BABI NA ASHIRIN DA UKU

6.2K 590 75
                                    

Cikin sati guda da suka yi a asibiti sun ga gata tare da kulawa daga wurin doctor hamza , har ma da ƙanwar sa rahima, domin kuwa kusan kullum sai ta zo da yamma ta taho musu da abincin da take girka musu na dare , shi kuma doctor hamza ke zowa da na safen ," da rana kuma ya yo musu take away daga sidic's ,ruwa kan sa na roba suke sha , ga lemuka da kayan shayi irin na garari , biscuits, cake , lokar gadon su cike take taf da cimaka iri-iri , tamkar dai wasu ɗiyan attajirai ,

Rahima tana da matuƙar surutu da wayon tsiya, yarinya ce da kaɗan ta girmewa yakaka , bai wuce shekaru biyu ta bata ba , ita ce ƙarama a ƙannen doctor hamza ," a halin yanzu ta gama secondry sch tana jiran sakamako , "

doctor hamza shi yace mata ta dunga zuwa ta na ɗan taya su hira ko da ta awa biyu ce , bayan ya nemi iznin mahaifin su , yayi masa bayanin su falmata da ƙudirin sa akan su na taimaka musu, sai dai ya boye masa cikin jikin yakaka na banza ne ,maimakon ya fadi gaskiya sai ya ce masa boko haram ne suka kashe mijin ta tun a garin su ,"

Maifinsa bai ƙi ya kawo su gidan su zauna ba , sai dai yayi masa gargaɗi mai karfi kamar yadda ya saba yi masa a kullum cewar ,"Ya tsoraci MATA tare da ƙaidin su yayi hankali da lamarin mata domin sau dayawa su ɗin ba'a gane gaskiyar su , wanda duk ya bada gaskiyar sa a gare su tabbas zasu takaita shi watarana ,"

Kamar koyaushe ya amsa masa yana jin yadda wani ɗaci ke yawo a zuciyar sa , sam bai so ba da mahaifiyar su ta zamto silar da ya sa mahaifin su ya samu mummunan tabo akan mace da yakasance kullum kalaman sa masu tsauri ne akan MATA ,

*********

Yau yake da niyyar kai yakaka ayi mata scan tare da gwaje-gwajen da ya kamata ayi wa mata a tun farkon samuwar cikin su , duk da cewa har kawo yau bai sake tada maganar cikin ga ita yakakar ba wacce ya lura ita bata da wata damuwa da zaman cikin a jikin ta ,

abun da bai kai ma ga gama fahimta ba kamar son cikin take sosai , saɓanin sauran matan da ya sani da suke shiga damuwa tare da ƙin abun da yake cikin nasu a duk lokacin da suka samu cikin ta haramtatciyar hanya irin nata ,

sai dai ya danganta hakan da kasancewar yakaka yarinya ce kuma akwai ƙarancin wayewa da rashin ilmi a tare da ita , ko ma menene shi daman ba shi da burin raba ta da cikin jikin ta wanda ya riga ya fahimci yayi ƙwari a mahaifar ta .

Ya zaɓi ya kaita wani asibitin daban a duba ta ne a saboda ƙoƙarin sa na kare martabar ta ko da anan gaba ya aure ta , domin a halin yanzu kowa ya san ba shi da mata , to kuma duk sauran likitocin da zai iya haɗa yakaka da su , abokanen aikin sa ne da suka riga suka san juna sosai ,ya kai ta wurin su a zuwan matsayin me take a gare shi ?

Bai son a kodayaushe ya dunga yin ƙarya dan haka ya fi son ya kaucewa duk wani abun da zai sa shi yayi ƙaryar ,"

Sai da ya bari rahima ta zo misalin karfe huɗu da rabi , ta hau sama ofishin sa tare da ajiye masa na shi abincin , nan yake sanar da ita zata Zauna tare da falmata , shi da yakaka zasu je wani waje su dawo ,"

Tare suka shiga ward ɗin inda suka tarar da su suna ƴar hirar su , babu laifi cikin sati guda falmata ta ji sauki sosai saboda kulawar magunguna masu kyau da take samu zuwa abinci mai inganci , uwa uba kwanciyar hankalin da ta samu , yini take a kan gado iskar fanka tana kaɗa ta , ga ta ga yakakar ta a gefen ta , wanda hakan shi yafi kome sanya ta farin ciki ,

Cikin fara'ar da jin muryar su ya sanya ta take gaishe da doctor hamza da zuwa yanzu take matuƙar girmama shi tare da ganin ƙimar sa har ma take jin sa a matsayin wani jigo cikin rayuwar su ita da yakaka ,

Shima faram-faram ya amsa mata yana mai sake tambayar ta yanayin jikin nata , kafin ya maida duban sa ga yakaka wacce take zaune bisa kujerar gaban gadon , "suna gaisawa ita da rahima wacce suka yi sabo da juna cikin ƴan kwanakin ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now