BABI NA SHA UKU

5.6K 837 43
                                    

Tuki Hamza yake cikin rashin kuzari wanda ba domin kan titin shal yake babu kowa ba a sakamakon gudun da kowa yayi  , da tabbas babu abunda zai hana ya samu tukuicin zagi daga wurin sauran direbobi saboda sam ya gaza yin sauri , zuciyar sa taƙi aminta da ya tafi ya bar ta cikin halin da take ciki , wani sashi na zuciyar na son sanin me ma ya kai ta wannan unguwar wacce take cike da hatsari .?

Gangarawa yayi gefen titin ya tsaya dai-dai lokacin da tunanin abun da zai iya samun ta marar kyau idan har dare yayi mata a wannan unguwar ya gitta masa , da hakan ya sa ba shiri ya karya kan motar ya juya batare da la'akarin ba akan hannun da yakamata ya juya bane .

Wannan shine karo na biyar da take safaa-da-marwaa a bakin babban titin tana mai kwalla kiran sunan falmata , wanda zuwa yanzu da ta kawo tsakiyar hanyar ta ji juya ya fara kwasar ta a sakamakon muguwar yunwa da kishirwa gami da tsantsar sanyin da yake ratsa bargo da kasusuwan ta ta jikin jiƙaƙkun kayan ta da iska ta fara busar da su ,

Ba shiri ta dira guwowin ta duk biyu a ƙasa tare da sake fashewa da wani matsanancin kukan da baya fitowa sosai a sakamakon kwalla kiran da take ya fara dusar da karfin muryar ta .

Kuka take bilhakki tana kiran sunan falmatan a hankali cikin ƙaramar murya ,"

Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)

Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)

Allahgammama falmata are3 nyi baa maa range3 kindaa dikkin3 baa ," (Dan Allah falmata ki dawo idan babu ke bazan iya rayuwa ba )

Ƙarasa bajewa tayi daɓas a cikin guntun ruwan da yake wajen idanun ta na fara ganin bibbiyu ,

Daf da ita ta bayan ta ya zo yayi birki , kallon ta yayi ya ɗauke kai gami da matsa mata hon ,

Taji ƙarar motar sarai a daf da ita amma bata yi wani alamu na motsawa ba hasalima wani ɗan guntun tunani ne ya gifta mata na ina ma da motar nan zata take ta ta mutu ita ma kamar yadda mahaifin su ya mutu take kuma hasashen mahaifiyar su da sauran kannen ta ciki har da mafi soyuwa a gareta "falmata" duk sun riga sun mutu sun bar ta ," tunanin hakan da tayi ya sa ta sake muskuɗawa ta matsa kan titi sosai yadda zata bawa motar da ta taho damar bi ta kan ta ,"

Wani dogon tsaki ya saki ganin yadda ta rarrafo ta hau kan titi a maimakon ta taso ta zo su tafi kamar yadda yake nufi ,

Balle murfin motar yayi ya fito laɓɓan bakin sa suna furta kalmar "sokuwar banza ƴar kauye ",

Tsayuwa yayi a kan ta ya zuba mata ido yana nazarin ta cikin tantamar samuwar cikakken hankali a gareta , gefe guda na zuciyar sa na yaba kyaun dogayen fararen yatsun kafafu da na hannayen ta da suke zara-zara kuma fasalin yatsun hannayen nata kamar an feƙe fansiri haka suke da ɗan tsini ta saman su , gwanin ɗaukar hankali duk da ɗauɗa da maikon miya da suka bata su .

Tsayuwar sa akan ta bai sa ta ɗago kan ta da ta ɗora bisa hannayen ta dake kan guwaowin ta ba wanda hakan ya bata ɗamar dunkulewa guri guda tana jiran motar tayi awon gaba da ita ,"

Ganin taƙi ɗago kan nata ya sanya ransa sake ɗugunzuma ganin sa tana neman ɓata masa lokaci alhalin shi taimakon ta kawai yake son yi wanda har zuwa yanzu ya rasa dalilin da ya sa yake son taimaka mata ,"

    Ke duba bana son wawanci ki taso na mayar da ke sansanin ku tun kafin dare yayi miki anan karnuka su yagalgala ki ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now