BABI NA BIYAR

7.7K 515 49
                                    

Yakaka yakaka ," da sauri yakaka wacce ta maida hankalin ta gaba ɗaya ga mutanen da suke kai kawo a wurin tana nazarin su,"cikin ranta tana hango musu irin rayuwar rashin sakewar da zasu yi ita da ƙanwar ta a cikin waɗannan ɗaruruwan mutanen da basu taɓa sanin koh ɗaya daga cikin su ba ,sanin da tayi su ɗin ba mutane ne waɗan da suka saba da shiga cikin jama'a ba , hasalima su ko a garin su a ƙebe da su da mahaifiyar suke , basa shiga cikin taron jama'a saboda wasu dalilai ,"

Da sauri ta juya gami da miƙewa tsaye hankali a tashe take duban yagana wacce ta ƙaraso gaban ta yanzu tana ta haki a sakamakon ɗan gudun da tayi ," yagana lafiya ta furta hakan hannun ta ɗaya dafe da kirjin ta ?
Lafiya lau yakaka Albishirin ku , ?
Da sauri falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye ,"
Da sauri kuma cikin zumiɗi tace goro ? ta zarce da cewa...kin ga maman mu ne ?

Ɗan kallon ta da gefen ido yagana tayi cikin ran ta kuwa tausayin su ne ya kawo mata ,! ," Falmata kin manta ni ban san mama ba ?,"ta ɗora da sake faɗaɗa fara'ar ta tace ,"wai yau gwamna ne zai zo wannan sansanin , Yakaka-falmata mu yau mun shigo maiduguri a sa'a ,wallahi yau zamu ga gwamna ta ƙarasa zancen tare da yin ɗan tsallen murna,"

Ɗan guntun tsaki falmata tayi ,' kana cikin sanyi jiki ta silale tare da lalubar inda ta tashi ta sake zama tare da rafka tagumi hannu bi-biyu , sam a gareta wannan ba Albishir ba ne ," toh ita ina ruwan ta da wani ganin gwamna ? Tukun da wanne idanun zata ga gwamnan ? Sannan koh da tana gani ma a halin da take ciki a yanzu bata jin ganin gwamna zai iya ƙarar da ita wani abu da ya shafi farin ciki da har za'a yi mata albishir a kan sa ,' a halin yanzu jin ɗumin mahaifiyar ta tare da sauraron gwalatun maganar ta ,irin ta kurame shine kaɗai abun da zai sanya ta farin ciki ," hawaye ne ya silalo daga gurbin idanun ta sakamakon amsa kuwwar muryar mahaifiyar ta da taji yana shawagi da yi mata gizo a kunnuwan ta ,"

Da ɗan guntun murmushi ɗauke akan fuskar yakaka ta koma ta zauna ita ma ," kai yagana saboda haka ne kike ta ihun ƙira na har kika tsinka min zuciya ?

Ɗan yaƙe yagana tayi ganin yadda ya da ƙanwar suka gwale ta ," cikin ranta tana cewe ku ai daman alamu sun nuna ba'a yi muku gwaninta

Yakaka ni kam ki kaini banɗaki fitsari nake ji kuma fa har yanzu ba mu yi sallar azhar ba har ga shi kamar kunnuwa na suna jiyo kiran sallar la'asar ,"
Da sauri yakaka ta sake miƙewa lokaci guda tana kai duban ta ga yagana wacce tsabar murna ta gaza tsayuwa guri guda ," yagana inane banɗakin ne ?
Ɗan diri-diri yagana tayi domin ita har ga Allah ta ma manta ina aka gwada mata banɗakin yake ,"saboda tsabar ɗoki ," amma ganin wani mutum ya fito daga wani ɗan ɗaki da yake daura da ɗakin da suka fara cin karo da shi a wurin (office ɗin mutumin nan ) hannun sa riƙe da buta ga alama kama ruwa yayi , hakan yasa yagana tayi nuni da wurin ta ɗora da faɗin ,' Kamar cewa aka yi nan baya haka yake koh ,?

Bin inda ta nuna da ɗan yatsanta manuniya yakaka tayi ,"cikin shakku take kallon inda yagana ke gwada mata ," domin dai ɗakin da yake gefe da ɗakin (office) ɗin mutumin nan da yayi musu korar kare take nunawa ,"
Yagana nan baya kika ce kuma gashi kina nuna gaba ? Anya kuwa can ne banɗakin ?

Yakaka kina gani dai mutum ya fito daga banɗakin hannun sa riƙe da buta kin dai gan shi ai koh ?,"

Toh muje falmata ," yakaka ta furta hakan dai-dai lokacin da take kamo hannun falmatan suka jera har bakin barandar ," mu karasa bakin kofar sai na jira ki ,"

Ɗan turus yakaka tayi lokacin da falmata ta ce toh ina ruwan da zan yi amfani da shi yakaka ?

Bari na tambayo matan can inda ake ɗibar ruwa , ta furta hakan lokacin da take mayar da kallon ta kan wasu gungun matan da suke tsaitsaye hannuwan su riƙe da wasu manyan farantai irin na rabawa jama'ar gidan biki abinci ,

Toh ni zan shiga dan gaskiya a matse nake yakaka idan kin kawo ruwan ki ajiyemin a bakin kofar ," falmata ke furta hakan a lokacin da take laluban ƙyauren kofar ," ɗan bin ta da kallo yakaka tayi cikin ran ta fal tausayi da ƙaunar ƙanwar ta ke ƙaraƙaina ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now