɗau kwalliyya ta gani a faɗa ,

Duk da fuskar Yakaka a tamke take da bayyanannen ɓacin rai hakan bai hana kyaun da tayi ratsowa ba , dai-dai tana karya kan motar ta fito kan titi sosai Samy baby ta dubi sashin Yakaka a kaikaice ,
Yanzu ke Yaks meye haka ? Dan asara akan na hana ki saka wannan uban barigizan hijabin naki shine kike wannan ƙuncin ? Mts!

Ji wannan ƙatuwar jakar da kika ɗauko kamar wata wanzamiya na faɗa miki bata dace da ƙwalliyar nan ba , ƙwalliyar nan taki ba ta babbar jaka bace ta ƴar ƙaramar jakar hannu ce amma kin ƙi ji , ai daman ɗan ƙauye sai ya shekara hamsin a birni yake barin ƙauyenci da gidadanci , ke kika sani sautun mahaukaciya !

Ta danna motar da gudun gaske suka cilla kan titi cikin manyan unguwannin abuja da ko sau ɗaya Yakaka bata taɓa kai ƙafar ta bigiren ba tun zuwan ta garin .

Bata cewa samy ƙala ba illa sake rungume jakar ta da tayi wanda a ciki ta saka hijabinta da niƙab ɗin ta , ƙwaƙwalwar ta a hargitse take da sabon tsoron da yake mamayar ta ,

Ƙofar wani tafakeken gida samy baby ta tsaya tare da zaro wayar ta ta latsa lamba , bugu ɗaya ya ɗauka

Gamu mun iso tace tare da sauƙe wayar daga kunnen ta ,

ba'a yi mintuna uku ba sai maigadi ya buɗe musu ƙofar gidan , samy baby ta danna kan motar a hankali

shigar su gidan yazo dai-dai da ƙaruwar firgici a fuskar yakaka , saboda girman gidan da ya wuce hankalin ta ga fitulu da suke a watse birjik a harabar gidan haske ya wadata tamkar tsakar rana ,

Gefen wasu tsirarun motoci da basu wuce guda shida ba samy baby ta ajiye motar ta ,

Muje Yaks ,

A tsorace ta fito tana bin gidan da kallo , ba tare da samy baby ta kula ta ba tayi gaba , cikin jaan ƙafafu ta bita a baya maƙale da jakar ta , suka dumfari katafaren ginin da yake tsaye a gaban su ,

Babu yalwar mutane a babban ɗakin hutawar da suka shiga , mata da mazan da suke harkokin su a wajen babu wanda ya kula su ,

Samy baby ta jagorance su suka zauna , basu jima da zama ba aka murɗo ɗaya daga cikin ƙofofin da suke ta cikin falon aka shigo ,

Kamal ne ya shigo yana ɗan gama hanya ya ƙaraso tare da sakin jiki ya faɗa kan kujerar kusa da yakaka , rigijib !

a tsorace ta miƙe tana raba ido .

Idanun sa da suka yi nawi saboda kayan mayen da ya ɗibga ya ɗaga ya watsa mata wani kallon ƙasƙanci ,

Ke wai ji mana , ya kike wani safurewa haka kina wani ƙoƙarin waskewa , ? Kamar baki da sanin cewa na biya kuɗin ki , zo nan na fara morar kuɗi na dallah

Ya miƙa hannu ya fisgota ta koma da ƙarfi ta zauna ,

Ganin sa ya mayar kan Samy baby

Yane to yawa kike fa, Zaman me kike ? Ko kina neman me tayi ne ? Nan duk suna da chicks ɗin su dan haka ki ƙara gaba ,..

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now