BABI NA HUDU ( MAFARI )

9.6K 532 46
                                    


Ƙanƙame da juna suke kwance a ƙarƙashin duhuwar bishiyar kukar da duhun ta ya haɗu da duhun dare tare da na damina ya bada matsanancin duhun da ba'a ko iya ganin tafin hannu .

Falmata ce a tsakiyar su yakaka da yagana suna gefe-da-gefen ta ,ko ƙokkwaran motsi basa iya yi saboda tsabar zullumi da tsoron da ya cika musu rai ! Numfashi ma a sace suke yin sa yayin da kunnuwan su suke tarwai a buɗe daga jin motsin abun da yake nesa da su da kusan rabin kilomita .

Babu motsin kome a dajin da ya wuce kukan jemagu da kuma wasu ƙananun ƙwarin da ba'a iya tantance kukan su ," haɗi da wani kuka da suke ji daga nesa ƙadan da su wanda tsananin tsoron da suke ji ya sa suka kasa tantance kukan koh na menene ,"ya dai fi musa kama da kukan bijiman sa (shanu) sai kuma jifa-jifa kukan manyan namun dawa waɗanda suke nesa sosai daga wurin da suke .

Ƙasa-ƙasa muryoyin su suka fara tashi ,"
Umm Yakaka zan yi fitsari ,"
Fitsari kuma falmata dan Allah kiyi hakuri mu jira safe.
Falmata kawai kiyi fitsarin nan anan kwance a jikin mu ," cewar yagana

Motsin da suka fara ji mai ɗan karfi yana doso inda suke ne ya sanya su sake damuƙar junan su kafin jikin su ya ɗau karkarwa kar-kar-kar .
Shikenan muryoyin su sun jawo mu su .

Wani ɗumi yakaka da yagana suka ji a jikin su wanda yake tabbatar musu yawaitar motsin da suke ji tare da ƙarin gabato su da motsin ke yi shi ya sanya falmata sakin fitsarin da tace tana ji saboda tsabar tsoro

Haske suka fara hangowa wanda basa raba ɗaya biyu hasken tocila ne ," kafin su fara jin taƙun kafafun mutum ," tare da tashin muryoyin mutanen da baza su wuce biyu ba sai dai magana suke a cikin yaren da su yakaka basa fahimtar sa ,"

Gani suka yi an ɗan kau da hasken tocilan kafin su ji an taho har kurkusa da su ," karar zubar wani abu kamar ruwa ne ya fara sauka kunnuwan su kafin su ji ruwan mai ɗumi ya fara fallatsuwa akan fiskokin su a zaɓure suka miƙe zaune wanda a tunanin su koh ruwan zafi ake watsa musu ,"

Miƙewar da suka yi shi ya mutumin da yake tsaye shima ya zabura tare da yin eho a take kuma ya buɗe murya gami da yin magana da maɗaukakiyar murya cikin yaren sa nan take sai ga hasken tocila ya dallare fuskokin su yakaka ,"

*****

A tsugunne suke bisa gwaiwowin su tamkar mai laifi a gaban hukuma ," maza ne kimanin goma a zagaye da su dukkanin su hannun su rike da makamai kama tun daga kan ,sanduna , gatari ,takobi,kwari da baka , wuƙake , da ma bindigar harbi ka buya ,

Fahimta da suka yi su yakaka basa jin yaren su na hullanci ya sanya ɗaya daga cikin su ya juya harce cikin yaren hausa
Yaro ku su waye ? Kuma daga ina kuke cikin daren nan ?

Nan take yagana wacce da alamu ta fi su yakaka fahimtar hausa ta ce mu ƴan gudun hijira ne daga garin Bama nake waɗanan kuma "tana nuna su yakaka " abokan tafiya ta ne daga nan kauyen mairambiri suke ," ƴan tawayen boko haram ne suka tarwatsa mana garuruwan mu ,"

Duk bayanin nan da suke yi yakaka da yagana basu samu damar ganin fuskokin su waye a tsaye zagaye da su ba su dai sun san mutane ne , kuma a ƙalla sun ji saukin tashin hankalin da suke ciki akan sanin da suka yi ashe akwai mutane dayawa haka kurkusa da su ,".

Juya harshe wannan mutumin da ya tambayi su yakaka yayi ,"tare da yi wa abokan tafiyar sa fassarar bayanin da yagana tayi cikin yaren su na hullanci ," nan take hayaniyar su ta ƙaure a wurin da alama Tausayawa yaran suke tare da Allah wadai da ƴan tawayen boko haram wanda sun riga sun san da zaman su ," kuma tsakanin su da su babu kare bin damo "abun nufi ko da sun haɗu cikin daji basa shiga harkar juna ," ( Makiyaya da ƴan tawayen boko haram )

Bayan doguwar muhawarar da suka yi a tsakanin su nan mutumin ya juya ga su yakaka yace ":
Yaro yanzu ku ina kuka nufa ?

Maiduguri zamu ," ance gwamnati ta tanada mana wurin zama ', za'a kula da mu cin mu da shan mu sutura da wurin kwana har ma ance za'a samu a makarantun gwamnati ," abincin cin mu ma na....

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now