Shigowar Hajja ita ta tsagaita kukan Yakaka da Falmata,
Da girmama juna suka gaisa ita da Biyamuradi Youssouf wanda ya samu da kyar ya iya harhaɗa kalmomin amsa gaisuwar Hajja , saboda jin sa da yake gaba ɗaya a birkice a gigice, tamkar babban mai laifin da yake jiran hukunci daga Alƙali , da yana da dama da tuntuni ya ɓace ɓat .
Hajja ta mayar da ganin ta gare su sai tayi saƙare tana bin su da kallon Al'ajabin yadda suka ƙaƙwume juna suna shiƙar kuka ,
" ku kuma yaran nan lafiya kuke kuwa ? Uwarɗakina Falmata ya daga zuwa sai kuka ? Ai ke yanzu kukan ki ya ƙare , farin-ciki ya kamata ki ta tayi 'yar nan , bari kuka Falmata .
Falmata ta ɗago kan ta daga jikin Yakaka idanun ta da hawaye amma tana ɗan murmushi tace ,
" Hajja ke ce wannan ?
Bata jira ta amsa mata ba ta ɗora da cigabada cewa ,
"Dole nayi kuka Hajja , wannan da take gabana yanzu ita ce Yayata da nake baki labarin ta Yakaka Mamar Mama , ta dawo ashe bata mutu ba , kukan murna nake Hajja , duk duniya a yanzu bani da wanda ya wuce ta .
Hajja ta ɗan taɓe baki , tana satar kallon Youssouf da yake wuƙi-wuƙi da ido yana shafa kan Mama da take jikin sa tana bin Yakaka da kallo ,
" aifa na ganta , labari kuma ya iske mini tun muna can , ai tare muka zo , ina gida lokacin da ta dawo daga inda tayi mafakarta tsawon shekaru ,
" Uwarɗakina lafiya ta samu ko ? , wallahi nayi murna , nayi murna Allah dai ya sakawa Babban soja da dubun Alheri , samun mijin da ya wuce shi a wannan zamanin akwai wuya , ki kama mijin ki ki riƙe ƙam-ƙam , Allah ya barku tare ya baku zuri'a masu yawa da Albarka ,
Shiru falon ya ɗauka aka rasa mai ƙarfin guiwar Amsawa ,
Ga Yakaka mummunar addu'a ta danganta addu'ar Hajja da ita dan haka tace " ba amin ba, cikin ranta tabbas ta san da Hajja take wannan kankanbar bata san wanene Youssouf bane ,
A sanyaye Youssouf ya miƙe riƙe da hannun Mama da taƙi barin jikin sa , so yake ya kaucewa sake haɗa ido da Yakaka , yana buƙatar wani ɗan saƙo da zai shiga ya rakaɓe ya haɗa kai da bango ya yi kuka ko zai ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki , fili da baɗini bai ji daɗin dawowarta ba , bai ji daɗin bayynuwar ta ba , ya so da ta cigaba da zama a matatciyar ta tulin addu'o'in sa na riskar ta ,
Taku ɗaya yayi yana ajiye na biyu , yaji sun ƙira sunan sa a kusan tare ,
"Baban Mama ,
"Yusuf ,Hatta hantar cikin sa sai da ta kaɗa , da jin tashin muryar ta da kaushi a ƙiran sunan sa ,
A firgice ya waigo idanun sa cikin nata da yake iya hango ƙiyayya da tsana masu ɗinbin yawa , ji yayi kamar ya durƙusa guiwa biyu ya roƙeta kadda ta fasa sirrin dake tsakanin su a yanzu .
Da sauri ya mayar da ganin sa ga Falmata wacce ya ga ta sunkuyar da kan ta yana iya hango bayyanar wani irin yanayi a tare da ita ,
"Na'am Fatima yace ,
Falmata wacce ƙiran sunan sa da Yakaka tayi ya ankarar da ita tare da tuno mata da matsayin Youssouf ɗin Na asali ga Yakaka , jikin ta yayi sanyi da tasowar wani yanayi mai suffar tsoro-tsoro daga ƙasan ranta , cikin dabarbarcewa tace ,
" un daman nace ga Maman Mama fa ? Baku gaisa ba ? Zaka fita da Mama bata gaishe da Maman ta ba ,
Da sauri ya saki hannun Mama , bai yarda ya dubi fuskar Yakaka ba , yace
" sannu dai ,
Da sassarfa ya ƙarasa barin falon Mama ta ƙara da gudu ta bi bayan sa duk ita zuwan Yakaka ya takurata ,
YOU ARE READING
MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)
Non-FictionMAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baƙuwa a gareka cikin ƙanƙanin lokaci. Tafiya mabanbanciya da sauri a cikin ka...