BABI NA ASHIRIN DA TARA ( TUN RAN GINI RAN ZANE )

8.8K 661 199
                                    

Washegari da misalin tara na safe , jirgi ya ɗaga da Tafeeda zuwa birnin Lagos inda ta chan zai wuce ƙasar su ,

Dukkanin su shi da Biyamuradi babu mai isashiyar walwala suka yi sallama , alhalin basu kai ga cimma matsaya guda kan matsalar su ba ,

Duk da cewa bangaren youssouf ya ji kaso sittin cikin ɗari na damuwar sa ta tafi , saboda ya bayyana ta ga aminin nasa , ya kuma san Tafeeda zai yi duk yadda zai yi ya ga ya dai-daita kome a gida kafin komawar sa , yanzu babbar matsalar sa ita ce rayuwar ɗiyar sa ,

A daren jiya kwana yayi yana dogon nazari akan yadda zai yi ya ga ya bata ingantatciyar rayuwa ba tare da gurbatatciyar hanyar da aka samar da ita ta zama ƙalulabe a gare ta ba , da mutum yana iya sauya kaddarar sa da a daren na jiya ya juya , ya gyaro hanyar da aka yi ƴar nan ta sa ta zo duniya , amma ya riga ya san bakin Alƙalami ya bushe ,

hakan ya sa ya ɗau ƙuɗirin zai jajirce akan duk wani ƙalubale da shi zai iya cin karo da shi cikin rayuwar sa wajen ganin ya inganta tare da kyautata rayuwar ɗiyar sa ta FARKO a duniya ,"

Tafeeda kuwa ya bar ƙasar ran sa cike taf da tunanin yaya zai yi yaga ya boyewa hajiya umma musabbin shiga damuwar yarima ? Ya zai yi ya boye mata irin mummunan aikin da yarima ya aikata ? Yaya zai boye mata samuwar wata haramtatciyar ɗiya daga tsatson ta ? Kome yana neman kubce masa , shi ya kasance a tsakiya ne , ɗan aike ne shi , sai dai saƙon da zai koma da shi a yau me nawi ne wanda ya fi ƙarfin fitowa daga kan harshen sa ,

Cikin awanni (2) da tashin jirgin su daga Murtala Mohammed International Airport Lagos, Ya samu dira a Diori Hammani International Airport Niamey , duk yadda ya so ya tsaya wajen 'ubbo' su gaisa kamar yadda ya tsara , ya gagara saboda rashin nutsuwar zuci , Allah-Allah ya ke ya samu isa wajen hajiya umma ,"

Jirgin da zai sada shi da Maraɗi kai tsaye ya hau , yana isa gidan su wanka kawai yayi ya sauya kaya ,ko abinci bai duba ba ya yiwa fada tsinke , nan ya nemi iso ga hajiya umma , aka yi masa ba tare da jinkiri ba ,"

Bayan ya gaishe ta yayi shiru yana son samun ƙarfin guiwar faɗin abinda ya shirya ,"
Yayin da ita kuwa hajiya umma baki ɗaya ta tattara hankalin ta gare shi , tana nazarin sa ," ita ta katse shirun da tambayar sa ,'
Yaya kun ka ƙarƙe da yarima ? Shin ya sanar da kai damouwar sa ? Ko kouwa ?

Ƙwarai ranki ya dade yarima ya shaida min basshi da watta damouwa da ta wucce , na rashin aboukiyar zama , inda har ya nouna ra'ayi da zai yiwu ma yana buƙatar a amra masa mataye biyu a rana gouda wanna shine ɗai guda damouwar yarima , sai kouma yace ayi albishir yana nan tafe nan da ƙarshen wata me kamawa, bayan haka yarima yana nan lafiya cikin yanayi mai kyau !

Tafeda ya ƙarasa zancen sa yana sunkui da kai da jin kunyar ƙaryar da ya gilla , wacce rashin mafita ya ja sa ga aikata ta ,"

A take fuskar hajiya umma ta yalwatu da fara'a zuciyar ta ta haskaka , har haƙoran ta suka bayyana ,"

Alhamdulillah , Madallah da kai Tafeeda yaron kirki , tashi maza ka tahi ka sanya a fara shiri tare da gyara ga bangaren da anka gina na wagga ɗiya ƴar mutan agades , zan yi magana da mai martaba akan buƙatar da yarima ya tado da ita , amsa zai isar maka , Madallah da kai ,Madallah !

Godiya Tafeeda yayi tare da miƙewa yana barin shigifar , yana sake ganin dacewar shawarar da ya bayar na aurawa Yarima mataye ganin sa hakan ne mataki na farko na dakile sa daga sake faɗawa cikin wata musibar a gaba , domin ya ƙare nazari kaf rashin aure shine dalili na farko da har ya sa Yarima faɗawa ga zina ,

Yana fatan yadda ya rufa asirin mummunan labarin nan a nan gaban hajiya umma , Youssouf ma ya rufawa kan sa asiri ya bar ɗiyar chan a Nigeria kamar yadda ya faɗa masa , idan kouwa har ya ƙi jin shawarar sa babu shakka jiki magayi ,"duka da ɗanyen kara ," tsuntsun da ya jaa ruwa kuma shi ruwa kan doka , shi dai yayi iya yin sa ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now