BABI NA TALATIN DA DAYA ( ALHAKI ƘUIƘUYO NE )

7.3K 570 79
                                    

Ba ƙaramin kaɗuwa Youssouf ya yi ba lokacin da Maimartaba yake shaida masa zancen auren sa da Siyama , da har an riga an miƙa dukiyar auren ta ga mahaifin ta dake niamey , za'a yi ɗaurin auren sa da ƴan matan duk biyu a rana guda kamar yadda ya buƙata ,

Ya jima a zaune gaban Maimartaba yana jin yadda zuciyar sa take cunkushewa da tarin takaici ,

Ba tun yau ba ya gama lura da take-taken yarinyar , shi yasa sam baya sakar mata fuska ashe bai sani ba har tayi girman da zata iya yin tsaurin ido irin haka a matsayin ta na mace ta doshi iyayen sa da buƙatar son a haɗa su aure ? Babu shakka zata ɗanɗani kuɗar ta a hannun sa , sai tayi danasanin wannan mummunan shisshigi da tayi ta kutso kan ta cikin rayuwar sa da take a hargitse a halin yanzu ,

Ganin shirun sa ya tsawaita ba tare da ya amsa da amincewar auren ba , ya sa me maimartaba yin gyaran murya

  Da fatan ba zaka bijirewa oumarnin mu ba ? Bisa ga wannan haɗi da munka yi na amre tsakanin ka da ƴar ouwar ka , saboda ba muyi haka ba face sai da munka hango tarin alkhaire tare da dacewa sannan munka so ƙulla igiyar amre a tsakankanin ku , wannan ɗiya ɗiyar ƴar uwa ta ce , kai ma kuma ƴar ouwa take gare ka , ina yi maka oumarni ka karɓi amren nan da hannu biyu da ikon Allah gaba kai zaka yi farin ciki .

Kalmar 'Umarni, ta daƙile dukkanin wani yunƙuri da zai iya yi , domin shi ɗin me yawan biyayya ne ga iyayen sa , haɗi da sanin da yayi a yanzu shi me tarin laifuka ne , wanda yake neman wata kafa ko yaya ne da zai iya faranta ran iyayen sa ta dalilin ta, ko domin su iya masa uzuri a duk ranar da laifukan sa suka bayyana a gare su , su duba irin faranta mu su da yayi su sassauta masa hukunci ,

Cikin harhaɗa kalmomin da suke suɓcewa daga harshen sa saboda kaifin su da yake iya ji ya furta ,

Na Amince , Allah shi ƙara girma da ɗaukaka .

Da murmushi bisa fuskar sa yace

Madallah da kai , Allah shi maka Albarka , Ya Albarkaci zuri'ar ka , Allah shi yi katanga tsakanin ka da miƙiya , kana iya tafiya ka fara shiri doumin nan da sati biyu da ranar tayi dai-dai da gomma ga watan gobe ake ɗaurin amre .

Godiya yayi ya miƙe yana barin shigifar sarki , kai tsaye gidan da zai tarar da Tafeeda ya nufa ,

Cikin sa'a ya same shi dawowar sa kenan daga aiki da sanyin la'asar ,

Babu walwala a fuskar sa ya samu wajen zama bisa kujerun shan iska ,

  Ɗan ouwa ka kuwa san me ke shirin farouwa gare ni ?

Maida ganin sa yayi kan sa , bayan ya miƙa masa sassanyan lemun da ya tsiyayo masa a kofin gilashi ,

Sanar da ni ɗan ouwa

Wai amren mataye biyu a rana gouda , kuma amre tare da yarinyar nan siyama da ko ƙamnar duban ta bana yi , shin baka yi tounanin akwai wani dalili da ya sa maimartaba haɗa min amren mataye biyu a rana gouda ba ?

    Ɗan guntun murmushi tafeeda yayi

Banda abun ka Yarima shin amren mataye biyu a rana gouda ba gata bane ?
   Ita siyama ai duk inda ake neman macen amre ta zarta ,

  Maimartaba bashi da sani kan kome wataƙila hasashe ne yayi irin nasu na manya ya sanya shi yi maka gatan amra maka mataye biyu a rana gouda ,

Juyar da kan sa gefe yayi yana jin yadda ran sa ke sake ɓaci , kan batun auren , ga kuma ya lura Tafeeda ba shi da niyyar taya shi jimami , shi ina zai kai mata har uku a shekarun nan nasa ??
   
Kurɓar lemun sa tafeeda yake yi yana satar kallon youssouf da yayi tagumi hannu biyu ya nisa cikin tunani ,
   So yake ya masa tambaya game da al'amuran sa na ƙasar nigeria , ɗiyar sa da take can , ƙaƙa ya ƙarƙare da barin ta a chan ? Hannun wa ya baro ta ? Sai dai rashin son tuno masa da ita ya sanya shi haɗiye tambayoyin sa , ga zaton sa Biyamuradi yayi amfani da shawarwarin sa , ya baro duk wasu kuskuren da ya aikata a inda ya aikata su !

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now