BABI NA ARBA'IN

6.4K 1.1K 222
                                    

Cikin sa'a da Yakaka ta nemi izni wajen Prof kan ta bi Hajja zuwa wajen 'yar uwarta sai Prof bai hana ta ba , sanin cewa da yayi haƙiƙa akwai buƙatar su ga juna ita da 'yar uwar ta .

Sai dai yayi mata jirwaye da kamar wanka , ya yi mata nasiha tare da jaan kunnen , a ƙarshe ya gindaya sharadin kar ta wuce kwanaki goma zuwa sati biyu a Niger ɗin ta dawo gida nan wajen sa ,

Cike da ɗokin sake ɗaura idanunta akan Halittun biyu mafiya soyuwa agareta ta fara shiri, duk wasu 'yan kuɗaɗen da take da su irin wanda Prof yake ba ta da wanda Rahima ke mata kyautar su da suka tasamma dubu goma sha biyar duk ta tattara su ta ƙulle ta nufi kasuwa ,

Sayayya ta shiga yi gefe guda na zuciyar ta na cigaba da saƙe-saƙen irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Youssouf ,

Daga Jiya zuwa yau, iyakar tunanin ta kan matakin da take ji zata iya ɗauka ya ƙare ne akan kawai abu mafi sauƙi shine ,

Idan Har sun hadu zata ce da shi, ya saki ƙanwar ta ya kuma bata 'yar ta , ko kuwa ta kai lamarin gaban iyayen sa , waɗanda ta riga ta san ko su , su waye ? ta san cewa shi ɗan sarki ne tun a lokacin da Samy Baby ta goranta mata akan sa ,

Ta san wannan ce kaɗai madogarar ta , idan har ba haka ba ai ita bata isa jaa da shi ba .

Tana da tabbacin ba zai yarda asirin da yake tsakanin sa da ita ya tonu ba da ta riga ta san ya ɓoyewa mutane dayawa ciki kuwa har da Falmata ,

ita kuma ta shirya sanar da ita gaskiyar kome da ya faru tsakanin su da Youssouf ɗin, ta tabbatar daga lokacin da Falmata ta san kome baza ta sake yarda da shi a matsayin Miji ba , za kuma ta taya ta su ƙwato Mama suyi dawowar su nan.

Da tunanin hakan ta ƙaraso wajen sayar da Takalman mata da yara irin na roba masu sauƙin kuɗi ,

Tafi son ta saya musu 'yan kayan sanyawa a jiki musamman dayake bata san yaya rabuwar ta su da shi Mayaudarin zai kasance ba ,

wataƙila suyi irin rabuwar da yayi da ita a baya , watau ya yasar su akan titi babu ko suturun kirki ya kora su .

Dan haka ya zama dole ta yi musu guzurin kaya daga Falmatan Har Mama .

Daga wajen 'yan takalman inda ta ɗauka musu ƙafa bibbiyu duk da cewa kintata tayi ta auna girman ƙafafun su a tunanin ta ,

Sai ta nufi wajen 'yan kayan yara , nan ma ta auna da girman Mama da ta gani a hoto ta saya mata shiga biyu masu sauƙin kuɗi ,

Ƙaunar Falmata ga Ƙuli-ƙuli mai sugar , ta tuno dan haka ta je ta saya mata shi na ɗari uku fal cikin ƙaramar baƙar leda ta ɗaure ,

Ba zata yi wasa da kuɗin ba saboda guzuri sanin da tayi basu da inda zasu samu kuɗin mota a Niger idan suka yi rabuwar baram-baram da Youssouf .

Ko da haka ta kasance wataƙila baza su shiga matsala mai yawa ba kuɗin hannun ta zai isa dawo da su Nigeria .

*****

Kwanakin da suka biyo duk tayi su cikin ɗokin zuwan ranar tafiyar su ne , daga Rahima har Hajja sun fara gajiya da sabanbatun ɗakin da Yakaka take musu daga sun zauna .

Ta ƙira Malama Maryam ma ta sanar da ita , inda ita ma dai Nasihar ce ta ɗora mata bayan ta mata addu'o'in kariya , daga nan ta ƙira Lubna wacce ta gama fushin ta har ta huce akan rashin zuwa auren ta da tayi , murna sosai Lubna ta yi mata tare da addu'ar dawowa Lafiya .

Ta so ta je ta yiwa Amnee Sallama amma Amnee sun yi tafiya tun wajen sati uku da suka wuce ita da Ƙanwar ta Khaalty Rahima ,

Wacce aka ce ta dawo , duk da cewa bata samu damar ganin ta ba , amma tayi murna ƙwarai da dawowar ta , har ma tayi fatan ina dai su ma Allah zai dawo musu da Mamar su haka watarana ?

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now