BABI NA TALATIN DA UKU

9.4K 840 243
                                    

Bayan an sallami mama daga asibiti sun dawo gida , idan banda lelen ta babu abunda falmata take rabon ta da makarantar ta ma yau kusan sati guda kenan ,

Domin duk yadda hajja ta so falmata ta tafi makarantar ta bar mata kulawar mama ta ƙiya ,

gani take daga ta matsa daga kusa da ita ciwon nata zai iya tashi .

A zaune suke a falo hajja tana kishingiɗe tana hutawa bayan ta gama ƴan kananun aiyukan ta na safe ,

Mama tana kalmashe bisa cinyar falmata , wacce take bin duk gaɓoɓin maman tana tausa mata su sannu a hankali , jikin ta sanye da ruwan hodan kayan sanyi na yara mata me adon ƴan ƙula-ƙulai farare , ƙafafun ta a ƙunshe cikin fararen safar ƙafa .

Biyamuradi ya shigo falon , a shirye yake tsaf cikin kakin sa na soji , fitowar sa kenan daga sashin sa da yake sabon gidan da ya saya musu wanda ya fi wanda suka fara zaman haya a cikin sa girma da tsari , domin wannan sashi uku ne da shi ƴan madaidaita , sashin da su falmata suke da sashin baƙi wanda ba'a amfani da shi sai kuma sashin biyamuradi da idan ya zo garin yake sauƙa a cikin sa a wasu lokuta , musamman a lokacin da ya tarar da rashin lafiyar mama , wasu lokutan kuwa a hotel yake zaman sa .

Mama tana jin sallamar sa ta miƙe daga jikin falmata wacce take ƙoƙarin riƙe ta ,
Mama ki tafi a hankali kin ga ba wani ƙwarin jiki kika samu sosai ba ,

Bata kula ba
Ta taka da ɗan gudun ta , da sassarfa shima ya ƙaraso ya chafe ta sama ya cillata ,

Yana juyi da ita kafin ya sauke ta zuwa ƙirjin sa yana dariya ,

Bonjour papa , ina kwana papa .

tace daidai lokacin da take kai hannu tana ƙoƙarin cire hular kan sa ,

Taya ta cire hular yayi ya ɗora mata bisa kan ta da aka mata manyan kitson kalba suka zubo har kan kafaɗun ta ,

Bonjour mon cher ," yaya kin ka tashi ?
Lafiya papa
tace da shi daidai lokacin da take ƙoƙarin sauƙa daga ƙirjin sa ,

Ya sauƙe ta yana riƙe da hannun ta suka ƙarasa cikin falon , ya samu mazauni kan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana gaisawa da hajja wacce ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi ,

Kamar yadda ta saba , yanayin ta babu walwala idan har yana waje ta gaida shi , tana riƙo hannun mama wacce take ƙoƙarin ajiye mata hular baban ta a kai ,

Bata iya hana ta ba sai da ta ɗaura mata hular akan hular da take rufe akan ta wacce take mahaɗin doguwar rigar jikin ta ruwan madara me ɗan nawi saboda tashi da aka yi da ɗan sanyi garin sakamakon ruwan sama da aka kwana yi daren jiya .

Shafa fuskar ta mama tayi , kamar yadda yake al'adar su ita da mamar ta .

Maama kin yi chau dayawa ,
Papa ka ga maama na tayi chau , donne-nous des photos ,

ta ƙarasa zancen tana hayewa kan kujerar da falmata take ta zagaya ta bayan ta gami da sarƙafa hannuwan ta biyu ta wuyan falmatan ta cusa fuskar ta gefen wuyan ta .,

Biyamuradi wanda ya fara yiwa hajja bayani game da shirye-shiryen da yake na tafiyar su US , ya juyo da duban sa kan su idanun sa suka sauƙa kan fuskar falmata wacce haƙoranta ke buɗe tana murmushin da yake bayyana farin cikin ta da ganin walwalar mama ya assasa mata ,

Kamar maganaɗisu ya riƙe shi , ya kasa janye idanun sa daga kan ƴar fuskar ta da komen ta yake ɗan madaidaici idan aka cire manyan idanun ta ,

Ba tare da ya iya ɗauke ido daga kallon ta ba ya zaro wayar sa daga aljihu , ya juyo baki ɗayan sa ya saita cemara ya haska musu hotuna wajen kala shidda ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now