BABI NA TALATIN DA BAKWAI

8.7K 818 399
                                    

Cike da zumuɗi Yakaka ta karɓi wani ƙaramin envelop ɗin da Rahima ta ɗauko mata daga ɗaki tana cewa

" Yakaka ga hoton Khaaltƴ Rahima duba ki gani, ita ce takwarata ai ina kama da ita ko ? .

Da murmushi bayyane kan fuskar ta , ta zaro hoton bayan ta goge hannun ta da yake da ɗan danshin ruwan ƙunshi .

Ƴar ƙaramar budurwa ce a jikin hoton na farko da baza ta wuce shekaru sha huɗu zuwa sha biyar ba , fara ƙal tamkar baturiya , ƙibabbiya 'yar dumur-mur jikinta sanye da doguwar rigar iya ƙwauri mai guntun hannu irin shigar su ta shuwa ,kanta ba ɗankwali sai manyan kitson guru da aka mata gwammon sa a ƙeya ,

" wai Masha Allah Rahima mai sunanki ta fiki kyau gaskiya ,

Ta furta tana 'yar dariya kafin ta zame hoton na bayan sa ya bayyana da bai kai wancen a tsufa ba domin a wannan ta ƙara girma ta zama budurwa da a lokacin zata iya kaiwa shekaru sha bakwai , da alama a makaranta ta ɗau hoton ganin jikinta sanye da uniform ,

Tsam , tayi tana ƙurewa cikakkiyar fuskar ta kallo da take dariya , tamkar dai tana rikiɗe mata zuwa fuskar da tayiwa sani na haƙiƙa ,

"fuskar wa ?

Ta tambayi kan ta da kan ta .

"Fuskar maman mu ," babu shakka dariyar ta da zubin haƙoranta irin na maman mu ne , sai dai maman mu bata da jiki da kyaun wannan mai kama da turawan,

Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar Amne wacce ita ma ta kafe ta da ido tana nazarin yanayin da take hangowa a tare da ita ,

" Yakaka ko kin san ƙanwata Rahima a wani waje ne ?

Kallon Amne tayi kamar zata ce wani abu sai kuma tayi ɗan yaƙe , tare da girgiza kanta lokacin da take ƙoƙarin mayar da hotunan cikin gidan su ,

" A ah Ban san ta ba Amne ,"

"Allah sarki , Rahima kenan ƙanwata da muke uwa ɗaya uba ɗaya jal a duniya , Yaa Allah ka san halin da na wanzu cikin sa tsawon shekarun nan akan rashin Rahima , Allah ka dawo min da Rahimatullah , ka sa muna da rabon sake ganawa a duniya .

"Amin Amne ,

suka amsa mata su duka fuskokin su na bayyana alhini , musamman Yakaka wacce ta shiga wani irin hali na ruɗani da ganin hoton khaalty Rahima ya jaza mata .

Ƙwarai fuskar ta tsaya mata a zuci da cikin tunaninta , Babu wadatar nutsuwa na sosai a tare da ita suka ƙarasa yinin su zuwa gefen La'asar suka kama hanyar komawa gida ,

Rahima ta dubi Yakaka bayan mai adai-daita ya sauƙe su a daf da ƙofar gida ,

"Yakaka ya naga duk kin yi wani iri , akwai damuwa ne ? Kafin mu fita a gida ba haka kike ba ,

Kafin Yakaka ta amsa Hajja tayi charaf ta amshe zance ,

"Ahaf zai wuce batun wannan ɗan banzan , ɗan hamsin yake ko ɗan daudu ? Idan har kika ce ƴar huɗubar wofin nan da ya wassafa miki zaki ɗauka ki aza a rai to kuwa kin kama kumfar teku , domin wannan da kike ganin sa rabon sa da alasambarka tun kwanansa bakwai ran suna , babu Alheri a tare da shi ko na aninin kobo atoh .

A ɗan kaikaice Yakaka ta dubi Hajja zata yi magana , aka buɗo babbar ƙofar gidan , Doctor Hamza ya turo kan motar sa , kallo guda ya yiwa gefen da Yakaka take ya ɗauke kan sa ,

Da sauri Yakaka ta wuce tana gyara zaman hijabinta , ta bar Rahima da Hajja suna gaisawa da shi , inda yake tambayar su daga ina suke ??

Suka sanar da shi daga gidan Amne suke , sosai ya ji daɗi tare da tambayar su yadda suka baro ta ? Suka amsa masa da tana lafiya ƙalau ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now